Ina nan daram a Jam’iyyar NNPP —Shekarau

Shekarau ya ce baya ga Atiku, Peter Obi ya neme shi ne don ya zama mataimakinsa, Tinubu kuma ya nemi ya koma APC don ya taka rawa a zaben 2023

Ina nan daram a Jam’iyyar NNPP —Shekarau

Sanata Malam Ibrahim Shekarau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce ba ya da niyyar komawa Jam’iyyar PDP.

Ya tabbatar da cewa wasu jiga-jigan ’yan siyasa daga jam’iyyun daban-daban suna tuntubar sa domin ganin ya koma jam’iyyunsu, ko da yake ba ya da niyyar yin haka.

Ya ce cikin wadanda suka tuntube shi har da Atiku Abubakar, da dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar LP, Peter Obi da dan takarar mataimakin shugaban kasa a Jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima.

Sanata Shekarau ya ce Peter Obi ya neme shi ne don ya zama mataimakinsa, yayin da Tinubu ya nemi ya koma APC don ya taka rawa a zaben 2023.

Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana haka ne ta bakin Kakakinsa, Malam Sule Ya’u Sule, a tattaunawarsa da BBC Hausa ranar Talata.

A cewarsa, babu kamshin gaskiya a rahotannin da wasu kafafen labarai suka bayar cewa dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi tayin ba shi manyan mumamai idan ya koma  jam’iyyar.

Sule Ya’u Sule ya ce Malam Shekarau, wanda yanzu haka shi ne Sanatan Kano ta Tsakiya yana nan daram a Jam’iyyar NNPP.

Amma ya ce hasashen da ake yi na komawarsa PDP na da nasaba da yadda bangaren tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya gaza cika alkawuran da suka yi a yarjejeniyar da suka kulla lokacin da zai shiga Jam’iyyar NNPP.

Sule Ya’u ya ce idan ban da Sanata Shekarau babu wani daga cikin mutanensa da bangaren Kwankwaso ya bai wa wani mukami ko kujera a yarjejeniyar shigarsa jam’iyyar tasu.

A cewarsa, kawo yanzu bai yanke shawara kan ko zai koma wata jam’iyya ba, yana mai cewa sai wani kwamitin mutum 30 ya zauna ya yi nazari kafin ya yanke hukunci kan mataki na gaba.

Yadda Shekarau ya bar APC

A ranar 29 ga Yuni ne Sanata Shekarau ya sanar da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ficewarsa daga Jam’iyyar APC zuwa NNPP a hukumance.

Sai dai tun 18 ga Mayu, tsohon gwamnan ya fita daga APC zuwa NNPP yana mai cewa ya yi haka ne don ceto jiharsa daga mawuyacin halin da take ciki.

Kafin fitarsa daga APC, Juma’a, 19 ga Agusta, 2022 Shekarau ya rika zaman doya da manja a tsakaninsa da Gwamna Abdullahi Ganduje, sakamakon zargin da ya yi cewa Gwamnan bai iya gudanar da mulki ba.

Ni da Shekarau muna nan tare —Kwankwaso

A martanin dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce babu wata matsala a tsakaninsa da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau.

A tattaunawarsa da BBC Hausa, Sanata Kwankwaso ya ce rahotannin da ake watsawa game da rashin jituwa a tsakaninsa da bangaren Shekarau ba su da kanshin gaskiya.

Sanata Kwankwaso ya ce ko da yake shi ma ya samu wannan labari amma ba haka batun yake ba.

“Gaskiya babu wata yarjejeniya da aka yi da ta wuce cewa akwai bukatu da aka kawo kuma mun yi kokarin biyan su, amma ba a kawo su a kan lokaci ba, kuma babu yadda za mu iya yi musamman abin da ya shafi takara,” inji Sanata Kwankwaso.

Ya ce, galibin wadanda bangaren Shekarau ya kawo domin su samu gurbin takara sun shiga NNPP a kurarren lokacin da INEC ba za ta amince da takararsu ba, domin an kammala zabubbukan fitar da gwani.

Sai dai ya ce idan aka kafa gwamnati za su samu mukamai masu daraja.

Sanata Kwankwaso ya kara da cewa hakan ba zai haifar da wata matsala a Jam’iyyar NNPP ba, yana mai cewa babu matsala a tsakaninsa da Sanata Shekarau.