Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya? 2

 A kwanakin baya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ’yan siyasar wannan zamanin suna shiga harkar siyasa ne saboda rashin abin yi. Abin tambaya a nan shi ne, shin gaskiya ya fada ko kuwa akwai gyara cikin batun nasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Akwai gaskiya a […]

Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya? 2
Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya? 2

 A kwanakin baya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ’yan siyasar wannan zamanin suna shiga harkar siyasa ne saboda rashin abin yi. Abin tambaya a nan shi ne, shin gaskiya ya fada ko kuwa akwai gyara cikin batun nasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Akwai gaskiya a batunsa – Halima Sabo

Hajiya Halima Sabo Azare: “Wasu rashin aikin yi na shigar da su siyasa saboda sun san sai sun shiga kafin su samu taimako da uban daki. Saboda mutumin da ba zai iya ba ka dubu dari kyauta ba sai ya kashe maka milyan don ka kai labari. Idan ka samu ka ba shi kwangila ya mai da jarinsa idan har ya san za ka samu tagomashi. A wurin talaka sana’ar marar sana’a ce, ta yadda zai fita laluben abin da zai ci har zuciyarsa ta mutu bai tara abin da zai rufa masa asiri ba, sai ko na cin lokacin ya dore da yunwa idan kasuwa ta ci ta watse sai a shiga mummunar hanya kamar yadda ke faruwa tsakanin matasa ’yan siyasa.  Masu sana’a sun dauke ta sai ta taso, wanda ya shigo da kudinsa ke takara wanda ba shi da sisi kuma sai ya zama dan kwaram, mai jiran zama a gindin ofis yana neman uban daki ana wulakanta shi.”