Ina nan daram, mutuwa sai lokaci ya yi-Ibro
Fitaccen jarumin barkwancin finafinan Hausa Rabilu Musa (Ibro) ya karyata jita-jita da ake yadawa a gari game da labarin mutuwarsa.Jarumin wanda ya zanta da wakiliyar Aminiya a Kano ya bayyana cewa yana nan daram cikin koshin lafiya, domin ko ciwon kai bai yi ba.“Ina sanar da duniya cewa ina nan daram da raina, na san […]
Fitaccen jarumin barkwancin finafinan Hausa Rabilu Musa (Ibro) ya karyata jita-jita da ake yadawa a gari game da labarin mutuwarsa.
Jarumin wanda ya zanta da wakiliyar Aminiya a Kano ya bayyana cewa yana nan daram cikin koshin lafiya, domin ko ciwon kai bai yi ba.
“Ina sanar da duniya cewa ina nan daram da raina, na san zan mutu amma sai lokaci ya yi. Kodayake ba yau aka fara kirkirar irin wadannan maganganu ba, idan da sabo ma an saba, domin kusan karo na goma sha ke nan makiya ke shirya irin wannan magana tare da yada ta a duniya.” Inji shi.
Har ila yau jarumin ya yaba da irin yadda masoyansa suka rika nuna damuwarsu a lokacin da suka ji wannan jita-jita. “Babu abin da zan ce da masoyana sai godiya, domin na ji dadin yadda suka rika nuna damuwarsu game da jita-jitar da aka rika yadawa a kaina, saboda yadda mutane suka rika kirana a waya wallahi wayata har daukewa ta yi.” Inji Ibro.
A karshe Ibro ya sanar da masoyansa cewa su sa ido da ganin fina-finansa masu kayatarwa. “Ina kira ga masoyana da su ci gaba da yi mana addu’ar alheri sannan ina sanar da su su sa ido da ganin fina-finanmu masu kayatarwa a nan gaba, domin harkokin da muka sa a gaba na fina-finai da kuma siyasa ba fasawa za mu yi ba sai ma abin da ya fi na da.
Idan dai za a iya tunawa a ranar Litinin ne aka baza labarin jita-jitar rasuwar jarumin a shafukan sadarwa na facebook da sauransu.