Ina matasa?
Hakika Allah Ya kawo mu wani zamani da abubuwa da dama ga mai tunani ba sai an zaunar da shi an ce ya yi ko ya bari ba. Ilimi ya yawaita kusan ya karade kowane sako sai dai idan mutum bai so ya kwasa ba. Idan za mu tsaya tsai mu yi tunani, babu wani […]
Hakika Allah Ya kawo mu wani zamani da abubuwa da dama ga mai tunani ba sai an zaunar da shi an ce ya yi ko ya bari ba. Ilimi ya yawaita kusan ya karade kowane sako sai dai idan mutum bai so ya kwasa ba.
Idan za mu tsaya tsai mu yi tunani, babu wani abu da muke jira nan gaba da sai an gaya mana wanda za mu yi mu gina ingantacciyar rayuwa. Domin duk wani nau’i na wa’azantarwa, tunatarwa, tsoratarwa kusan babu wanda ba mu ji ko mun karanta, ko kuma mu ganshi kuru-kuru a zahiri ba. Kama daga wanda aka ba mu labari a cikin Alkur’ani Mai girma ko hadisan Manzon Allah (SAW), zuwa wanda aka ba mu labari ya faru a wasu kasashe, har zuwa kan wadanda muka gani da idanunmu a zahiri. Musamman daga lokacin da muka fara mallakar tunani har zuwa yau.
Kada mu tsaya wadansu su rika wasa da kwakwalwarmu, bayan a koyaushe muna ikirarin mu wayayyu ne. Cikakken wayayye shi ne wanda zai iya tsayawa ya kiyaye lokacinsa wajen amfanar da rayuwarsa, ya zauna da kowa lafiya, ya bada himma wajen neman guzurin da zai amfani lahirarsa.
Kada mu rika bata lokacinmu wajen inganta rayuwar wadanda ba mu ne a gabansu ba, muke inganta rayuwar ’ya’yansu mu kuma muna dakushe hasken rayuwarmu.
Mu yi kokarin kawar da duk wani tunani na bambancin ra’ayi mu rika hangen gobenmu, mu rika kyautata wa juna zato na alheri. Mu cire kyashi ko hassada da suka makale a zukutan daukacinmu. Idan har kana tunanin wane yana yi maka hassada to ka rabu da shi, ka sanya abin da zai amfanar da rayuwarka a gaba. Kullum kana dada cirawa sama kana kara ba shi rata, shi kuwa yana bata wa kansa lokaci, domin bai isa ya hana Allah ikonSa a kanka ba. Matsayin da Allah Ya so Ya gan ka dole sai ka kai wajen, domin an riga an tsara maka duk abin da za ka zama tun kafin ka fito duniya har ku hadu da wanda kake tunanin yana yi maka hassadar.
Mu daure wa zuciyarmu mu fitar da kwadayi, mu daure mu fitar da tunanin cewa dole sai na kare muradun wane na bata wane zan yi arziki.
Mu dage da rokon Allah da neman agajinSa domin Shi ne Mai dukkan iko da komai ke gare Shi (S.W.T).
Mu tashi mu nemi sana’a mu nemi na kanmu sai rayuwarmu ta yi haske har na baya gare mu su kwaikwayi kyawawan halayenmu.
Babu wanda zai gyara mana halayenmu, har sai mun sanya a ranmu da gaske gyaran muke so. Allah Ya yi mana jagora.
Dan uwankuKabiru Maigari Gumel
(0802848009)
Gmail:- [email protected]