Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya? 4
A kwanakin baya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ’yan siyasar wannan zamanin suna shiga harkar siyasa ne saboda rashin abin yi. Abin tambaya a nan shi ne, shin gaskiya ya fada ko kuwa akwai gyara cikin batun nasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Siyasa ibada ce […]
A kwanakin baya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ’yan siyasar wannan zamanin suna shiga harkar siyasa ne saboda rashin abin yi. Abin tambaya a nan shi ne, shin gaskiya ya fada ko kuwa akwai gyara cikin batun nasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Siyasa ibada ce – Alaramma Abdullahi
Alaramma Abdullahi kofar Nasarawa: “Bayaninsa akwai gyara. Siyasa ibada ce ba aikin banza ba ce. Tun kafin Jonathan ya san zai zo duniya ake yin siyasa kuma tun zamanin annabawa ake yin siyasa. Da ita ake ciyar da kasa gaba ake gina jama’a, don haka shugabanci ba ya yiwuwa sai da siyasa. Idan da ya san marasa aikin yi ke siyasa lokacin da ya fito ya nemi marasa aiki na zahiri ya zuba a gaba ya ce da su zai nemi matsayin da yake kai ya gani idan zai kai labari. Don haka maganganun Goodluck magana ce irin ta mai mulkin da bai wahala ba ya tsinci dami a kala daga hannun marasa kishi, yanzu kuma yake nuna musu ba yadda za su yi da shi. Don haka ya rage wa ’yan Arewa su yi wa kansu fada su san Annabi ya faku, su koma ga Allah.”