Ina magadan Sardaunan Arewa?
A ranar Laraba, 15 ga watan Janairu ce wasu shugabannin Jamhuriya ta farko suka cika shekaru arba’in da bakwai da wafati, sakamakon kisan gillar da sojojin wani sashen kasar nan suka yi masu bisa dalilan siyasa da kuma kabilanci. An bindige Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Jihar Arewa na farko, kuma na karshe a […]
A ranar Laraba, 15 ga watan Janairu ce wasu shugabannin Jamhuriya ta farko suka cika shekaru arba’in da bakwai da wafati, sakamakon kisan gillar da sojojin wani sashen kasar nan suka yi masu bisa dalilan siyasa da kuma kabilanci. An bindige Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Jihar Arewa na farko, kuma na karshe a gaban iyalansa, aka kuma kashe abokin hadakarsa ta siyasa, Firimiyan Jihar Yamma, Chief Samuel Ladoke Akintola, aka kuma makure Firayiminista Sa Abubakar Tafawa balewa kuma shugaban Gwamnatin Tarayyar Najeriya, don a kawo karshen mulkin jam’iyyar Northern Peoples Congress, NPC wacce ke mulkin kasar bisa tafarkin dimokuradiyya.
Abin da ya ba kowa mamaki game da haka shi ne wani gungu hafsoshin Najeriya, ‘yan kabilar Ibo ne zalla suka aiwatar da wannan aika-aikar, kuma ko da suka kashe shugaban gwamnati da wasu biyu daga cikin firimiyoyin jihohi guda hudu, ba su kashe na Jihar Gabas, Chief Mikel Okpara, dan kabilar Ibo ba, da takwaransa na Jihar Yamma-ta-Tsakiya, Chief Dennis Osadebay, dukkansu ‘yan jam’iyyar adawa ta NCNC. Wannan ya nuna a zahiri cewa an yi haka ne don a nakasa mulkin jam’iyyar NPC ta Arewa da kuma kawarta, Nigerian National Democratic Party, NNDP ta mutanen Yammacin kasar nan don a dasa tsarin ‘yan kabilar Ibo kamar yadda daya daga cikinsu, Manjo-Janar Thomas Johnson Amunikwe Aguiyi Ironsi ya gaji mulkin Najeriya da tsinin bindiga.
Tun daga lokacin nan Najeriya ba ta sake zama lami lafiya ba har ya zuwa yau, domin kuwa bakin burin wadancan Ibon da suka nemi yi mata hawan kawara bai kai ga biyan bukata ba, ba su kuma hakura da kirkiro fitintinu irin wadanda suka yi ta haddsawa ba kamar yadda suka saba yi ga dukkan gwamntin da aka kafa a kasar nan, walau ta soja ce ko ta farar hula. Dangane da haka ne Najeriya ke cikin mawuyacin matsayi a halin yanzu fiye da wanda ya haddasa yakin basasar da aka yi watanni 30 ana fafatawa da ‘yan kabilar Ibon da suka fara tayar da fitina a kasar nan, sakamakon ballewar yakin Gabashin kasar don Ibo sun kasa samun yadda suke so.
A wancan lokaci sun fahimci cewa harkar mulkin kasar nan sai ‘yan Arewar da hatta ma Turawa suka jinjina masu. Sa’annan sun gane cewa idan dai har za a ci gaba da bin tafarkin dimokuradiyya babu yadda za a yi su samu galba kan jama’ar Arewar da ke yawan samun nasara a dukkan zabubbuka don rinjayensu a kasar. A yanzu ma abin da ke faruwa ke nan, sun tabbatar da cewa babu ta yadda za a yi su ga wallen ‘yan Arewa a siyasance idan ba amfani da bambancin addini da kabilanci suka yi ba don rarraba kawunan ‘ya’yanta.
Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya shige gaban ‘yan Kudu, domin kuwa ya dunkule Arewar da ke da mabambantan kabilun da suka kasance masu yi masa mubaya’a da biyayya saboda adalcin da ya shimfida wajen mu’amalarsa da dukkan kabilun Jihar Arewa da kuma janyo wadanda ba mabiya addininsa ne ba a jika. Haka nan kuma Sa Ahmadu Bello ya nuna matukar kauna ga sarakuna da al’ummomin yankin Tsakiya (Middle-Belt) da a yanzu ake kira yankin Arewa ta Tsakiya (North-Central Zone), kuma hakan ne ya sa suka ba shi cikakken goyon baya har jama’arsu suka rungumi dukkan manufofinsa, aka tafi tare, ba wata tangardar da ta kawo rashin jituwa. Ta haka ne Sardauna Ahmadu ya yi ta samun nasarori a fannonin siyasa da mulki cikin ruwan sanyi.
Sardauna Ahmadu Bello ya kare mutuncin Arewa daga ‘yan kudun da suka nemi yi mata hawan kawara, kuma cikin dan kankanin lokaci, bayan zamansa Firimiyan Jihar Arewa a 1954, ya kuma samar da ci gaba mai ma’ana ta fannoni da yawa bisa tsarinsa na daukaka matsayin jiharsa ta yadda idan ba ta wuce sauran ba, to kada ta zame koma bayansu. A sakamakon haka Arewa ta bunkasa, aikin gona ya habaka. Wannan ne ya haifar da masana’antun da suka samar da arziki da wadata a gidajen talakawa, har ta kai wani ban kashin na wani.
Babban nasarar da Ahmadu Bello ya samu shi ne habaka ilmin da ya ba ‘yan Arewa daman jan ragamar jiharsu da ma Najeriya baki daya, alhali kuwa tun can farko ‘yan Kudu sun yi masu fintinkau a fannin ilmin boko, sun riga su farawa fiye da shekaru 75. Amma babban abin da za a rika tunawa da Sardauna shi ne fafutikarsa ta hada kan Arewa ta hanyar kawar da kabilanci da bambancin addini, abin da ya karfafa zaman lafiyar al’umman cikinta, domin kuwa a lokacinsa zaman lafiyar Arewa shi ne zaman lafiyar kasar nan. Shi ya sa tun daga lokacin da aka yi masa kisan gilla aka yi ban-kwana da zaman lumana a kasar, amma hakan bai isa ishara ba ga makasansa wadanda har gobe suna nan kan bakarsu ta tayar da sabuwar husuma don cimma bakin burinsu na daidaita Arewa da jama’arta, kuma bisa ga dukkan alamu sun fara cin nasara game da hakan domin managartar shugabanni a Arewa da za su kwatanta ayyukan Sardauna wajen kare mutuncin yankinsu duk sun kau. Yanzu dai ga masu kiran kansu Sardauna bila adadin, amma babu mai kwatanta halin Ahmadu Bello, ga kuma Arewar na ta shan wuya, babu abin da suka iya.