Ina mafitar tabarbarewar ilimi a Arewa?

Tabarbarewar ilmi ta shafi ko’ina a kasar nan, amma fa ta fi illa a Arewa. Mutum zai iya gane haka ne idan ya kalli yawan dalibai ‘yan Arewa da ke manyan makarantun kasar nan. Kuma ya kwatanta su da yawan daliban ‘yan kudu da ke wadanan nan makarantu. Wadannan makarantu kuwa sun hada da jami’oi […]

Ina mafitar tabarbarewar ilimi a Arewa?
Ina mafitar tabarbarewar ilimi a Arewa?

Tabarbarewar ilmi ta shafi ko’ina a kasar nan, amma fa ta fi illa a Arewa. Mutum zai iya gane haka ne idan ya kalli yawan dalibai ‘yan Arewa da ke manyan makarantun kasar nan. Kuma ya kwatanta su da yawan daliban ‘yan kudu da ke wadanan nan makarantu. Wadannan makarantu kuwa sun hada da jami’oi da kolejojin kimiyya da fasaha da kuma mayan makarantun horar da malamai. Abin bakin ciki shi ne, in ka je irin wadannan makarantu da ke Arewa za ka iske cewar ana kan-kan ne a tsakanin dalibai ‘yan asalin Arewa da kuma ‘yan kudancin kasar nan. Amma kuma idan ka je irin wadannan makarantu da ke Kudu za ka samu cewa ‘yan Arewa da suke a irin wadannan makarantu ko kashi biyar cikin dari ba za su yi ba. Me yasa har yanzu muke kurar baya ?

Farko dai, gwamnatoccin Arewa ba su ba da muhimmacin da ya kamata wajen ci gaban ilmi. Wannan ko ya hada da gwamnatocin jihohi da kuma kananan hukumomi. Babbn gararin da muka shiga a Arewa bayan dawowar mulkin siyasa shi ne yadda a ka yi wa bagaren ilmi rikon sakainar kashi. Domin su ’yan siyasa sun fi ba da muhimmanci ne ga ayyuka da za ka gani da ido, kamar gine-gine da sauransu, irin waddannan ‘yan siyasar za su iya kashe makudan kudi domin gina ajijuwa bila adadin. To amma ai wannan baya ba zane ne aka yi. Tun da an gina ajujuwa, amma kuma ba malamai da kayan aiki. Shi yasa a yanzu dukkan jihar da ka ziyarta a Arewa za ka samu makaran tun da dalibai suke karatu a kasa. A wasu gauraren ma ko ajin babu sai dai ka tarar ana karatu a karkashin bishiya. Kuma abin bakin ciki a irin wadannan jihohi ne ake kashe bilyoyin Naira wajen gina filin jigin sama, kawai don a samu abin fada a wajen kanfen. Na tabata in dai ba don talakawa za’ayi, kuma ba don amfani mai dorewa to bayar da ilmi mai inganci ya fi gina filin jirgin sama muhimmanci.
Wata matsalar da rashin ko in kula na gamnatocin mu ta haifar shi ne yadda ake daukar malaman da ba su cancanta ba. A wasu makarantu za ka iske akwai malamai masu yawa, musamman ma a makarantun sakandare da Firamare da suke a manyan birane, to amma abin bakin ciki shi ne mafi yawan su ba su cananta su koyar ba. Yanzu mun shigo mulkin siyasa, inda za ka ga ana tursasa ma’aikatun ilmi na jihohi da na kananan hukumomomi su ba da takardun daukar aiki ga mutanen da ba su da kwarewa, don su koyar a makarantu. Kawai in dai ka san wani dan siyasa to kai kayan ka ya tsinke gidin kaba. Kwanakin bayana, ji wani sakataren ilmi na wata karamar hukuma a daya daga cikin manyan biranen arewacin kasar nan yana ko kawa da yadda fiye da 70 cikin 100 na malaman da ke koyarwa a makarantun Firamaren mata ne. Kuma illar anan, ba wai ta kasancewar su mata ne kawai ba, a’a, sai dai don rashin cancantarsus. Domin kuwa shi sakataren ilmi ba yadda yaka iya , domin kuwa wadannan matan, mazajensu sun taimaka wa jam’iyya mai ci wajen cin zabe. Kun ga kenan dole ne a saka musu. Hanya mafi sauki ita ce a ba su koyar wa a makarantu. Kuma irin wadanana mata.
Sannan su kansu ma’aikatun ilmi na wadannan jihohi ba sa bayar da kulawa kan yadda tsarin koyarwa ke tafiya a makarantu. A kowacce ma’aikatar ilmi akwai sashen da aka dora wa nauyin bibiyar makarantu akai-akai, don su tabbatar da cewar ana koyarwa kamar yadda ya kamata, to amma yanzu ba ka ganin irirn wadannan masu bibiyar abin da yake gudana a makarantun da ake kira ‘inspectors’. A da, irin wadannan masu duba makarantun sun ba da gagarumar gudun mawa wajen ci gaban ilmi. Domin kuwa su kan je makarantu akai akai don su ga yadda malamai ke koyarwa. Kuma suga dukkan matsaalolin dake damun makarantun. To amma yanzu abin ya canza. Wata kila shima wannan zamu iya dangan ta shi da rashin kulawar gwamnatocin mu na jihoshi da na kananan hukumomi.
Ni din nan, na san a lokacin da nayi firamare, wato a waja jen shekaru talatin da suka wuce irin wadannan masu za ga makarantu sanannu ne. Do min kuwa ko da yaushe za ka gansu a kekunan su suna shiga lungu lungu don duba makarantun firamre. Ahali yanzu haka ma akwa wani tsaho ma, a yankin mu, da tuni yayi ritaya, amma har yanzu yana amsa sunan b.T., wato ‘bisiting teachers’.
Wata matsala da ta dada kassara ilmi a arewa itace, a tunanin mafi yawan ‘yan arewa, tun da ba a saman aiki yanzu, to ba bukatar ma su tura yaran su makarata. Sun gwammace su tura su karatun allo su yi ta bara. Idan kuma sun girma, su fara zuwa rani da kadar raba don neman kudi. Wani lokaci ma suje Kudancin kasar nan inda za ai ta wulakanta su. Anan mutane ba su da wayewar da zasu gane cewar shi ilmi ba ana yin sa bane kawai don a samu aikin gwamnati. In muka dau Kasashen da suka ci gaba, mafi yawa da mutanen su da suke da ilmi ba gwamnati suke yi wa aiki ba. Shi ilmi yana ba ka dama ne ka samu tunanin ka, ta yadda zaka iya rike kanka da kanka. Domin da ilmi ne mutum zai iya zamanan tar da dukkan sana’o’in mu na da, kamar noma, jima, kira, rini da dai sauransu. Kuma ma in muka duba sai muga cewar ai su ‘yan kudu har yanzu basu yi sako sako ba da sa yaran su a makaranta duk da cewar yanzu ba’a samun aikin gwamnati. Wanana yana nuna cewar, in mu a arewa muka sake to wata rana ‘ya’yan mu da jikokin mu sune zasu rinka yiwa wadannan ‘yan Kudu bauta.
Sabo da haka ya zama wajibi ne ga dukkan mu muba da himma wajen cigaban ilmi a arewa, musamman ma gwamnatocin mu na jihohi da kuma na kananan hukumomi. Lallai ne ‘yan siyasa su ba ilmi muhimmanci. Kuma su dai na yi masa rikon sakainar kashi, a wani lokaci, ba abu ne da za a gani ba da ido kuru-kuru. Kuma shi ilmi abu ne da yake da bangarori masu yawa. Alal misali gina ajujuwa kawai ba zai waddatar ba, har sai an samar da kayan aiki kuma an samar da wadatattun malmai kwararru.
Wani bangare kuma da ya kamata a bai wa mihimmanci, shi ne, na yaki da jahilci.Ya kamata Gwamnomin Arewa su yi koyi da Gwamanan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, kan yadda yake bai wa wannan bangare muhimmanci a Kano. Har wa yau, ya kamata gwamnatocin mu su samar da wani yanayi ta yadda wadanda suka gama makaranta za su iya samar wa kansu ayyuka, kuma ma har su samar wa wadansu. Wannan shi zai sa mutane su daina dari-darin tura yara makaranta ta dalilin rashin akin yi. Idan aka aiwatar da wadannan tsare-tsaren, to ilmi a Arewa zai farfado sosai. Yunus Ahmed Kabo, Kano

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi