Ina ji kamar in jagoranci zanga-zanga – Oshiomhole

Gwamnan Jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomhole ya yi gargadin cewa al’amura sun tabarbare a kasar nan ta yadda yake jin kamar ya yi bore kan halin da ake ciki.Gwamnan ya bayyana haka ne, lokacin da shugabannin kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) suka ziyarce shi a Benin, ranar Litinin da ta gabata.Ya ce, “A halin yanzu […]

Ina ji kamar in jagoranci zanga-zanga – Oshiomhole

Kwamared Adams Oshiomhole Gwamnan Jihar EdoGwamnan Jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomhole ya yi gargadin cewa al’amura sun tabarbare a kasar nan ta yadda yake jin kamar ya yi bore kan halin da ake ciki.
Gwamnan ya bayyana haka ne, lokacin da shugabannin kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) suka ziyarce shi a Benin, ranar Litinin da ta gabata.
Ya ce, “A halin yanzu wasu daga cikinmu sun damu kan abin da ke gudana a kasar nan, ba zan yi zanga-zanga ko bore ba ne a yanzu saboda za a yi min muguwar fassara, amma zuciyata tana son yin bore, domin ’ya’yana kada su gaji miyagun abubuwan da muke gani yau da gobe.”
Ya kara da cewa, “Muna cikin wani hali na kalubale, inda muke fama da ’yan bokon da aka ba su amanar mulkin kasa a matakai daban-daban da suka mayar da wannan mulki kayan gidansu, suna nuna kamar wasu alloli suna mugun cin zarafin marasa karfi tare da amfani da dukiyar kasa wajen yin abin da ke cutar da talakawa.”
Oshiomhole ya ce Najeriya ta nufi hadarin da zai iya tumbuke harsashinta. “Abubuwa suna gudana a wurina suna dauke da hadari mai girma. Akwai mutanen da ba su fatar alheri ga kasar nan kuma abin takaici akwai maza da mata da ba za su san inda suka nufa a kasar nan ba, ta yadda suke kokarin lalata makomar kasar ga kowa. Ya zama tilas al’ummar Kiristoci su fito su yi magana a inda ya kamata, ta yadda kurame bebaye za su ji, makafi ganinsu ya dawo ta yadda za mu hadu mu gina kasar da za ta kasance mai tsoron Allah, inda jama’a za su ci gajiyar albarkatun da Allah Ya albarkace mu da su.”
Ya ce, “Muna bukatar jajircewa a daidai lokacin da muka fuskanci zaben shekarar 2015 ta yadda kasar ba za ta kasance kamar kayan gadon wasu ba, domin jama’a ne kawai suke nan da’iman, amma shugabanni sukan zo ne su wuce, kuma wannan shi ne alkawarin dimokuradiyya, don haka muna bukatar ku taimaka mana.”
Gwamna Oshiomhole ya ce, “Don haka muna bukatar CAN wadda ta nuna karfin hali ta yi magana a lokacin mulkin soja, a yanzu da muke dimokuradiyya mun fi bukatar wannan karfinm hali.” Ya bukaci Kiristoci su ci gaba da yi wa kasar nan addu’a, inda ya ce, “Addu’o’in ’yan uwanmu Kirista da ’yan uwanmu Musulmi ke rike kasar nan.”
Tun farko Babbban Sakataren kungiyar CAN ta kasa Rabaran Musa Asake wanda ya wakilci shugaba kungiyar na kasa Fasto Ayo Oritsejafor ya ce, “Mu a kungiyar CAN muna farin ciki da abin da kake yi a Jihar Edo, mutanenmu maza da mata suna ci gaba da ba rahotannim irin goyon bayan da kake ba coci da kuma samar da ribar dimokuradiyya ga jama’a ta wajen yin ayyukan inganta jin dadinsu a fannin ilimi da kiwon lafiya da inganta rayuwar matasa da kayayyakin jin dadin jama’a.”