Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya?

A kwanakin baya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ’yan siyasar wannan zamanin suna shiga harkar siyasa ne saboda rashin abin yi. Abin tambaya a nan shi ne, shin gaskiya ya fada ko kuwa akwai gyara cikin batun nasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Ra’ayinsa ya fada […]

Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya?
Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya?

A kwanakin baya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ’yan siyasar wannan zamanin suna shiga harkar siyasa ne saboda rashin abin yi. Abin tambaya a nan shi ne, shin gaskiya ya fada ko kuwa akwai gyara cikin batun nasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Ra’ayinsa ya fada – Sanusi Argungu

Sanusi Argungu: “Ra’ayinsa ne kawai ya fada amma bai yi gaskiya ba. Siyasa abu ce mai kyau idan ka yi la’akari da ba wani addini da ya haramta yenta. Hasali ma hanya ce ta jagorancin al’umma. Ga adinin Musulunci, ta bangarena, duk wanda bai karfafa siyasa da inganta ta ba to shirme ya yi in har ban ce ya bi daji ba ko dimuwa ta kama shi. Ya kamata Shugaban kasa ya san irin zancen da yake yi, ba wai duk abin da ya ga dama shi zai fada ba. Ka ce ’yin siyasa rashin aikin yi ne, to yana son ya fada mana shi ba shi da aikin yi ne? Kuma yake son sake zarcewa ko a mutu ko a yi rai? In dai har yana son mu yarda da kalamansa to ya ajiye mulki ya nemo sana’a; daga nan sai mu yarda da maganarsa. Samun dama ne yake sanya mutum babatu. Shi ai karantarwa ya ajiye ya koma siyasa, ke nan daga aikin yi ya koma rashin aikin yi ke nan? Kai wannan maganar abar dariya ce fa, kai akwai Shugaban kasa a Najeriya?”