Ina Jinjina Ga Masu Zanga-zanga —Gwamna Makinde

Gwamna Oyo ya nuna matukar farin ciki a kan yadda matasa suka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa cikin lumana a jihar.

Ina Jinjina Ga Masu Zanga-zanga —Gwamna Makinde

Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya nuna matukar farin ciki a kan yadda kungiyoyin matasa suka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa cikin lumana a jihar.

Gwamnan ya jinjina wa matasan ne a bayan kwanaki uku da fara wannan zanga-zangar a kasa baki daya.

Bayanin haka yana kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Labarai, Yarima Dotun Oyelade, ya tura wa kafofin labarai a Ibadan babban birnin Jihar Oyo.

Ya ce kwanaki kadan kafin a fara zanga-zangar, Gwamna Makinde ya shiga sahun shugabannin da suka fara nuna goyon baya ga yin zanga-zangar lumana.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya musamman a jihohin da suka samu kansu cikin hargitsi a sakamakon zanga-zangar da su zauna lafiya kuma su kauce wa shiga cikin dukkan abun da zai iya janyo rikici da tashe-tashen hankulan jama’a.

Binciken Aminiya a kan irin rawar da mahukumta suka taka a Jihar Oyo kwanaki biyu kafin fara zanga-zangar, ya nuna cewa duka bangarorin mahukumta sun taka rawar gani wajen tabbatar da ganin an gudanar da ita lami lafiya.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Sonubi Ayodele, ya gayyaci dukkan masu ruwa da tsaki, inda ya yi wata ganawa da su a ranar Laraba, ya kuma shaida masu cewa rundunar ta kammala shirin kare lafiyar al’ummomi da su kansu masu zanga-zangar.

Sarakuna da shugabannin kungiyoyi da shugabannin bakin kabilu suna daga cikin mahalarta taron.

A waje daya kuma Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Oyo, Debo Ogundoyin, ya yi wata ganawa ta musamman da kungiyoyi 80 masu zaman kansu da suka hada da matasa da ’yan kasuwa da direbobi da malaman addini da manoma da makiyaya da makamantansu.

Ya yi ganawar ne kwana daya kafin isowar fara zanga-zangar inda ya shaida masu matsayin majalisar a kan zanga-zangar.

Hakazalika ya saurari shawarwarin mahalarta taron.

Ita ma Fadar Mai Martaba Olubadan na Ibadan ta umarci dukkan masu unguwanni da Dagattai da hakimai a masarautar mai kunshe da kananan hukumomi 11 su tabbatar da cewa sun isar da sakon sarki ga talakawa a kan bukatar yin zanga-zangar cikin lumana.

Tun farko sai da kungiyar ’yan asalin Ibadan (CCII) ta shafe kwanaki uku tana yin yekuwa musamman ga kungiyoyin da suka shirya yin zanga-zangar su tabbatar da cewa ba su tsani kowa ko yin amfani da siyasa wajen tayar da zaune-tsaye ba.

Binciken na Aminiya ya nuna cewa matakan da wadannan bangarorin mahukumta suka dauka tun kafin a fara zanga-zangar ya yi tasiri domin shi ne ya haifar da yin wannan zanga-zangar a Jihar Oyo cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.

Binciken ya nuna cewa mahukunta a sauran jihohi 5 da ke Kudu maso Yamma su ma sun dauki irin wannan mataki tun kafin a fara zanga zangar, inda  suka rinka ganawa da masu ruwa da tsaki wanda ya kai ga yin zanga-zangar lami lafiya ba kamar yadda aka saba yi a baya ba.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS