Ina nan da raina- Matashin da yasha kwata don murnar zaben Buhari

Matashi mai suna Aliyu Mohammed Sani, wanda ake ta yada rahoton cewa, ya rasu bayan ya yi wanka da shan ruwan kwata a Bauchi da nufin murnar taya shugaba Buhari lashe zaben takarar shugaban Najeriya da aka yi ranar 23 ga Fabrairu 2019, ya ce yana cikin koshin lafiya da ransa. Aliyu, ya bayyana hakan […]

Ina nan da raina- Matashin da yasha kwata don murnar zaben Buhari

Matashi mai suna Aliyu Mohammed Sani, wanda ake ta yada rahoton cewa, ya rasu bayan ya yi wanka da shan ruwan kwata a Bauchi da nufin murnar taya shugaba Buhari lashe zaben takarar shugaban Najeriya da aka yi ranar 23 ga Fabrairu 2019, ya ce yana cikin koshin lafiya da ransa.

Aliyu, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar da ya yi da wakilinmu ta wayar sadarwa a yau Laraba. Ya musanta rahoton da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta cewa, bayan yasha ruwan kwata don taya Buhari murnar lashe zabe ya mutu.

Aliyu, ya kara da cewa wasu rahotannin na bayyana cewa, ya rasu ne bayan an kai shi asibiti duk wannan ba gaskiya bane.

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno