Ina nan a raye, ban mutu ba – Shugaban INEC
Ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman, ya fitar.
Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya rasu a wani asibiti da ke Landan.
Ya bayyana haka ne a ranar Asabar cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mista Rotimi Oyekanmi, ya fitar.
- Zamana a gidan yari jarabawa ce daga Allah – Farouk Lawan
- Tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu da suka tayar da ƙura
A baya, an samu rahotanni a kafafen sada zumunta wanda suka nuna cewa Farfesa Yakubu ya rasu bayan jinya a wani asibiti da ke Landan.
Sanarwar ta bayyana cewa labarin ba gaskiya ba ne.
“Mun samu labarin wata jita-jitar ƙarya da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya rasu a wani asibiti da ke Landan.
“An fara yaɗa wannan jita-jitar tun a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba, 2024.
“Muna kiran jama’a da su yi watsi da wannan jita-jitar.
“Farfesa Yakubu yana nan cikin ƙoshin lafiya, kuma bai je Landan cikin shekaru biyu da suka wuce ba,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Yakubu ya halarci wasu taruka da suka shafi INEC, ciki har da ganawa da Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Zaɓe a ranar Laraba.
Sanarwar ta ƙara da cewar ya halarci wani taro da Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi a ranar Alhamis, 12 ga watan Disamba, 2024.
Sanarwar ta ce an taɓa yaɗa irin wannan ƙaryar a baya, inda aka ce shugaban hukumar ya rasu.
“Yanzu kuma, bayan shekaru uku, sun sake yaɗa irin wannan ƙaryar da suka yi a baya,” in ji sanarwar.
Hukumar ta buƙaci jama’a su fahimci illar da irin waɗannan jita-jitar ke haifarwa ga mutum da al’umma baki ɗaya.
Ta kuma jaddada ƙudirinta na ci gaba da aiki tare da kafafen yaɗa labarai na gaskiya domin yaƙi da labaran ƙarya.