Ina goyon bayan hana bara da gwamnoni suka yi – Sani BK
Matakin da gwamnatoci suka dauka na hana bara abu ne da ya dace matukar sun hana yin almajirancin ne da nufin hana almajirai bara. Jawabin hakan ya fito ne daga babban limanin Masallacin Juma’a na Dutse Malam Mahammadu Sani Birnin Kudu a wata zantawa da ya yi da manema labarai a ofishinsa. Sai dai ya […]
Matakin da gwamnatoci suka dauka na hana bara abu ne da ya dace matukar sun hana yin almajirancin ne da nufin hana almajirai bara.
Jawabin hakan ya fito ne daga babban limanin Masallacin Juma’a na Dutse Malam Mahammadu Sani Birnin Kudu a wata zantawa da ya yi da manema labarai a ofishinsa.
Sai dai ya ce yadda gwamnoni ke korar almajirai daga jihohinsu a wannan yanayin suna mayar da su jihohinsu na asali ya saba wa kaidar da Kungiyar Gwamnonin ta shinfida.
A cewarsa hakan ya saba wa kaida da tsarin lafiya kasancewar ana fama da cutar coronavirus a fadin duniya.
- Karatun almajiranci ya haramta a Kano – Ganduje
- An bude kasuwanni, za a koma aikin gwamnati a Katsina
- Ba yanzu za mu janye dokar hana fita ba – Badaru
Don haka ne ma Malam Muhammad Sani ya shawarci gwamnonin su yi koyi da yadda jihar Jigawa take ba wa almajiran kulawa kuma ba ta koransu daga jihar saboda tsoron karya kai’dojin da aka shinfida na cewar duk mai cutar a killace shi a inda yake har sai ya samu sauki.
Ya kuma bukaci gwamnoni su yi wa almajiran tanadi na cin moriyar harkokin ilimi na addinin da na zamani a matsayinsu na ‘yan kasa kamar kowa.