Ina hakkin Hanifa?
‘Mutane ba su san azabar da wanda aka kashe da guba ke sha ba’
A wannan makon, hukumomin makarnatar da ’ya’yana suke zuwa suka sanar da mu aniyarsu ta kai yaran ziyara daya daga cikin makarantun gwamnati da ke Kano.
An karfafa wa yaran gwiwa su tafi da tsofaffin takalmansu na makaranta, da tufafi, da kuma jakunkuna domin bai wa takwarorinsu masu rangwamen gata.
- Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Hanifa
- Za Mu Sa Kafar Wando Daya Da Gwamnati In Aka Janye Tallafin Mai – NLC
Wasu daga cikin iyayen yaran ma takalma da jakunkuna sababbi dal suka sayo suka raba wa daliban.
A ganina, duk da cewa wasu za su iya daukar wannan lamari a matsayin nuna isa, an yi nasara matuka kasancewar da dama daga cikin abokan ’ya’yana ba su taba yin arba da talauci ba kafin lokacin.
Wasu daga cikin yaran, wadanda suka fara girma, har hawaye suka zubar lokacin da suka ga yadda wadancan ke rayuwa – wasu daga cikin ajujuwan babu kujera ko benci sai dai a zauna a kan dabe babu ko tabarma, ga shi ana tsaka da tsananin sanyin hunturu.
Wasu daga cikin daliban makarantar gwamnatin ma ko takalmi babu a kafafunsu balle safa; don haka kowa na ganin yadda kafafun suka yi kaushi ko ma faso.
Rangwamen gata
Rigunansu na makaranta sun yayyage, kuma sun yi musu kadan, sannan galibinsu ba su da rigar sanyi ko suwaita.
Dana ya tasirantu sosai da abin da ya gani yayin ziyarar, har ta kai tun lokacin ba shi da wata hira sai ta daliban.
A yanzu haka ya kuduri aniyar tara kudi don saya wa makarantar da suka je takalman silifas, da tabarmi, da suwaitu. Jinjina a gare shi!
Ranar Alhamis, 20 ga watan Janairun 2022 aka kai ziyarar. Ina cikin tunanin aika wa hukumar makarnatar sakon yabo sai labarin Hanifa ya riske ni.
Hanifa yarinya ce ’yar shekara biyar wacce daliba ce a makarantar Noble Kids dake Dakata a Kano. Ranar 4 ga watan Disamban 2021 ta bata.
Ina iya tunawa na dan ga labarin a shafina na sada zumunta har na ce a zuciyata ‘Allah Ya sa kada a kuma!’
Yawan sace-sacen mutane da ake yi ya sa mun daina jin komai – idan muka ji ko muka karanta faruwar irin haka sai mu yi addu’ar neman tsari a zuciya mu ci gaba da harkokinmu na yau da kullum. To babu wani abin a zo a gani da za mu iya yi.
Mutane sun yi ta tururuwa suna zuwa gidan iyayen Hanifa don su yi musu jaje su da ’yan uwansu da abokan arziki.
Har da kaza a cin danko?
Daga ciki wadanda suka je din har da Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar da Hanifa take.
An bayar da rahoton cewa ya nuna matukar alhini da sace ta, har ma ya bi sahun sauran ’yan uwa wajen yin addu’ar Allah Ya dawo da ita lafiya.
Da aka sanar da ’yan sanda sai Kwamishinan ’Yan Sanda ya umarci rundunar Operation Puff Adder (ina kaunar irin wadannan sunayen) ta gudanar da bincike a kan sace yarinyar.
A daidai wannan lokacin, shi kuwa wanda ya sace ta ya fuskanci wani kalubale – yarinyar ta shaida shi don haka idan ya sake ta za ta fasa kwai.
Ranar 18 ga watan Janairu, wanda ya sace ta ya ba ta shayin da ya yiwa sirki da maganin bera sannan ya koma gefe yana kallo har ta mutu.
Daga nan ne ya binne ta da taimakon wani mai suna Hashimu Isyaku a harabar makarantar wadda take Unguwar Tudun Murtala.
Cewa ‘an bai wa mutum guba ya sha ya mutu’ – sam wadannan kalmomi ba sa bayyana irin ukubar da mutumin ya fuskanta.
Kalmomin na nuna mutuwar ta dauke mamacin nan take, ko kuwa? Kamar kawai da mutum ya sha guba sai ya bingire ya mutu.
To alal hakika abin da yake faruwa ba dadin ji sam.
Wanda ya sha gubar ihu zai yi ta yi yana murkususu saboda azabar ciwo – wannan ya danganta da irin gubar – har sai jijiyoyn da suke sarrafa numfashinsa sun daina aiki ta yadda ba zai iya numfashi ba.
Wannan shi ne abin da galibin magungunan bera suke haddasawa. Ku yafe ni, ba manufata ba ce na tsorata ku.
Kama Abdulmalik Tanko
Binciken ’yan sanda ya kai ga kama Abdulmalik Tanko, shugaban makarnatar nan da ya je yi wa iyayen Hanifa ‘jaje’.
Da bakinsa ya shaida wa ’yan sanda cewa bayan ya yi yunkuri har sau biyu don gamsar da wasu su taimaka, daga bisani ya yi nasarar jan hankalin Hanifa (dalibarsa) ya kai ta gidansa.
Bayan nan ne ya tuntubi iyayenta ya nemi a ba shi Naira miliyan shida kudin fansa.
Duk da ya kashe Hanifa, Abdulmalik bai fasa karbar kudin ba.
Dubu ta cika
’Yan sanda sun tabbatar da cewa an kama shi ne a wurin da zai karbi kudin fansar. An gai da Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya!
Ranar Alhamis labari ya fito da dumi-dumi cewa an ga Hanifa – sai dai ba yadda aka so ba.
Tono gawarta aka yi aka garzaya da ita asibiti don yin gwaji da tabbatar da cewa ta mutu.
A karo na biyu danginta da sauran kafatanin al’ummar Kano suka shiga jimami.
Bayan na saurari ’ya’yana suna bayar da labarin ziyararsu sannan na karanta labarin Hanifa, zuciyata ta dugunzuma.
Yaya za mu yi?
Me ake so mu yi ne a matsayinmu na iyaye? Me Najeriya take so mu yi?
Shin so ake yi mu rika rufe yara a gida muna karantar da su? Ina batun alfanun zaman aji wanda ba zai kidayu ba?
Yanzu ke nan ba zato, ba tsammani, kai yara makaranta ya zama babban laifi?
Idan ka kai su makarantar kwana ta gwamnati, wata kungiyar ’yan ta’adda ta yi awon gaba da su; idan kuma ka kai su makarantar kudi, wani malami – wani dan iskan mai makarantar – ya sace su ya kashe.
Wai don Allah yaya za mu yi ne?
A daren Alhamis din ban yi wani barcın kirki ba, ina ta tunanin anya zan tura yarana makaranta kashegari kuwa? To ina dalili?
Na ji cewa Gwamnatin Jihar Kano ta rufe makarantar da abin ya faru.
Na tausaya wa asalin mai makarantar domin a sanadin gurbataccen malami daya zai rasa hanyar samun abinci.
Ranar Juma’a yaran suka tsaya kai da fata a kan cewa sai sun je makaranta.
Amma ban amince ba sai da na zaunar da su na ja musu kunne a kan kada su kuskura su bi kowa zuwa ko’ina a wajen makaranta bayan ni.
Taraddadin da nake yi ya sa na fara binciko yadda za a sakala na’urar GPS mai bibiyar inda mutum yake a agogunansu na hannu.
Yadda tarbiyyar yara ta zama ke nan a karni na 21.
Tuni makarantu, a matsayinsu na wuraren da ya kamata a ce ana daukar darussa, suka zama mabubbugar tashe-tashen hankula.
Sace-sacen daliban makarantun kwana da suka ki karewa a Najeriya da harbe-harbe a makarantun Amurka sun isa su sa mutum ya fara tunanin anya ba wani gagarumin makirci ake kullawa don ganin an durkusar da bangaren ilimi gaba daya ba?
Muhimmancin zaman aji
Tun tale-tale ake makaranta, kuma aka tabbatar da fifikon zaman aji a kan sauran hanyoyin daukar karatu, hatta a wannan zamanin na daukar darasi ta intanet.
Baya ga darussan, yara kan koyi mu’amala da wasu halaye da za su taimaka musu a tsawon rayuwarsu.
Don haka ba sai an fada ba, karantarwa a aji na da matukar muhimmanci.
Amma, yaya za mu yi mu kare ’ya’yanmu?
A bi wa Hanifa hakkintaW
Wata fuska ta daban da za a iya kallon wannan lamari ita ce cin amanar da ‘malamin’ ya aikata.
A da, al’umma na girmama malami fiye da kowa saboda mutum ne shi da za ka iya danka mishi amanar yaro ka yi barcinka ba wani haufi.
Yanzu abin da wannan mutumin ya yi zai tarwatsa yardar shekara da shekaru da ke tsakanin masu makarantu da malamai.
Daga yanzu za a rika binciken kwakwaf a kan malamai a fadin Kano da ma Najeriya baki daya domin ba wanda zai kara amince wa wani.
Wanne rashin imani ne zai sa mutum ya sace yarinya, sannan ya je gidan iyayenta jaje, yana kukan munafunci?
Tabbas zuciyar mutum makare take da zalunci.
Al’umma na ta kiraye-kiraye cewa, in har aka tabbatar ya aikata wannan laifi, a kashe Abdulmalik Tanko shi ma.
‘Wanda ya cire wa wani ido, shi ma a cire mishi’, kamar yadda littattafai masu tsarki ke cewa.
Sai dai an karantar da mu cewa idan ana cire idon wadanda suke cire wa wasu, to makafi za su yi yawa a al’umma.
Amma a wannan karon ina ganin babu laifi idan yawan makafi ya karu, matukar za a samu raguwar satar mutane don neman kudin fansa.
Mutuwar yaro fa ba abar wasa ba ce.
Wannan fassara ce ta makalar da Dokta Fatima Damagum ta rubuta wadda aka wallafa a jaridar Daily Trust Saturday ta ranar 22 ga watan Janairu, 2022 mai taken ‘#JusticeForHanifa’.