Ina makomar malamai a siyasar zamani?
Matukar za mu gaya wa kanmu gaskiya, mu ajiye son zuciya da bambancin ra’ayin bangarancin da yake ta wahalar da mu a cikin addini, to babu dalilin da zai sa malamanmu su je su bude kanti a tsakiyar kasuwar bukatar dagulalliyar siyasar wannan lokaci kuma su yi zaton a nan ma za mu bi su […]
Matukar za mu gaya wa kanmu gaskiya, mu ajiye son zuciya da bambancin ra’ayin bangarancin da yake ta wahalar da mu a cikin addini, to babu dalilin da zai sa malamanmu su je su bude kanti a tsakiyar kasuwar bukatar dagulalliyar siyasar wannan lokaci kuma su yi zaton a nan ma za mu bi su kwatankwacin irin biyayyar da muke musu a zaurukan ilimi, majalisu da kan mumbaran karatuttukan ‘kalallahu kala rasulu.’
A nawa dan karamin sani da fahimtar, ba na jin akwai alfanu da dacewar malaman addinin Musulunci su dauki bangare ta fuskar siyasa, da har za ta kai su ga ajiye gafaka su dauki fosta su kama talla ba. Su kuma sauko daga kan mumbari su dare kan durom suna tallar dan takarar neman kujerar mulkin dimokuradiyyar da har yanzu ba ta da cikakken mazauni a addini. Kwadayin duniya, son a sani da zalamar zuci ne kawai zai sa kin fadin gaskiya, ya koma goyon bayan karya da tunanin kuma samun hanyar zullewa.
Idan akwai wadanda ya kamata su yi aiki da gaskiyar da suka fi kowa saninta, to, malamai ne. Kuma su ya kamata rayuwarsu ta zama abin koyi ga al’ummar da suka tsinci kansu a cikinta, a matsayinsu na jakadun Ubangiji.
Tsakar gidan siyasar wannan zamani, cike yake da dagwalo da kazantar da ta fi kashi wari da doyi, sakamakon irin bakin tsarin da aka gina ta akai na rashin gaskiya, munafunci, karya, yaudara, cin amana da kuma rashin cika alkawari. Wadannan abubuwa ba baki ko boyayyu ba ne, da za mu gaza fahimtarsu a tattare da ’yan siyasarmu a wannan zamani.
Mutanen da kullum suke haska mana tsarin shugabanci nagari a kan tsarin tafarkin addini su ne dai malamai, tunda su Allah Ya sanar abin da ya gabata na magabata kan yadda suka tafiyar da jagorancin al’umma. Tunda haka ne kuwa, ashe sun fi mu sanin daidai da rashin daidai din salon kamun ludayin shugabannin nan da muke da su a wannan zamani.
Idan har karya da zamba da sata da yaudara da rashin cika alkawari mugayen dabi’u ne ga wanda ya siffantu da su, to, kuwa kashi 95 cikin 100 na ’yan siyasarmu a wannan zamani sun siffantu da wadannan miyagun halaye da dabi’un. Domin a yi alkawari na karya, a yi karya don a ci zabe, a bata wani don a gyara kai, a yi zamba cikin aminci, a saci dukiyar al’umma don a kece raini kusan su ne ababen da kasuwarsu ke ci a shiga siyasar kasar nan. In kuwa haka ne ashe ba abin da zai su in goya musu bayan ‘Sai Kayi’ ya kamata a fadi gaskiyar da Allah Ya sanar da ku, ya kamata ku matsa da fada musu ba tare da shakku, tsoro ko fargabar rasa wani abin da Allah ke da hurumin bayarwa da hanawa ba.
Shugabanci ko jagoranci, nauyi ne da ke tattare da kalubalen da nagartattun bayi ke guje masa a zamainn baya don guje wa alhakin da sauke shi zai je ya zame musu jangwam a inda babu mai kama musu. Amma tsarin a yanzu ya canja, ya koma ido rufe ma ake neman shugabancin, ta amfani da hanyoyin zahiri da na badini a kokarin da ake na kaiwa ga madafun ikon tafiyar da rayuwar al’umma ta duk yadda ake so. A irin wannan hali da yanayin da aka kazantar da hanyoyin da ake bi wajen neman mulki, ta hanyar cin mutunci, kazafi, karya, bankado al’aura da basaja da ake yi wa juna ne, malamin addini zai yi tsalle ya fada cikin wannan dambarwa da hauma-haumar, ba don cika umarnin ‘al’amru bil ma’aruf’ ba, sai dai don daukar bangare da goya wa mutumin da yake da hakki a kanka isar masa da sakon Allah.
Muddin kuwa aka gaza yin wannan, aka je ana kokarin gyara miya aka dauki bangaren sai wane, to, kuwa a shirya wa karbar kowane irin sakamakon jifa da masu hamayya da shi za su wurgo yayin da aka makale a karkashin rumfar siyasar.
Don a tsira da mutunci, maganin kada a yi kada a fara. Tun ba yau ba, na dade ina ta tunani yadda za ta kare kan shiga da tsunduma kafar malamai cikin siyasar ‘wane ne namu’ ko ‘mu muna tare da wane’ din nan ba zai haifar mana da alheri ba. Saboda muddin son zuciya ya shiga cikin lamari irin wannan, to, a karshe ILIMI ne zai tozarta, wanda hakan kuma zai bude wata kofar da za ta sada al’umma ga bakar makoma.
Ilimi, musamman na addini a sama yake da mulki da sarauta da dukiya da duk wani matakin rayuwa da dan Adam zai taka. Amma idan ka san ya kamata ne za ka tattala shi har ya yi maka amfanin da zai daga darajarka, ka zama mai kimar da za ka kauce wa wautar wawaye. Amma idan ka kasa fahimtar haka, to la shakka wata rana za ka dora hannu a ka, ka rusa ihun takaicin da muka kasa gane shi ne ke bibiyar malamanmu a dan lokacin nan.
Daga Ahmad A. Umar, Kano. 08060381355