Ina makomar Arewa a Najeriya? (2)

  Ga fahimtata shugabanni da mutanen kasar nan ne suke bukatar su sake fasalin kansu, su sake fasalin tunaninsu. Duk tsarin da za a kawo a kasar nan in dai shugabanni da mutanen kasar suna nan kan irin tunaninsu, suna nan kan irin fahimtarsu, suna nan kan halinsu, to wannan tsari da za a kawo […]

Ina makomar Arewa a Najeriya? (2)

 

Ga fahimtata shugabanni da mutanen kasar nan ne suke bukatar su sake fasalin kansu, su sake fasalin tunaninsu. Duk tsarin da za a kawo a kasar nan in dai shugabanni da mutanen kasar suna nan kan irin tunaninsu, suna nan kan irin fahimtarsu, suna nan kan halinsu, to wannan tsari da za a kawo ba zai canja komai ba, ba zai kawo wata nasara ko ci gaba ba.

A baya mun bayyana cewa tun farko Malam Sa’adu Zungur ya nuna kada ma a hade Arewa da Kudu kowa ya kama gabansa, saboda lurar da ya yi cewa wannan aure ba za a yi zaman dadi ba. Kuma da aka hada wannan auren dole, shekara nawa aka yi abin da yake gudun ya auku? To ba abin da ya aukun ne abin takaici ba, a’a shugabannin Arewa da suka biyo baya ne ababen takaici. An nuna wa ’yan Arewa ba a sonsu, an nuna musu ba a kaunarsu a tafiyar wannan kasa, amma kuma abin takaici har zuwa yanzun nan ba su hankalta ba. Me ya sa na ce haka?  Zubin shugabannin da muka samu a wannan jamhuriyya hakika hankalinsu galibi a bakin zane yake, mulkin kawai suke so ba tunanin makomarsu da ta al’ummarsu ba. Idan ba haka ba, irin mahaukatan kudin da kasar nan ta samu daga 1999 zuwa 2014, a ce babu wani Gwamna a Arewa da ya gina sabuwar madatsar ruwa ta Naira biliyan daya a jiharsa, amma an samu gwamnonin suna gasar gina filayen saukar jiragen sama a jihohin nasu? Ina amfanin gina filin jirgin sama a Bauchi da Gwamna Isa Yuguda na Jihar Bauchi ya yi alhali kullum yana kukan Gwamnatin Tarayya ta zo ta karasa ginin madatsar ruwa ta Kafin Zaki? Me ya sa bai karasa ginin madatsar ruwa ta Waya ba? Me ya sa bai giggina madaidaita da kananan madatsun ruwa a sassan jihar ba wadanda manoma da makiyaya a yankunan karkara za su dogara da su ba, wajen inganta harkokinsu ba? Me ya sa bai inganta harkokin noma ya zamo mai dorewa a jihar ba, ta yadda za a raba dubban daruruwan matasa da zaman kashe wandon da ke kai su ga aikata miyagun ayyuka na Sara-Suka ba? Shin da an inganta harkokin noma hakan ba zai inganta harkokin kiwo da kasuwanci ba? Shin hakan ba zai inganta harkokin kasuwanci ba? Shin hakan ba zai taimaka wajen rage dogaro da aikin albashi a jihar ba? A yau idan aka ce babu albashi a Jihar Bauchi to fadar jihar kusan komai tsayawa yake yi. Babu masana’antu ko kamfanoni, babu wasu cibiyoyi na samar da kudin shiga ga jama’a, amma ya gina filin jirgin sama da amfaninsa daga lokacin aikin Hajji sai aikin Hajji! Ina amfanin gina filin jirgin sama a Dutse da Gwamna Sule Lamido na Jihar Jigawa ya yi? Wane ne zai rika hawa jirgin zuwa Dutse, me zai je ya yi a jihar da ba ta da wani kamfani ko wata fitacciyar harka ta tattalin arziki? In da madatsun ruwa ya giggina a yankunan jihar dubban mutanen Jihar Jigawa nawa ne za su amfana? Haka lamarin yake a Jihar Kebbi, filin jirgin sama tsohon Gwamna Dakingari ya gina a kauyen Zauro da ke tsakanin Birnin Kebbi da Argungu. Wadannan jihohi uku duk jihohi ne da bukatar a inganta aikin gona da samar musu da ruwan sha ta fi muhimmanci a kan wani abu wai shi filin jirgin sama. Kuma babban abin takaicin gwamnonin nan sun giggina filayen jiragen saman ne a daidai da ita kanta Najeriya a matsayinta na kasa ba ta da ko jirgin sama daya! Sannan filayen jiragen saman nan ba fa kudin shiga za su kawo wa jihohin ba, sai dai jawo musu asara. In muka leka Kano, tsohon Gwamnan Kwankwaso duk da sanin muhimmancin giggina madatsun ruwa ga ci gaban tattalin arzikin jihar da mutanenta, sai ga shi ya narkar da biliyoyin Naira wajen gina wasu rukunnan unguwanni masu suna biranen Kwakwasiyya da Bandirawo da Amana, kudin da aka narkar a wadannan rukunin gidaje madatsun ruwa nawa za su iya ginawa? Me ya sa ya zabi ya gina gidaje bayan amfaninsu bai kai kashi 5 cikin 100 na gina madatsun ruwa ba? Shin wace riba ke cikin gina irin wadannan gidaje na alfarma da kashi 90 na mazauna jihar ba za iya sayensu ba? Me ya sa bai karasa aikin noman rani na Kadawa ba? Me ya sa bai kirkiro wani sabon shirin noman rani a sauran sassan jihar ba?

Idan aka zagaya galibin jihohin Arewa haka lamarin yake, galibin ayyukan da gwamnoni suke yi gine-gine ne da za su samu damar tafka sata da almundahana, babu tunanin makomar yankinsu da jama’arsu.

To ga irinta nan a yau a ce kowane yanki ya rike arzikinsa, me Arewa za ta dogara da shi? Noma ko me? Idan noma ne ta ina za a fara? Talakawa za a rika kamawa ana kaiwa gandun gwamnati ko kuwa harajin rashin imani za a dora musu domin a samu tafiyar da harkokin gwamnati a yankin? Ko kuwa za a hakura ne da harkar gwamnati a kori ma’aikata a ce kowa ya san inda dare ya yi masa? Ba ina magana ne a kan talaka ba, wanda dama can an sanya batunsa a mala, ina magana ne kan ayyukan hukumomin gwamnati da ita kanta gwamnatin. Ina za a samo kudin gudanar da su tunda babu kudin ‘banza’ da ake samu daga man fetur? Misali na ji Gwamnan Jiharmu ta Bauchi yana cewa wai yana biyan kimanin Naira biliyan biyar a matsayin albashi duk wata, alhali Shugaban Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Jihar Alhaji Yakubu Isah ya shaida wa jaridar Aminiya a makon jiya cewa a bara hukumar ta tara Naira biliyan shida da miliyan 250 ne a shekarar gaba daya, wato in abin da Gwamna M.A.Abubakar ya fada gaskiya ne game da albashi, to albashin wata daya da doriya kawai jihar take iya samu a shekara, ka ga dole za a dakatar da tafiyar gwamnatin ke nan idan aka ce kowa ya ci tuwon gidansu! Haka galibin jihohin Arewa suke, shugabanninsu sun kwanta da sirdi, suna magagin barci a lokacin da shugabannin Kudu ke ci gaba da yakin kowa-ya-ci-tuwon-gidansu!

Baya ga noma da aka yi watsi da shi, shugabannin Arewa ba su yin wani katabus na hako albarkatun kasa da suke yankunansu, sun bar lamarin a hannun wadansu shafaffu da mai suna ta lalata muhalli da sunan hako ma’adinan. Su suna zama miloniyoyi yankunan da suke hako ma’adinan suna zama fakiran fukara’u.

Don haka tilas ne shugabannin Arewa su sake tunani su sani makomar Arewa tana hannunsu, makomar Arewa tana hannun ’yan Arewa! Abubuwa da dama suna tafiya ba daidai ba a Arewa, amma wannan ba damuwar shugabannin yankin ba ne, kullum tunaninsu yaya za a yi su tara dukiyar da za su nemi mukami na gaba? Takwarorinsu na Kudu da sarakunansu suna can suna ta gudanar da tarurruka kan matsayar da za su dauka, su kuma a nan sun yi gum da bakunansu, sai batun tsayawa takarar zaben shekarar 2019 suke yi. Kusan kowa yana sane da cewa, hauragiyar neman kasar Biyafara da su Nnamdi Kanu suke yi, ba haka kawai suke yi ba, suna yi ne tare da daurin gindin manyansu wadanda akalla burinsu su tursasa ’yan Arewa su sarayar da wasu hakkokinsu don kawai a biya musu wasu bukatunsu. Wannan ne fa ya tunzura wasu kungiyoyin matasan Arewa suka ce tunda Ibo ba su son zama a Najeriya su tattara nasu-ya-nasu su koma yankinsu cikin wata uku don a huta da barazanar da suke yi. Amma sai namu shugabannin suka fara la’antarsu.

Idan aka dawo kanmu mu talakawa haka muke tafiya kara-zube, ba mu da tsari a al’amuranmu, aurenmu ne, kula da ’ya’yanmu ne, kasuwancinmu ne, neman iliminmu ne, hatta yadda muke gudanar da addini abin cike yake da ban takaici. Muna neman zama tamkar garken tumakin da ba su da makiyayi, muna neman zama tamkar garken tumakin da kerkeci ya koro daga daji. Ba mu dauki shugabanci da kima da muhimmanci ba, koda a tsakanin kungiyoyinmu balle a tsakaninmu da shugabannin da suke matakan mulki. Mu ke nan daga tsinuwa sai zagi, daga kaharu sai jafa’i, sharri bayan sharri, kazafi bayan kazafi. Ban yi tsammanin akwai wani shugaba a Arewa da ba a zaginsa ba, na siyasa ne ko na sarauta ko na addini ko na kasuwanci ko na ilimi kai ko ma na mene ne! Kuma wani lokacin ma shiga kafafen watsa labarai ko na sada zumunta ake yi ana irin wadannan miyagun abubuwa babu kunya babu tsoron Allah. Wace irin al’umma ce wannan? Yaya makomar irin wannan al’umma za ta kasance alhali kuma tana kewaye da makiya daga kowace kusurwa? Lokaci ya yi da za mu koma cikin hayyacinmu, ko kuma ’ya’ya da jikokinmu su ci gaba da yi mana Allah Ya isa da tofin Allah tsine!