Ina karanta Alkur’ani kullum – Tony Blair

Tsohon Firayi Ministan Birtaniya, Mista Tony Blair ya ce yana karanta Alkur’ani a kullum sakamako yadda Alkur’anin ‘yake kara masa imani.’Mista Blair wanda ya rungumi darikar Katolika ‘’yan watanni bayan ya sauka daga mulki a shekarar 2007 ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Mujallar Obserber a ranar Litinin da ta gabata.Mista Blair ya kara […]

Ina karanta Alkur’ani kullum – Tony Blair
Ina karanta Alkur’ani kullum – Tony Blair

Tsohon Firayi Ministan Birtaniya, Mista Tony Blair ya ce yana karanta Alkur’ani a kullum sakamako yadda Alkur’anin ‘yake kara masa imani.’
Mista Blair wanda ya rungumi darikar Katolika ‘’yan watanni bayan ya sauka daga mulki a shekarar 2007 ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Mujallar Obserber a ranar Litinin da ta gabata.
Mista Blair ya kara da cewa: “Domin kara samun imani yana da matukar muhimmanci a duniyar da ta zama a dunkule, na yi imani. Ina karanta Alkur’ani a kowace rana. Dalili domin in fahimci wasu abubuwa da suke faruwa a duniya, amma galibi domin yana matukar shiryarwa.”
Mista Blair ya ce yana da yakinin sanin addinin Musulunci ne ya sanya shi kasancewa Jakadan Majalisar dinkin Duniya da na Amurka da na Tarayyar Turai da kuma na Rasha a yankin Gabas ta Tsakiya.
 Mista Blair ya rika yaba wa Musulunci inda ya rika bayyana shi da “mai kyau” tare da bayyana Annabi Muhammad (SAW) da ‘babban jigon wayewa.’
A shekarar 2006 ya bayyana Alkur’ani da cewa “Littafi ne da ya kawo sauyi kuma ya dace da kowane zamani. Ya daukaka kimiyya da ilimi kuma ya kyamaci camfe-camfe. Ana amfani da shi kuma hanya ce a kowane lokaci kan abin da ya shafi zamantakewar aure da hakkokin mata da ma gudanar da shugabanci.”
Don haka ya rika nuna mamaki kan yadda wadansu suke fassara Alkur’ani a gurgunce suna kashe jama’ar da ba su ji ba, ba su gani ba, da sunan jihadi
Yana shugabancin Ingila ne aka kai harin bam na 7 ga Yulin shekarar 2005 inda aka kashe mutane 52.
Ba ya ga karanta Alkur’ani, wani abin da ya taimaka wa Mista Blair ya kasance Jakadan zaman lafiya, shi ne wata surukarsa mai suna Lauren Booth.
’Yar jarida Misis Booth – kanwar matarsa Cherie Blair – ta tayar da kura bayan da ta bayyana karbar addinin Musulunci a watan Oktoban bara a kasar Iran.