Ina jin dadin yin fim da Sha Rukh Khan – Sharib Hashmi
Sharib Hashmi, sabon dan fim a Indiya ya ce yana jin dadin fitowa fim tare da shahararren tauraro, Sha Rukh Khan. Ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da ya yi da ’yan jarida a Indiya.Sharib, wanda kafin ya fara fitowa cikin fim ya kasance Mataimakin Daraktan Fim, ya fito tare da Sha Rukh […]

Sharib Hashmi, sabon dan fim a Indiya ya ce yana jin dadin fitowa fim tare da shahararren tauraro, Sha Rukh Khan. Ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da ya yi da ’yan jarida a Indiya.
Sharib, wanda kafin ya fara fitowa cikin fim ya kasance Mataimakin Daraktan Fim, ya fito tare da Sha Rukh Khan a cikin fim din Jab Tak Hai Jaan a matsayin abokinsa, kamar kuma yadda ya jagoranci sauran ’yan wasa a fim din Filmistaan.
Da aka tambaye shi yadda ya fara harkar fim sai ya ce: “Na fara harkar fim ne da mukamin Mataimakin Darakta, inda muka yi aikin ba da umurni a fim din Hum Tumpe Marte Hain, inda bayan kammala fim din kuma na fara rubuta labaran fim ga gidajen talabijin. An nemi a yi gwajin ’yan wasan da za su fito cikin sabon fim din Haal E Dil sai na shiga aka yi da ni kuma na yi nasara aka zabe ni. Haka kuma na fito cikin fim din Slumdog Millionaire, duk da cewa ban fito wurare da yawa ba.”
Da yake kara bayani, dan wasan ya ce a 2008 ne ya aje aikinsa na ba da umurni, kuma sai da ya zauna tsawon shekara uku ba tare da ya yi wani abu muhimmi ba, in ban da fitowa da ya yi cikin gajeren fim din Mehrooni, wanda Faraz Ali ya yi aikin ba da umurni a cikinsa.
Da aka tambaye shi cewa ko yaya ya ji lokacin da suke aikin fim din Jab Tak Hai Jaan tare da Sha Rukh Khan? Sai ya amsa da cewa: “Hakika na ji dadin aiki tare da shi, domin kuwa ko alama bai nuna mani cewa ina aiki tare da babban jarumi ba. Ya kasance mai ba ni hadin kai matuka a yayin aikin, kamar kuma yadda ya kasance cikin sakin fuska da raha. Don haka a kullum ina sha’awar yin aikin fim tare da shi.”
dan wasan dai ya ce akwai manyan ’yan fim da suke burge shi baya ga Sha Rukh Khan, wadanda suka hada da Raj Kumar Hirani, Dibakar Bannerjee, Shimit Ameen da kuma Anurag Kashyap.