Ina goyon bayan a bai wa kananan hukumomi ’yanci amma… – Gwamnan Jihar Neja
Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Bello ya ce ba ya da matsala da batun ba kananan hukumomi ’yancin gashin kansu, matukar za su aiwatar da ayyukan da aka dora musu, kuma ya bayana kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen samar da ababen more rayuwa ga jama’ar jihar. Gwamnan ya fadi haka ne lokacin da yake […]

Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Bello ya ce ba ya da matsala da batun ba kananan hukumomi ’yancin gashin kansu, matukar za su aiwatar da ayyukan da aka dora musu, kuma ya bayana kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen samar da ababen more rayuwa ga jama’ar jihar. Gwamnan ya fadi haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilin Aminiya Abubakar Ibrahim da ke Washington na Amurka lokacin da ya zo hutu a Najeriya:
Ranka ya dade wani lokaci can baya da ka zo Amurka ka ce daya daga cikin ayyukan da kake bai wa muhimmaci shi ne ilimi, ina aka kwana kan wannan batu?
Ba shakka muna nan a kai yanzun nan Kwamishinar Ilimi ta fita daga ofishina kuma ta ba ni rahoto ne a kan wasu makarantu da muke gyarawa. Ta ce an kammala gyaran 6 daga cikinsu an yi musu komai tamkar an sake gina su, kama daga ajujuwa zuwa wurin kwana da na bukatun dalibai, kai kusan komai an kammala. Sai kuma wasu uku, wato Commercial Kontagora da ta Tegina da Baro ayyukansu an yi kusan sama da kashi 70 ko fiye da haka, muna sa ran za a gama su nan ba da jimawa ba. A zantawarmu da Kwamishinar yanzu mun kara sake zabar wasu makarantu 6 muna fata mu fara su da zarar mun samu karin kudi a shekara mai zuwa. Muna da makarantun kwana kusan 40 a Jihar Neja, a lissafin da muka yi muna fata a kowace shekara mu gyara 10, kafin karshen wa’adin aikinmu mu kammala su idan kuma ba mu kare su ba abin da zai rage kadan ne.
Gaskiya mun samu makarantun da daliban a cikin wani mummunan hali domin suna zama kamar dabbobi, suna kwana a kasa dakunan kwanansu ba kyau suna yoyo, ajujuwa kuma ba kujeru kuma malaman ba su kulawa, abin dai ga shi nan ba dadi. Yanzu Allah da ikonSa mun kusa kammala 9, za mu ci gaba da kokari domin ilimi yana da muhimmaci. Wannan ina batun makarantun sakandare ne, sannan cikin takardar da Kwamishina ta kawo min yanzu, muna son mu waiwayi makarantun gaba da sakandare, wadancan makarantu abin da ya fi damun yawancinsu shi ne wurin kwana, kuma iyaye da dama ba su da kudin da za su daukar wa ’ya’yansu haya a gari. A cikin takardar da Kwamishina ta kawo kamar Jami’ar Ibarahim Badamasi Babangida da Polytechnic ta Zungeru, da School of Agric ta Mokwa muna son mu fara gina dakunan kwanan dalibai na maza da na mata. Muna son kowace makaranta mu gina mata jerin dakuna biyu, wannan na cikin wadanda Kwamishinar ta kawo da kudin da muke bukata Naira biliyan daya da miliyan 400, sai dai gaskiya ba mu da kudin amma za mu yi kokari mu fara mu gani, domin hakan zai sa mu toshe wata kafa, wannan aiki ne da ke da muhimmaci.
Ka yi bayani a kan abubuwan da gwamnatinka ke fatan ta samar amma ba ka ambato malamai ba?
Su ma ba mu manta da su ba, domin sun tafi yajin aiki saboda karin albashi mun yi kokari mun dan kara kuma ina fatan cewa za a samu fahimta. Ba muna kin kari ba ne, amma muna kula wajen karin kada mu daukar wa kanmu nauyin da gwamnati ba za ta iya dauka ba. Kwanakin baya mun kara na likitoci sun ji dadi, da ba mu da wadatattun likitoci domin albashin da ake biyansu ba yawa, ko sun zo bayan ’yan watanni ko shekara daya sai wuce, su koma jihohi makwabtanmu, amma yanzu yadda muke biyan likitocinmu ya zo daidai da na ko’ina a Najeriya, koda an fi mu ba yawa, don haka yanzu likita bai da hujja na kin yin aiki. Kuma na fada musu tunda muna biyan su abin da ya dace, su ma ya kamata su yi wa jama’a abin da ya dace, su yi aikinsu bakin gwargwado kuma ina fata suna yi domin kawo yanzu ban samu wani rahoto cewa akwai rashin kula daga wurin kowane likita ba, kuma muna sa ido.
Maganar hanyoyi, daga kowane bangare za ka shigo Jihar Neja sai ka yi kamar ka ce wayyo Allah saboda rashin kyawunsu, me gwamnatinka ke yi game da wannan matsala?
Wallahi gaskiyarka, batun hanyoyin ya dame ni, yawancin hanyoyin da kake magana hanyoyi ne na Gwamnatin Tarayya ka ga daga Minna zuwa Suleja muna kashe makudan kudi wajen gyara su, idan ka duba daga Minna zuwa Kwakuti mun gama gyara ta, daga Kwakuti zuwa Lambata akwai matsala daga Lambata zuwa Maje ma ana nan ana aikinta, duk mu muke biya ba Gwamnatin Tarayya ba, kuma hanyoyinta ne. Na yi kuka, na yi kuka, babu wani mataki da aka dauka, a bisa tsari ya kamata ne in mun yi wannan aiki Gwamnatin Tarayya ta biya mu, amma tunda mu mutane Jihar Neja ne ke wahala shi ya sa muke gyarawa. Da yawa mutane ba su gane wace hanya ce ta Gwamnatin Tarayya wacce ce ta Jihar Neja. Kuma Gaskiya ban da hadari da wahalar jiki ga motocin mutane na lalacewa an zo kuma an wayi gari muna gyara, manyan motoci sun karu a wannan hanya saboda karyewar gadar Bokane da Jebba, sun dawo suna biyowa ta Bida da Minna. Mun yi kuka a kan nauyin motocin ya yi yawa, a tsarin da muka sani a doka, tirela kada ta wuce kayan tan 30, idan ta mai ce kada ta wuce lita dubu 33, amma yau an wayi gari sai ka ga tirela tana daukar lita dubu 40 zuwa 50, kai akwai mai daukar lita dubu 67, kuma hanyoyinmu ba a tsara su dauki wannan nauyin ba. Ko Saudiyya da ke da hanyoyi masu kyau tirelolin ba su daukar wannan nauyi, ba su wuce nauyin tan 33 ko kwanan nan da na je Makka na duba na gani, wallahi duk kudin da gwamnatin jiha da na tarayya za su kashe kan hanyoyi mutuwa za su yi, saboda hanyoyin nan ba su daukar wannan nauyi.
To me gwamnati za ta yi domin magance matsalar?
To a tsarin Najeriya akwai hanyoyin gwamnatin jiha da na tarayya. A tsari ba ni da abin da zan ce kan wata hanya mallakar tarayya, ba abin da zan iya yi duk da cewa a jihata hanyar take. Gwamnatin Tarayya ce za ta ba da doka ta ce kada wata mota ta wuce nauyin tan 30 ta hau titi. Na yi magana da Minista na yi magana da Mataimakin Shugaban kasa duk sun amince cewa haka abin yake, domin za mu jima muna kashe biliyoyin Naira muna gyara hanyoyi amma ba za su dade ba. Kana tsaye ana gyara hanya da babbar mota ta bi sai ka ga ta fashe, in da manyan motocin nan suna daukar tan 30 ko tankokin mai na daukar lita dubu 33 ba abin da zai samu hanyoyinmu, gadojin da suke karyewa ba a banza ba ne yanzu a Neja gadojojin da suka karye sun kai 4 zuwa 5, ko makon da ya gabata sai da wata gada ta karye a hanyar Lapai, gadojin nan sun tsufa kuma ba a tsara su yadda za su dauki wannan nauyin na tsawon wannan lokaci ba, a ce motoci akalla 200 suna gittawa kullum dole ne su yi wa gada illa.
Na tabbata ba jihar ce kadai ke fuskantar irin wannan matsala ba, a taronku na gwamnoni ba ku tattauna batun ne don daukar mataki na bai-daya?
A daya daga cikin tarurrukanmu na taba tado wannan magana, amma ba ta yi kwari ba, amma kamar yadda na fada maka na yi magana da Minista, kuma zan ci gaba da magana da shi, dole sai mun koma a tsarinmu yadda muke a da, akwai nauyin gada (weigh bridge) wannan ba sabuwar doka ba ce, amma kowa yana so ya samu riba mai yawa aka bari motoci masu nauyi suna wucewa suna lalata hanyoyin, muna wahala, motocinmu na wahala, su kansu masu wuce ka’idar suna wahala. Babu abu mai kyau kamar hanya mai kyau, ka je inda za ka cikin kwanciyar hankali kuma tana rage hadari. Misali daga nan zuwa Abuja tafiyar awa daya da rabi amma sai ka yi sama da awa 3 ba don gyaran da muka yi ba. Daga yanzu duk lokacin da na ga Minista sai na tado masa da wannan batu har sai sun mayar da dokar kayyade kayan da tirela za ta dauka, ai ni ma ina da tankuna.
Akwai labarin cewa ruwa ya kwashe gonakin mutanen yankin Agwara, me gwamnatinka ta yi domin agaza musu?
Kowace shekara muna samun wannan matsala, ko bara mun samu hasarar gonakin shinkafa da yawa, saboda idan an bude dam din Kainji yana shafar mutanenmu, wajen Agwara ba zan yi mamaki ba saboda kogin Kainji yana ta gefen garin ne. Kawo yanzu ban samu wannan rahoto ba, amma da zarar na samu mukan tura Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha ta tattaro sunayen wadanda abin ya rutsa da su akwai dan abin ihsani da gwamnati ke ba su, Idan da a ce ka zo da wuri da ka tarar da ’yan kasuwar Minna da suka yi gobara, mun ba su dan abin da zai rage musu radadin wannan hasarar. Mu san wannan ba zai dawo musu da hasarar ba amma zai dan toshe wata kafa, wannan ke nan. Game da maganar noma muna mayar da hankali a kan aikin gona kwarai da gaske, domin kwanaki mun je Jihar Pennysylabania ta Amurka kan maganar noma ta yadda za mu yi aiki tare. Ba shakka mun fara samun fahimta iyaka za mu ci gaba da magana kan me za su iya saye daga hannunmu kuma me za mu iya saye daga hannunsu. Duk da ba mu riga mun yi yarjejeniya ba, ina ganin abin da muke bukata daga wurinsu shi ne kayan noma su injuna. Saboda bashin nomansu a can kashi biyu ne cikin 100, na fara magana da su idan za su yarda su ba mu bashin kayan noma, mu kuma idan muka yi noma su sayi kayan gonarmu. Saboda haka mun yi musu wannan talla za su yi nazari muna fata su yarda. Wannan karon gwamnati za ta shiga harkar noma gadan-gadan kai-tsaye.
Kamar me kuke fatan nomawa domin ku sayar musu?
Su suna son waken soya da citta, ana bukatarsu a duniya sosai, akwai ridi, akwai yazawa, idan muka samu takarda ko yarjejeniya a duk duniya za mu iya samar musu, sai kuma kwara (Shea butter), maganar kwara ta yi karfi kuma har mun dauki wani kamfani da zai fito da yadda za mu samu riba mai yawa a kwara domin muna da itatuwa amma ba mu tsar yadda za mu amfana da shi ba sosai. Yanzu ana duba yadda za mu ci amfaninsa sosai. Wadannan hudu da na lissafa maka a koyaushe a shirye muke mu samar da su ga duk wata kasa ko kamfani. Sai dai mun samu wasu shaidanu suna sare mana itacen kwaran don haka mun kafa rundunar sha-yanzu- magani-yanzu, duk wanda muka kama yana sare mana itacen kade da ke samar da kwara, sai doka ta yi aiki a kansa. Ina ganin ’yan majalisa sun yi dokar dauri ne ko tarar kudi mai yawa. Kuma mun fara shuka itatuwan kwara, baya ga wadanda Allah Ya ba mu, na fada wa ma’aikatar gona ta fara shuka wannan itace kuma ta fara, ina jin ta shuka hekta biyar-biyar yanzu.
Wani lokaci da ka ziyarci sashen Hausa na Muryar Amurka na tambaye ka batun cin gashin kan kananan hukumomi, ina wannan batu ya kwana?
A tsarina ba ni da matsala da cin gashin kan kananan hukumomi, sai dai akwai kananan hukumomi 12 a nan jihar da ba za su iya tsayawa da kafafunsu ba. Dalili shi ne sun dauki ma’aikata sun yi yawa, sun dauki ma’aikatan da ba su da bukatarsu, don haka ko mun bar su ba su iya biyan albashi, saboda haka muke taimaka musu domin su iya biyan albashin. Amma wadanda suke iya biyan albashi idan ka je cikinsu za ka tarar an yi ayyuka da yawa, su kuma wadanda ba su iya biyan albashi sai ka tarar ba abin da suka yi wa mutanensu. Ba ni da matsala ko kadan wajen bai wa kananan hukumomi cin gashin kansu, dama can ban sa ido a kan kudinsu, idan za su ci gashin kansu kuma su yi wa mutane aiki wannan ya yi daidai, haka ake so, domin su ke tare da jama’a a can kasa. Su suka san bukatun jam’arsu, ni ina Minna, shuhgaban karamar hukuma idan ya san abin da yake yi ya kamata ya yi ayyuka a karamar hukumarsa kamar makarantun firamare ba sai gwamnatin jiha ta sa hannu a ciki ba, ko ’yan gyare-gyaren hanyoyi, amma mafi yawansu ba sa yi. Kwanakin baya kungiyar Malamai (NUT), sun zo nan suka ce ba su son a mayar da su karkashin kananan hukumomi, suka ce ba za su iya daukar dawainiyarsu ba. Kuma ta wani gefen na yarda da su, domin wadansu sun nace sai a ba su gashin kansu, to idan za a ba su sai a hada musu da ayyukan da ya kamata a ce yana kasrkashin kananan hukumomi ba wai a ba su kudi ba, amma kuma wasu ayyukan a ce gwamnatin jiha ce za ta yi.
Wasu jam’iyyu sun ce lokacin da kake takara sun janye maka amma da ka samu nasara sai ka share su, ina gaskiyar wannan batu?
Gaskiya ban ji wannan korafi ba, amma akwai wata kungiya da ake kira IPAC, wadda ita ce na wadannan jam’iyyun siyasa ko mutanen da kake magana, na san su kuma muna da kyakkyawar fahimta da su kuma sun zo ofishina ban san iyaka ba. Su na sani idan sun ce ba su zo ba, to shi ke nan, domin na san su na san sakatarensu muna abubuwa da dama, amma idan akwai wata kungiya daban ban san ta ba, wannan kwanakin baya na bukaci su kawo sakataren wata hukuma da za a nada. Kuma kungiyar ta IPAC duk lokacin da suka zo nemana idan ba su gan ni ba, sukan gana da Mataimakin Gwamna ko shugaban jam’iyyarmu ta APC.