Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya? 3
A kwanakin baya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ’yan siyasar wannan zamanin suna shiga harkar siyasa ne saboda rashin abin yi. Abin tambaya a nan shi ne, shin gaskiya ya fada ko kuwa akwai gyara cikin batun nasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Akwai gyara ga […]
A kwanakin baya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ’yan siyasar wannan zamanin suna shiga harkar siyasa ne saboda rashin abin yi. Abin tambaya a nan shi ne, shin gaskiya ya fada ko kuwa akwai gyara cikin batun nasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Akwai gyara ga batunsa – Jarman Ibadan
Jarman Ibadan Alhaji danjuma Yakubu: “Idan shi Shugaba Jonathan yana tunanin ya shiga siyasa a lokacin da yake ragaita babu abun yi ne, to ya kamata ya sani cewa ya tarar da wasu fitattun ’yan kasuwa masu arziki a hannunsu, wadanda duniya ta san da su kuma akwai ’yan boko da makamantansu masu abun yi kafin su shiga siyasa. Haka kuma akwai irin wadanda suka jefa kawunansu cikin siyasa kamar shi Shugaba Jonathan domin neman biyan buwatun kansu. Abun da muke so shi ne, dukansu su hadu su sama wa Najeriya mafita ta hanyar yin adalci ga jagorancin jama’a, ba kamar yadda aka kyale talakan Najeriya cikin halin ni ’yasu ba.”