Ina kera kayan da suka fi na kasashen waje inganci – Ahmed Idris

Aminiya ta samu tattaunawa da Ahmed Idris Zariya wanda ya kware wajen kere-keren abubuwa iri-iri da mutane suke amfanin yau da kullum da su. Cikin abubuwan da yake kera wa akwai injin yin kankara da abin gasa nama da abin kwashe shara na zamani da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Za mu so […]

Ina kera kayan da suka fi na kasashen waje inganci – Ahmed Idris
Ina kera kayan da suka fi na kasashen waje inganci – Ahmed Idris

Aminiya ta samu tattaunawa da Ahmed Idris Zariya wanda ya kware wajen kere-keren abubuwa iri-iri da mutane suke amfanin yau da kullum da su. Cikin abubuwan da yake kera wa akwai injin yin kankara da abin gasa nama da abin kwashe shara na zamani da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka?
Ahmed Idris: Sunana Ahmed Idris Zariya. Ni kwararre ne a harkar kere-keren karafuna. An haife ni a garin Zariya da ke Jihar Kaduna a yankin Arewacin kasar nan. Yau shekaru fiye da 67 da suka gabata ke nan. Kodayake ban yi karatun boko mai zurfi ba, amma na yi karatun zamani zuwa matakin makarantar firamare, inda na kammala a makarantar Nurul Huda da ke Unguwar Tudun Wada da ke garin Zariya a Jihar Kaduna. A halin yanzu matana uku ’ya’yan tara.
Aminiya: Ta yaya ka fara ita wannan sana’ar?
Ahmed Idris: Ni dai ba gadar wannan sana’a na yi ba. Na shige ta ne da rana tsaka. Na fara tun ina da shekaru 20 a duniya a garin Zariya. Na koyi sana’ar a wurin wani maigidana daga bisani na koya na kware a cikinta. Kuma ni mutum ne mai sha’awar kere-kere da kuma walda tun ina karami. To akwai lokacin da na tafi garin Jos na tarar da wasu abokanaina suna yin sana’ar. Akwai wani abokina mai suna Umar Lafiya da shi muka fara sana’ar. Akwai wani maigidana da na koyi aiki a wurinsa mai suna Muhammed Sani dan-Zariya. Tun muna kera akwatuna daga bisani sai muka fadada sana’ar muke yin abubuwa daban-daban kamar injin kankara da injin kwashe shara da sauran abubuwa iri-iri.
Aminiya: Wadanne irin abubuwa kake kerawa?
Ahmed Idris: Gaskiya ina kera abubuwa da yawa kamar injin kankara da akwatin kwashe shara da kofofi manya da kanana da abin soya kaza da na gasa biredi da nama da sauransu sannan ina kera karamin injin sarrafa kayan tande-tande da lashe-lashe na zamani.
Aminiya: Wadanne kalubale kake fuskanta a lokacin da kake koyar wannan sana’ar?
Ahmed Idris: Gaskiya na  sha wahala sosai a lokacin da nake koyar wannan sana’a domin a lokacin ni nake daukar dawainiyar kaina. Kodayake a lokacin ba ni da iyali ban yi aure ba, amma na sha gwagwarmaya sosai. A lokacin da kyar nake samun abinda zan ci abinci ko na yi sutura.
Aminiya: Me ya sa ka yanke shawarar zuwa garin Abuja a maimakon ka gudanar da sana’ar a Zariya?
Ahmed Idris: To kasan komai kaddara ce daga Allah. Na zo Abuja tun fiye da shekaru 20 da suka gabata. A lokacin da na zo sai na lura sana’armu tana ci gaba. Saboda haka sai na yanke shawarar na zo na bude reshe. Kusan zan ce ni ne mutum na farko da na fara bude sana’ar a kasuwar Wuse daga bisani saboda lamarin yadda garin yake na taso na dawo tashar Utako. Kuma na gode wa Allah komai na tafiya daidai muna samun dan abinda da za mu ci.
Aminiya: Ta yaya kake kera injin kankara?
Ahmed Idris: Shi injin kankara yana bukatar abubuwa da yawa. Bayan kwarangwal din inji akwai bututu da ake hada shi da wayar lantarki a cikinsa sannan kuma sai na hada da na’urar sanyaya daki. Da an hada sai ka ga ya bayar da abin da ake so.
Aminiya: Shi kuma injin gasa nama fa?
Ahmed Idris: Shi injin gasa nama iri-iri ne akwai wanda yake fitar da hayaki sama akwai kuma wanda ba ya fitar da hayaki. Akwai wanda nake yi nake hada masa na’urar iskar gas ko kuma na’urar bona.
Aminiya: Nawa kake kashewa wajen kera injin kankara?
Ahmed Idris: Ya danganta da girmansa. Iri-iri ne akwa karami akwai babba. Misali wanda yake iya daukar kankara dari da hamsin. Zai ci maka naira dubu 150 kuma idan ka gama shi za ka iya sayar da shi naira dubu 180 zuwa dubu 200. karamin injin kankara mai daukar  kankara hamsin za ka iya kashe kimanin naira dubu 50 ka sayar da shi dubu sittin akwai kuma wanda za ka iya kashe dubu sittin ka sayar da shi dubu saba’in. Shi kuma injin gasa nama idan za ka yi da kayan aiki masu inganci za ka kashe naira dubu 60 ka sayar da shi dubu saba’in ko tamanin.
Aminiya: Wadanne nasarori za ka iya bayyanawa ka samu tun lokacin da ka fara sana’ar zuwa yau?
Ahmed Idris: Na samu nasarori masu yawa. Musamman ma yadda na koyar da yara fiye da hamsin. A yanzu haka suna gudanar da sana’ar a wurare daban-daban. Wasu kuma suna rike da iyalinsu.
Aminiya: Wadannane kalubale kake fuskanta?
Ahmed Idris: Babban kalubale shi ne rashin samun tallafi da ba ma yi daga gwamnati. Duk sana’ar da ka sani tana bukatar a rika bai wa mai yin ta tallafi. To mu a Najeriya gwamnati ba ta ba mu komai kuma ba ta yin hulda da mu. Akwai abubuwan da na ke kerawa wadanda sun fi na kasashen waje karko da amfani amma gwamnati ba ta tallafa mana. Idan da gwamnati za ta tallafa mani babu shakka zan rika kera abubuwa masu inganci da mutane za su amfana. Misali ni ne mutum na farko da na fara kera abin kwashe shara da ake amfani da shi a Abuja. Har ta kai an daina shigowa da na kasashen waje. Akwai wani jami’in gwamnati da ya fara zana mani shi, yana kawo wa na kera shi ba tare da wata matsala ba. Ya yi kyau fiye da na kasashen wajen.
Aminiya Me ye burinka a wannan sana’ar?
Ahmed Idris: Burina shi ne idan na samu yadda nake so shi ne na ga na bude katafaren kamafani, inda zan sanya manya-manyan injina da zan rika kera manyan abubuwa wadanda mutane za su rika amafana da su. Saboda haka ina bukatar tallafi daga gwamnati ko kuwa kamafanoni masu zaman kansu.