Ina nan a raye ban mutu ba – danwanzam
Shahararren dan wasan Hausa kuma daya daga cikin wadanda da suka assasa wasan kwaikwayon barkwanci a Arewacin Najeriya da ke zaune a Sakkwato, Alhaji Abudurrahaman Muhammad danmalam, wanda aka fi sani da danwanzam ya shaida wa Aminiya cewa yana nan da ransa bai mutu ba, kamar yadda aka rika watsawa a gari cewar ya rasu. […]
Shahararren dan wasan Hausa kuma daya daga cikin wadanda da suka assasa wasan kwaikwayon barkwanci a Arewacin Najeriya da ke zaune a Sakkwato, Alhaji Abudurrahaman Muhammad danmalam, wanda aka fi sani da danwanzam ya shaida wa Aminiya cewa yana nan da ransa bai mutu ba, kamar yadda aka rika watsawa a gari cewar ya rasu.
Ya yi wadannan kalamai ne a gidansa da ke unguwar Nakasari a cikin garin Sakkwato a zantawarsa da wakilinmu a makon da ya gabata kan labarin da ake bazawa a garin cewar ya kwanta dama.
“Lalle na yi jinya sosai a kwanakin da suka gabata amma yanzu Allah Ya kawo min sauki, garau nake jin kaina. Ina sanar da al’umma cewar ina raye ban mutu ba kamar yadda ake fada a gari, ciwo ba mutawa ba ne;” a cewar danwanzam.
Da ya juya kan rayuwarsa, ya ce ya gode wa Allah da halin da yake ciki na rayuwar godiya, duk da ba wani abun kirki a hannunsa, domin gwamnatin jiha, musamman Hukumar Kula da Al’adu ta Jihar Sakkwato sun watsar da shi kwata-kwata; inda ba su ma san yadda rayuwarsa da ta iyalinsa suke ba, duk da gudunmuwar da ya ba jihar wajen bunkasa al’adu da tattalin arzikin jihar. Yau shi ne a walakance, ba wani tallafi ko tunawa da gwamnati ke yi masa. “Ni ba na zuwa kofar gidan kowa don neman wani abun sanya wa bakina, mu ne, ku ne, kun sani, na sani Allah yana nan kuma na tabbata bai manta da ni ba.” Injin shi, cikin rawar murya.
Ya kara da cewa: “Kana son ka san shekaruna a wannan duniya? Zan yi maka daushe waton dausantaka. Matata na aure ta ne tun tana budurwa, a lokacin na fi shekara 40, yanzu kuma ina tare da ita sama da shekara 40, kila zan kai 90 ke nan ko? Ina godiya ga ’yan wasan kwaikwayo, musamman wadanda ke kawo min ziyarar bangirma saboda sun kasa mantawa da mafari. Abokan wasana da suka yi saura a raye, muna tare da su cikin zumunci da godiyar Allah.”
Wani mai kishinsa ya bayyana wa Aminiya cewa, “Yanayin gidansa da lafiyar jikinsa da iyalinsa, akwai bukatar gwamnatin Jihar Sakkwato ta taimaka masa in aka yi la’akari da gudunmuwar da ya bayar wajen bunkasa al’ada da kafofin yada labarai na Jihar Sakkwato da Arewa da ma Najeriya gaba daya.”