Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya? 1

A kwanakin baya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ’yan siyasar wannan zamanin suna shiga harkar siyasa ne saboda rashin abin yi. Abin tambaya a nan shi ne, shin gaskiya ya fada ko kuwa akwai gyara cikin batun nasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Akwai siyaya a […]

Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya? 1
Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya? 1

A kwanakin baya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ’yan siyasar wannan zamanin suna shiga harkar siyasa ne saboda rashin abin yi. Abin tambaya a nan shi ne, shin gaskiya ya fada ko kuwa akwai gyara cikin batun nasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Akwai siyaya a tsarin kasa – Sani Bello

Sani Bello: “Akwai siyasa cikin tsarin kasa a matsayin harkar yi da jagoranci, to ya za a ce kuma shugaban da siyasa ta dora shi kan al’umma ya dubi ’yan uwansa da shi kansa ya furta kalma irin wannan? Haba, bai yi daidai ba. Na san a yau da siyasa ne ake kawo kowane irin ci gaba kuma ’yan siyasar ne ke samar da ci gaban kuma duk a ce a rashin aikin yi ne suke wannan? A tsarin Musulunci akwai karatun sana’a, siyasa ko sana’a ce don haka duk mai yin ta a addinance yana da aikin yi; ya rage nasa gyarawa ko bbatawa. A tunanina, Shugaban kasa na nufin ’yan siyasa da suna da aikin yi kafin su shiga siyasa da ba su sace kudin al’umma ba amma rashin aikin yi ne ya sa ba su da tausayi da sanin ya kamata, kowa bukatarsa ya cika aljihunsa; wato sama da fadi da dukiyar jama’a, wanda hakan abin takaici ne ga siyasar duniya.”