Ina nan daram ba zan fice daga PDP ba – Shugabar Mata

Hajiya Asabe Isa Tirwun ita ce Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP reshen Jihar Bauchi a tattaunawarsu da wakilinmu ta yi fashin baki game da halin da matan PDP suke ciki a jihar, inda ta ce ba za ta fice daga PDP ba duk da shan kaye da jam’iyyar ta yi:  Aminiya: Hajiya me za k […]

Ina nan daram ba zan fice daga PDP ba – Shugabar Mata
Ina nan daram ba zan fice daga PDP ba – Shugabar Mata

Hajiya Asabe Isa Tirwun ita ce Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP reshen Jihar Bauchi a tattaunawarsu da wakilinmu ta yi fashin baki game da halin da matan PDP suke ciki a jihar, inda ta ce ba za ta fice daga PDP ba duk da shan kaye da jam’iyyar ta yi:

 Aminiya: Hajiya me za k ice game da zabubbukan da suka gabata, ganin jam’iyyarku ta fadi a zabe tare da rasa mukamai da dama?

 

Asabe Tirwun: Mun yi mutukar godiya ga Allah Madaukacin Sarki bisa yadda aka gudanar zabubbukan lami lafiya, dama zabe dole akwai wanda zai yi nasara akwai wanda zai fadi. Kuma wannan zabe da aka gudanar ya nuna cewa tabbas dimokuradiyyar Najeriya za ta dore fiye da tunanin wasu mutane. Bayan haka mun yarda da Allah PDP ta fadi, APC ta lashe zabe kowa ya san cewa Shugaba Jonathan ne ya fara amincewa da sakamakon zaben, inda ya taya Janar Muhammadu Buhari murnar kuma ya yarda da kaddara ya mika wuya. Babban abin da muke bukata a halin yanzu shi ne zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma dorewar mulkin dimokuradiyya. PDP ta yi bakin kokarinta a Najeriya sai dai kuma duk lokacin da mutum ya jima yana waje daya a kan bukaci canji domin kowa ya san cewa ana damawa da shi wajen tafiyar da harkokin gwamnati.

Aminiya: A matsayinki ta shugabar mata ta Jam’iyyar PDP wace gudunmawa kuka ba matan Jihar Bauchi? 

Asabe Tirwun: Hausawa sun ce yabon kai jahilci ne amma tunda muke a Jihar Bauchi ba a taba samun lokacin da matan birni da karkara suka amfana da mulkin dimokuradiyya kamar lokacin Gwamna Isa Yuguda ba, domin mata da dama sun samu ci gaba. Da yawa daga cikinsu sun mallaki motoci da gidaje da mukamai wadanda ake ba su makudan kudi a duk karshen wata, wasu sun yi aure sun sama wa mazansu aikin yi a gwamnati. Saboda haka matan jihar sun fita zakka a wannan shiyya na Arewa maso Gabas. Kuma matan Jihar Bauchi za su ci gaba da tunawa da PDP a zuciyarsu, muna fata za su ci gaba da zama a PDP daram ba gudu ba ja da baya. Marayu da marasa galihu suna daga cikin na gaba-gaba da suka amfana da gwamnatin PDP, mata da kananan yara suna karbar magani a asibitoci kyauta. Muna da kananan hukumomi 20 a jihar kuma dukkan kananan hukumomin sun samu ci gaba bakin gwargwado. An dauki sababbin ma’aikata a bangaren kiwon lafiya masu yawa, bayan haka Gwamna Yuguda ya sake daukar ma’aikatan gwamnati sama da mutum dubu 10.

Aminiya: Mutum nawa kike ganin sun sauya sheka daga PDP zuwa APC a Jihar Bauchi?

Asabe Tirwun: Maganar gaskiya babu wani dan jam’iyya da muka samu labarin cewa ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC a Jihar Bauchi, saboda haka muna fata a ci gaba da yin hakuri. Akwai dai mutane da dama da a cikin PDP suka koyi siyasa amma saboda wasu dalilai suka koma APC.

Aminiya: Da gaske ne za ki sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC nan da makonni kadan kamar yadda ake yadawa?

Asabe Tirwun: Wannan labari ba gaskiya ba ne, a matsayina na shugabar mata ta PDP babu abin da na sani, sai PDP kuma zan ci gaba da zama a PDP har zuwa shekara ta 2019 lokacin da za a sake fafatawa tsakanin APC da PDP. Zababben Gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed Abubakar ya san Asabe sosai kuma yana da tabbacin cewa ba za ta shiga APC ba.

Aminiya: Mene ne sakonki game da yadda aka gudanar da zabubbukan?

Asabe Tirwun: Babban sakona shi ne muna fatar alheri ga sababbin shugabannin da aka zaba tun daga kan gwamnoni da sanatoci da ’yan majalisar wakilai da ’yan majalisar dokokin na jihohi. Kowa ya tsaya ya yi aikinsa tsakaninsa da Allah domin a shekara ta 2019 za a sake zuwa neman alfarma a wurin talakawa.

Aminiya: Me kike so Barista Abubakar ya yi wa matan Jihar Bauchi?

Asabe Tirwun: Abin da nake fata sabon Gwamna ya fara yi wa matan Jihar Bauchi shi ne ya dora daga inda Gwamna Yuguda ya tsaya, kuma wajibi ne sabon Gwamnan ya yi watsi da ’yan ba-ni-na-iya.

Aminiya: Mene ne sakonki ga shugaban PDP na kasa?

Asabe Tirwun: Babban sakona ga shugaban PDP na kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu shi ne ya ci gaba da zama da mambobin jam’iyyar domin karfafa musu gwiwa ta yadda kowa zai ci gaba da zama a gidansu da aka gina da shi.

 

Hajiya Asabe Isa Tirwun ita ce Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP reshen Jihar Bauchi a tattaunawarsu da wakilinmu ta yi fashin baki game da halin da matan PDP suke ciki a jihar, inda ta ce ba za ta fice daga PDP ba duk da shan kaye da jam’iyyar ta yi: 
Daga Hamza Aliyu, Bauchi
Aminiya: Hajiya me za k ice game da zabubbukan da suka gabata, ganin jam’iyyarku ta fadi a zabe tare da rasa mukamai da dama?Asabe Tirwun: Mun yi mutukar godiya ga Allah Madaukacin Sarki bisa yadda aka gudanar zabubbukan lami lafiya, dama zabe dole akwai wanda zai yi nasara akwai wanda zai fadi. Kuma wannan zabe da aka gudanar ya nuna cewa tabbas dimokuradiyyar Najeriya za ta dore fiye da tunanin wasu mutane. Bayan haka mun yarda da Allah PDP ta fadi, APC ta lashe zabe kowa ya san cewa Shugaba Jonathan ne ya fara amincewa da sakamakon zaben, inda ya taya Janar Muhammadu Buhari murnar kuma ya yarda da kaddara ya mika wuya. Babban abin da muke bukata a halin yanzu shi ne zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma dorewar mulkin dimokuradiyya. PDP ta yi bakin kokarinta a Najeriya sai dai kuma duk lokacin da mutum ya jima yana waje daya a kan bukaci canji domin kowa ya san cewa ana damawa da shi wajen tafiyar da harkokin gwamnati.Aminiya: A matsayinki ta shugabar mata ta Jam’iyyar PDP wace gudunmawa kuka ba matan Jihar Bauchi? Asabe Tirwun: Hausawa sun ce yabon kai jahilci ne amma tunda muke a Jihar Bauchi ba a taba samun lokacin da matan birni da karkara suka amfana da mulkin dimokuradiyya kamar lokacin Gwamna Isa Yuguda ba, domin mata da dama sun samu ci gaba. Da yawa daga cikinsu sun mallaki motoci da gidaje da mukamai wadanda ake ba su makudan kudi a duk karshen wata, wasu sun yi aure sun sama wa mazansu aikin yi a gwamnati. Saboda haka matan jihar sun fita zakka a wannan shiyya na Arewa maso Gabas. Kuma matan Jihar Bauchi za su ci gaba da tunawa da PDP a zuciyarsu, muna fata za su ci gaba da zama a PDP daram ba gudu ba ja da baya. Marayu da marasa galihu suna daga cikin na gaba-gaba da suka amfana da gwamnatin PDP, mata da kananan yara suna karbar magani a asibitoci kyauta. Muna da kananan hukumomi 20 a jihar kuma dukkan kananan hukumomin sun samu ci gaba bakin gwargwado. An dauki sababbin ma’aikata a bangaren kiwon lafiya masu yawa, bayan haka Gwamna Yuguda ya sake daukar ma’aikatan gwamnati sama da mutum dubu 10.Aminiya: Mutum nawa kike ganin sun sauya sheka daga PDP zuwa APC a Jihar Bauchi?Asabe Tirwun: Maganar gaskiya babu wani dan jam’iyya da muka samu labarin cewa ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC a Jihar Bauchi, saboda haka muna fata a ci gaba da yin hakuri. Akwai dai mutane da dama da a cikin PDP suka koyi siyasa amma saboda wasu dalilai suka koma APC.Aminiya: Da gaske ne za ki sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC nan da makonni kadan kamar yadda ake yadawa?Asabe Tirwun: Wannan labari ba gaskiya ba ne, a matsayina na shugabar mata ta PDP babu abin da na sani, sai PDP kuma zan ci gaba da zama a PDP har zuwa shekara ta 2019 lokacin da za a sake fafatawa tsakanin APC da PDP. Zababben Gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed Abubakar ya san Asabe sosai kuma yana da tabbacin cewa ba za ta shiga APC ba.Aminiya: Mene ne sakonki game da yadda aka gudanar da zabubbukan?Asabe Tirwun: Babban sakona shi ne muna fatar alheri ga sababbin shugabannin da aka zaba tun daga kan gwamnoni da sanatoci da ’yan majalisar wakilai da ’yan majalisar dokokin na jihohi. Kowa ya tsaya ya yi aikinsa tsakaninsa da Allah domin a shekara ta 2019 za a sake zuwa neman alfarma a wurin talakawa.Aminiya: Me kike so Barista Abubakar ya yi wa matan Jihar Bauchi?Asabe Tirwun: Abin da nake fata sabon Gwamna ya fara yi wa matan Jihar Bauchi shi ne ya dora daga inda Gwamna Yuguda ya tsaya, kuma wajibi ne sabon Gwamnan ya yi watsi da ’yan ba-ni-na-iya.Aminiya: Mene ne sakonki ga shugaban PDP na kasa?Asabe Tirwun: Babban sakona ga shugaban PDP na kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu shi ne ya ci gaba da zama da mambobin jam’iyyar domin karfafa musu gwiwa ta yadda kowa zai ci gaba da zama a gidansu da aka gina da shi.