Ina nan daram- Jega

A wannan makon an yi ta yada jita-jitar cewa Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Farfesa Attahiru Jega ya yi murabus ko kuma an sauke shi har ma an bayyana cewa wani dan uwan gwamnan jihar Ondo ne zai maye gurbinsa, al’amarin da ya sanya mai magana da yawun hukumar zaben  Mista Kayode Idowu ya […]

Ina nan daram- Jega

Farfesa Attahiru JegaA wannan makon an yi ta yada jita-jitar cewa Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Farfesa Attahiru Jega ya yi murabus ko kuma an sauke shi har ma an bayyana cewa wani dan uwan gwamnan jihar Ondo ne zai maye gurbinsa, al’amarin da ya sanya mai magana da yawun hukumar zaben  Mista Kayode Idowu ya fito ya bayyana cewa Farfesa Jega yana nan daram a kan mukaminsa, kuma ba shi da wani kuduri na tafiya hutun wata uku, kamar yadda ake rade-radi cewa fadar shugaban kasa za ta tilasta masa tafiya hutun dole na wata uku daga ranar 1 ga Maris, 2015. Inda ya ce maigidansa yana ta kaiwa da komowa wajen gudanar da zabe mai zuwa. “Jega yana ta fadi tashi wajen shirya zabe mai zuwa, amma sai ga shi kuna cewa wai za a tilasta masa tafiya hutun dole na wata uku. Ta yaya wanda zai shirya zabe sannan ya tafi hutun dole? Babu wani abu makamancin haka.”
Idowu ya bayyana hakan ne a lokacin da wani gidan talabijin da ke Legas yake hira da shi a ranar Talata, inda ya ce ka’idojin da aka bi aka dauki Jega aiki ba daidai suke da na aikin gwamnati ba, saboda zai ci gaba da aiki har zuwa ranar 30 ga watan Yuni lokacin da wa’adinsa zai kare.
Ya kara da cewa, dage zaben da aka yi zai kara ba Hukumar zabe damar yin kyakkyawan shiri don gudanar zabukan da za a yi a ranakun 28 ga Maris da kuma 11 ga Afrilu.
Idowu ya kuma karyata batun cewa Jega ya aje aiki sakamakon matsin lamba daga fadar shugaban kasa.Ya ce, “A’a, babu batun ya aje aiki, wannan batu ba gaskiya ba ne, bai aje aiki ba, jita-jita ce kawai.”
Tun da farko dai a ranar Asabar Farfesa Attahiru Jega ya gana da ’yan jarida a hedikwatar hukumar da ke Abuja,inda ya bayyana dalilan da suka sanya hukumarsu ta dage zabe zuwa watan Maris. Aminiya ta samu damar zantawa da shi inda a nan ma ya tabbatar da cewa ba zai aje aiki ba duk da kiraye-kirayen da ake yi na ya aje aiki. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Ga shi ka bayyana dage zabe, ba ka tunanin dama ’yan Najeriya suna cewa akwai makarkashiya game da hakan, ko kuma tilasta ku aka yi?
Jega: Alhamdulallahi, wannan hukunci ko mataki da muka dauka, mun dauke shi ne ba tare da wani ya tilasta mu ba, ko kuma wani ya samu mu yi wani abu da muke ganin ba daidai ba ne, zancen gaskiya shi ne, a wannan shekarar yadda muka tsara za a yi zabe shi ne, mun tsara za mu yi amfani da masu yi wa kasa hidima da daliban jami’o’i kusan dubu 700, kuma a kodayaushe idan muka shirya zabe abin da yake gabanmu shi ne, yaya za a kula da tsaronsu da lafiyarsu, a kuma takaita irin wahalhalun da za su shiga don a samu zabe mai inganci, kuma kamar yadda kuka sani ne rikici ya taso a lokacin da muka yi zaben 2011, kuma a lokacin akwai kyakkyawan tsaro, amma aka rasa rayukan masu yi wa kasa hidima har 9, akwai tsaro ke nan a lokacin, to yanzu ga shi mun samu shawara mai karfi daga jami’an tsaro, inda suka ce saboda hankalinsu ya karkata wurin yaki da masu tarzoma a jihohin Arewa maso Gabas, suna ganin cewa ba za su iya tabbatar mana da samun  tsaro ba, to gaskiya abin da ya fara zuwa mana shi ne, yaya za mu sa duk wadannan ma’aikatan namu bayan an tabbatar mana ba za a samu ingantaccen tsaro ba, duk da cewa mutane ba za su so a dage zabe ba, amma mu ce dole sai an yi zaben nan, yaya za a yi mu kare ma’aikatanmu, sannan mu dauki matakan tsaro, babu wadansu masu bada tsaro idan ba wadannan jami’an tsaron ba. To wannan ya sa muka dauki wannan matakin.
Aikinmu shirya zabe, amma yadda siyasar Najeriya take ciki, inda ake fadace-fadace da kone-kone da kuma kashe-kashe, dan abu kadan saboda hamayya ta siyasa sai a mayar da shi rikici, da jami’an tsaron ma yaya aka kare, ballantana yanzu an ce ba za a same su ba. A gaskiya an sanya mu a cikin wani hali.
Da mu dauki matakin da za mu jefa mutane cikin tashin hankali, gara mu dage zaben. Mutane da yawa ba za su ji dadin wannan matakin ba, amma komai sai an yi shi cikin hikima, idan har ana so a samu nasara.
Yanzu duk wadanda suka ce mu yi zaben nan da muka tambaye su, to wane mataki suka dauka sai suka yi shiru, babu wata gamsasshiyar amsa. Fatanmu shi ne Allah Ya sa hakan shi ne mafi alheri. Muna rokon jama’a su yi hakuri, domin mahakurci mawadaci.
Aminiya: Me za ka ce game da batun da ake cewa an dage zaben ne don a ba wadansu damar yadda za su murde zaben?
Jega: Ina so in tabbatar wa jama’a cewa dage zaben nan da aka yi bai saba wa kundin tsarin mulki ba. Kundin tsarin mulki ya tanadar cewa ana iya yin zabe saura kwana 30 ga zuwan  ranar da za a rantsar da wanda aka zaba, misali za a iya yin zabe har 29 ga watan Afrilu.
Kun ga ba za a ce jami’an tsaro su bada shawara a kuma ki la’akari da ita ba, saboda mun duba, mun kuma yi tunanin illar da za a samu sakamakon rashin amfani da shawararsu za ta fi mu rufe ido mu yi zaben, domin idan mun yi ba mu san me zai faru ba.
Aminiya: Wane tabbaci za ka ba ’yan Najeriya cewa za a ba kayan zabe kariya, musamman ma ganin cewa yanzu an kara lokaci?
Jega:   Ba shakka mutane suna zargin abubuwa masu yawa, amma wani lokaci ana yin hakan ne cikin fushi ko rashin sani, amma ina tabbatar maka, matakan da muka dauka wajen bada kariya ga takardun zabe, a ganinmu babu yadda wani zai je ya same su har ya yi magudi, mun dauki kwakkwaran matakai, dama idan muka buga takardun nan, aka kuma shigo da su, to tun daga filin jirgin sama za mu tare su, sannan mu kai su wani wurin da za a ba su matakai na tsaro, don haka babu wani haufin cewa za a yi magudi, ko wani zai samu wadannan takardun.
Aminiya: Ka yi magana cewa rashin tsaro a jihohi 4 na Arewa maso Gabas ne suka sanya aka dage zabe, idan rashin tsaron ya ta’azzara yaya za ka yi ke nan?
Jega: Fatan da muke yi shi ne kada abin ya ta’azzara har ya sanya a shiga halin kaka-ni-kayi. Fatanmu shi ne, yadda jami’an tsaro suka ce mu ba su wannan lokacin domin suna ganin cewa  za su ci galaba a yakin da suke yi na  magance ta’addanci, to shi ne a samu zaman lafiya da za mu iya gudanar da zaben. Abin da nake so mutane su sani shi ne, mu hukumar zabe mun yi alkawarin ba za mu taba barin a dage zabe sama da hurumin da kundin tsarin mulki ya tanadar ba. Dole a yi shi kafin 29 ga watan Mayu.
Aminiya: Mene ne dalilin da ya sa aka dage zaben saboda jihohi guda hudu na Arewa maso Gabas?
Jega: Dalilin da ya sa aka dage shi ne, jami’an tsaro sun bayyana mana a halin yanzu sun fara aiki gadan-gadan a wadannan jihohi 4, idan kun tuna da ana zancen jihohi 3 ne, wato Adamawa da Barno da Yobe, amma yanzu yadda suka yi bayani har da Jihar Gombe, sun ce suna cikin yanayi na yaki, sun ce ranar da za a fara zabe to ba su kammala wannan yakin ba, don haka ba za a iya yin zabe ba, sun ce sun tattaro duk jami’ansu da ma’aikatansu, kuma sun dukufa wajen yakin, to zai yi wuya su bada taimakon tsaro kamar yadda suka saba a dukkan jihohi a lokacin zabe. Mun yi tunanin za a iya gudanar da zabe ba tare da wadannan jihohi 4 ba, wato a yi zabe a sauran jihohi. Mun amince cewa za a iya yi, amma za a iya shiga wani hali, dokokin zabe sun ce ba za a ce dan takarar shugaban kasa ya ci zabe ba, na farko sai ya samu kuri’un da suka fi yawa, bayan wannan sai ya samu kashi 25 cikin 100 na adadin kuri’un da aka samu a jihohi kashi 2 cikin 3. Ko a wadannan jihohi hudu, mun raba katin zabe na dindindin kashi 80 cikin 100 a Jihar Gombe, kashi 64.54 cikin 100 a Jihar Yobe, mun raba kashi 70 cikin 100 a Jihar Adamawa, mun kuma raba kashi 60.78 cikin 100 a Jihar Barno. Idan aka yi wannan zaben ba tare da jihohi 4 nan ba, za a iya kasa samun dan takarar da zai ci zabe, idan haka ta faru to sai an jira sun kammala yakin kafin a yi zabe. Da a yi zabe rabi-da-rabi gara a dage zaben.
Aminiya: A yanzu yaya kake ji bayan ka kammala shirye-shiryen zabe kuma sai ga shi an dage shi?
Jega: Tabbas mun shirya, mun dauki dukkan matakan da suka kamata, duk da cewa da wahala shirin zabe ya kammala dari bisa dari, dole a samu matsalolin da ba za a rasa ba, amma mun tabbata za mu iya shirya zabe a 14 ga Fabrairu, 2015, kwatsam wani abu ya taso, babu dadi irin haka, ga shi mun bata wa mutane rai da yawa, duk bayanin da za mu yi wani ba zai gamsar da shi ba, zai dauka ko an saye mu ne, ko an tsorata mu, Allah Ya sani, mun dage ne saboda hakan ne mafi alheri ga kasarmu.
Aminiya: Batun cewa kana halartar zaman kungiyar ACF fa?
Jega: Ban taba halartar wani zama ba, kuma da a ce akwai lokaci sai na je kotu an bi mini hakkina, kuma halarta taron da ya shafi kungiya irin wannan ya saba wa aikina, hakan zai sa in yi murabus.
Aminiya: Wata kungiya ta Kudancin Najeriya ta bukaci ka aje aiki sakamakon dalilan da suka zayyano na cewa ka karkata wajen ba yankin Arewacin kasar nan fifiko, me za ka ce kan hakan?
Jega: Ba zan aje aiki ba, wannan kuma wani ra’ayi ne na wadansu tsirari, sun bukaci hakan ne saboda wani dalili na kashin kansu. Da a ce na aikata wani abu, misali kamar halartar taron kungiyar ACF, to wannan zai sa in ajiye aiki saboda na keta ka’ida. Amma a halin yanzu babu wani abu da zai sa in aje aiki.

….Ban ce zan sauke shi ba   -Jonathan

Balarabe Ladan a Abuja

Shugaban kasa Goodluck Jonathan  ya bayyana cewa bai fada wa kowa cewa zai sauke shugaban hukumar zabe (INEC) Farfesa Attahiru Jega daga mukaminsa ba.
Ya ce wadansu mutane ne kawai suke yada wannan jita-jitar domin  su haifar da rudani,  ‘’ tun daga Farfesa Jega har zuwa manyan jami’an hukumar zabe ni ne na nada su, ina da ikon cire su, amma babu wanda na fada masa cewa zan sauke su, domin na yarda cewa za su iya gudanar da aikin da aka sanya su.’’
Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a yayin da yake hira ta musamman da manema labarai a fadar gwamnati da ke Abuja shekaranjiya Laraba.
Dangane da batun cewa yana tunanin tura Jega zuwa hutun dole na wata uku kuwa, Jonathan ya ce babu kamshin gaskiya a game da labarin.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cbewa lallai babu shakka za a gudanar da zabe a sabon ranar da aka tsayar kuma za a mika mulki a ranar 29 ga watan Myun wannan shekara kamar yadda aka tsara.