Ina nan ban mutu ba – Ali Nuhu

A ranar Juma’ar makon jiya ne aka baza jita-jitar cewa fitaccen jarumin fina-finan Hausa Ali Nuhu ya mutu, bayan wadansu ‘yan bindiga sun harbe shi.Jarumin ya karyata jita-jitar, inda ya ce yana nan da ransa cikin koshin lafiya.A lokacin da ake yada jita-jitar ma yana tare da Wakilinmu a Gwarinpa da ke Abuja lokacin daukar […]

Ina nan ban mutu ba – Ali Nuhu

A ranar Juma’ar makon jiya ne aka baza jita-jitar cewa fitaccen jarumin fina-finan Hausa Ali Nuhu ya mutu, bayan wadansu ‘yan bindiga sun harbe shi.
Jarumin ya karyata jita-jitar, inda ya ce yana nan da ransa cikin koshin lafiya.
A lokacin da ake yada jita-jitar ma yana tare da Wakilinmu a Gwarinpa da ke Abuja lokacin daukar fim din Kamfanin Saira Mobies mai suna ‘Ya Daga Allah’.
Ana cikin daukar fim din ne sai aka fara kiransa a waya don a tabbatar da zargin da ake yi, inda ya rika karyatawa. Daga karshe ya shiga shafin Twitter da Facebook ya karyata jita-jitar mutuwar, a lokaci guda ya sanya wakar da mawaki Sa’eed Nagudu ya yi masa mai taken ‘Ban Mutu Ba.’
“Wannan jita-jita ce kawai, kai kanka Bashir ka tabbatar da hakan tun da jiya da yau muna tare da kai. ” Inji Ali Nuhu.
A karshe ya gargadi mutane su guji yada jita-jita.
A washegarin ranar Asabar din makon jiya ya cika shekara 40 a duniya, ya kuma cika shekara 15 a masana’antar fina-finan Hausa. Hakan ta sanya a ranar ya shiga shafin twitter da facebook, inda ya rubuta ya kara shekara guda.  
An kammala daukar fim din a ranar Talatar da ta gabata, kuma jarumin ya koma gida.
Aminiya ta gudanar da bincike inda ta gano salsalar faruwar jita-jitar. Ta samo asali ne daga wani sako da wadansu mutane suka kirkira a kan jarumin barkwanci John Okafor, sun yi rubutun ne da Turanci, a sakon sun bayyana an kashe jarumin ta hanyar amfani da bindiga, inda a karshen suka bayyana hakan ya faru a wani fim ne, ba wai da gaske ba.
Bayan hakan ne sai wadansu suka kwaikwaiyi rubutun amma sai suka sanya sunan Ali Nuhu, inda al’amarin ya watsu cikin kankanen lokaci, sannan aka rika dauka da gaske ne ba wai basaja aka yi ba.