Ina nan da raina – Shekau

Shugaban kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati wal Jihad da ake kira Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da wani sabon bidiyo inda ya ce yana nan da rai.Gidan rediyon BBC Landan ya  fadi a shekaranjiya Laraba ya samu sautin sakon inda Shekau ya ce kungiyarsa ce ke da alhakin kashe mutane a garuruwan Benisheik […]

Ina nan da raina – Shekau

 Abubakar Shekau Shugaban Boko HaramShugaban kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati wal Jihad da ake kira Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da wani sabon bidiyo inda ya ce yana nan da rai.
Gidan rediyon BBC Landan ya  fadi a shekaranjiya Laraba ya samu sautin sakon inda Shekau ya ce kungiyarsa ce ke da alhakin kashe mutane a garuruwan Benisheik da Monguno a Jihar Borno.
Kuma a cewarsa, mutane kusan 200 ne suka mutu a harin sabanin mutane 160 da jami’an gwamnati suka ce sun halaka sakamakon harin.
Abubakar Shekau a cikin sakon wanda mabiyansa ke kabbara, ya ce babu gudu babu ja da baya a kokarinsu na tabbatar da addinin Musulunci tare da yaki da mulkin dimokuradiyya.
A watan Agusta ne, Rundunar Hadin Gwiwa don tabbatar da tsaro a Jihar Borno (JTF) ta fitar da wata sanarwa ga manema labarai dauke da sa hannun Laftanar Kanar Sagir Musa cewa, akwai yiwuwar raunin harbin bindiga ya yi ajalin Shekau.
JTF ta ce an raunata Shekau ne a wani artabun da aka yi tsakanin jami’an tsaro da ’yan kungiyar ta Boko Haram a dajin Sambisa a ranar 30 ga watan Yuli.
Sanarwar ta ce an shigar da Shekau wani kauye mai suna Amitchide da ke kasar Kamaru domin a yi jinyarsa, amma ya mutu tsakanin ranar 25 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Agusta.
Sai dai masana harkokin tsaro sun yi ta nuna shakku kan hakan inda Dokta Bawa Wase, wani mai bincike kan tsaro ya shaida wa BBC a lokacin cewa, “Sai jami’an tsaron Najeriya sun nuna kabarin da aka binne Shekau, da kuma gwajin kwayoyin hallita na DNA kan gawarsa kafin mutane su yarda da maganarsu.”