Ina kake? Inji Ubangiji Allah1
Sa’adda macen ta lura itacen yana da kyau domin ci, abin sha’awa ne kuma ga idanu, itacen kuma abin marmari ne domin bada hikima, sai ta debi ’ya’yansa, ta ci; ta kuma ba mijinta tare da ita, shi kuwa ya ci. Dukansu biyu kuwa idanunsu suka bude, suka waye kuma tsirara ne su; suka dindinke […]
Sa’adda macen ta lura itacen yana da kyau domin ci, abin sha’awa ne kuma ga idanu, itacen kuma abin marmari ne domin bada hikima, sai ta debi ’ya’yansa, ta ci; ta kuma ba mijinta tare da ita, shi kuwa ya ci. Dukansu biyu kuwa idanunsu suka bude, suka waye kuma tsirara ne su; suka dindinke ganyen baure, suka yi wa kansu mukuru. Sai suka ji muryar Ubangiji Allah yana yawo cikin gona da sanyin yamma: mutumin fa da mata tasa suka buya daga fuskar Ubangiji Allah a cikin itatu wan gona. Ubangiji Allah kuma ya kira mutumin, ya ce masa, INA KAKE?” (Farawa: 3:6-9)
Koda yake mutum ya aikata zunubi, kuma Ubangiji Allah ba Ya son zunubi domin Shi Mai tsarki ne, amma Allah Ubangiji Mai jinkai ne, Mai alheri ne kuma. Shi da kanSa Ya kudurta Ya nemo mutum Ya kuma tsamo shi daga cikin zunubi. Wannan shiri ba wai Adamu kadai ba ne, amma ga dukan mutanen da ke cikin duniyar nan duka; eh, da kai da ni.
Shaidan, a kullum zai yi gaba da shirin Allah domin mutum, Littafi Mai tsarki yana koya mana game da Iblis kamar haka “barawo ba yakan zo ba sai domin sata da kisa da halaka: ni na zo domin su sami rai, su same shi a yalwace kuma.” (Yohanna 10:10). Shaidan magabci ne a koyaushe, ba ya da shiri mai kyau ga kowane dan Adam, idan ya sami zarafin, zai bata duk kyawawan shiri da Allah Ya yi domin jin dadin rayuwar mutum. Ubangiji Allah Ya kwatanta Shaidan da barawo, aikinsa shi ne ya yi sata, ya yi kisa, ya halakar, ba ya da abin alheri ko daya; amma Allah Ya riga ya magance duk wannan shirin muguntar Shaidan domin irin kaunar da Yake da shi ga mutum. Maganar Ubangiji Allah ta koya mana cewa, “Wanda ya aikata zunubi na Shaidan ne; gama Shaidan yana yin zunubi tun daga farko. Dalilin bayyanuwar dan Allah ke nan, shi halaka ayyukan Shaidan.” (1Yohanna: 3: 8). Tun daga farko, lokacin da mutum ya yi zunubi, ya bar bin tafarkin Allah, ya soma nasa irin tunanin, wanda tushensa Shaidan ne; a kullum, tunanin mugunta ne ba na alheri ba, maganar Allah ta ce, “Amma Ubangiji Ya ga muguntar mutum ta yi yawa cikin duniya, kuma kowace shawara ta tunanin zuciyarsa mugunta ce kadai kullum.” (Farawa: 6 : 5). Haka mutum ya zama, ko a cikin rayuwarmu ta yau da kullum, abin da muke gani ke nan. Mutane ba su yin tunanin alheri domin ’yan uwansu, a kullum tunanin kansu ne kawai, masu iya magana suka ce so duka so ne amma son kai ya fi . Irin wannan tunani ba daga wurin Ruhun Allah ba ne, tunanin mutum ne wanda ya kasa ga darajar Allah. Duk wanda bai san Ubangiji Allah ba, babu yadda zai iya yin wani irin tunani idan ba na son kai ko mugunta ba, domin yanayin rayuwarsa ta riga ta canja: a cikin aya goma sha daya zuwa sha biyu na Farawa, Sura Shida, maganar Allah ta ce: “Duniya kuwa ta baci a gaban Allah, duniya kuma ta cika da zalunci. Allah Ya duba duniya, Ya ga kuwa, batacciya ce; gama dukan masu rai sun bata tafarkinsu a duniya.” Ina so mu gane wani abu da wuri a nan, yaduwar zunubi ba ta da wahala ko kadan, zunubi kan ci ne kamar wutar daji; ba lallai ne sai ka koyi aikata zunubi ba, idan an bar mutum haka ga karan kansa da halin zunubi ne zai tashi, halin son kai, halin mugunta, abin da mutum ke koya, shi ne bauta wa Allah.
Abin la’akari shi ne, idan Ubangiji Allah bai dauki matakin neman mutum ba, haka mutum zai halaka tare da Shaidan. Shi Iblis, shi ne ya aikata zunubi na farko, kuma ba shi da zarafin tuba, hakin aikin rayuwarsa shi ne Jahannama na wuta. Inda Shaidan yana so ya kai duk mutanen da sun ki bin maganar Allah, kuma sun ki bin hanyar da Ubangiji Allah Ya shirya domin ceton dan Adam, masaukinsu daya ne da masaukin Shaidan ranar da Yesu Almasihu zai dawo wannan duniya domin shari’a.
Mun ji irin kiran da Allah Ya yi ga mutum – INA KAKE? Har wa yau Allah na kiranka da babbar murya, Ina kake? Mutane sun rigaya sun bata, sun bar bin tafarkin Allah, sun shiga halin bauta wa Shaidan da kuma aikata nufinsa, sun taurare ga Ubangiji suna gani kamar sun waye ashe wauta ce. Mai yiwuwa ne kana zuwa sujada a Ikilisiya tare da wadansu masu bin Yesu Kiristi, amma muddin rayuwarka bai cacanci rayuwar da za a iya ce da ita ta Kirista ba, to babu shakka masaukinka tare da Shaidan ne a ranar karshe.
A binciken da muka yi makonnin da suka gabata, mun ga yadda Allah cikin kaunarSa, Ya kashe dabba ya zub da jinin dabbar, Ya kuma cire fatar dabban ya yi wa mutum sutura. Suturar da mutum ya yi wa kansa ba za ta dade ba, ko kadan domin da ganye ya yi ta; mun gani cewa babu yadda za a sami fatar dabba idan ba ya yanka ko an kashe ba, kuma ta kowane fanni muka duba, dole ne jinin wannan dabbar ya zuba. Haka nan take,