Ina neman afuwar Musulmai bisa furucin da na yi kan zaben Majalisar Dattawa — Kashim Shettima
Ni dan Adam ne kuma ajizi.
Maitamakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya ce yana neman afuwar al’ummar Musulmi bisa wasu kalamai da ya yi game da zaben shugabannin Majalisar Dokokin Tarayya.
A cewar Mataimakin Shugaban Kasar, ba a fahimci maganar a muhallinta ba, kuma ba shi da wata manufa ta bata sunan addininsa.
- Za mu sasanta rikicin Rasha da Ukraine — Shugabannin Afirka
- NAJERIYA A YAU: Musabbabin takaddamar siyasa a Jihar Filato
Sanata Kashim a tattaunawarsa da BBC ya ce ya yi wadannan kalamai ne saboda maslahar Najeriya, ganin cewa suna da wasu bayanan sirri da bai dace ya fito bainar jama’a yana bayani a kansu ba.
Sannan yadda lamura ke tafiya a Najeriya a wannan lokaci, dole shugabanni su fito su ja hankali domin wanzuwar kasar baki-daya.
Kalaman Shettima a cikin makon jiya sun haifar da zazzafar muhawara musamman a shafukan sada zumunta, inda aka rika sukar Mataimakin Shugaban Kasar.
Sai dai Kashim Shettima ya ce shi Musulmi ne na hakika domin zuri’arsu sun shafe tsawon dubban shekaru a kan tafarkin addinin.
Sannan duk wanda bai ji dadin kalamansa ba, ya yi hakuri a yafe masa, ba shi da niyyar muzanta wa addini.
“Ni dan Adam ne kuma ajizi don haka ina neman afuwar al’umma da Ubagijina.”
Kashim Shettima ya tunasar da cewa shi dan malamai ne kuma jikan malamai, don haka ba shi da niyyar muzantawa wani bangare na addinin kasar.
‘Ban ce duk lalacewar Kirista ya fi Musulmi ba’
A wannan makon ne dai Aminiya ta ruwaito Mataimakin Shugaban Kasar yana nesanta kansa daga kalamai da ya ce ana alakanta shi da su kan shugabancin Majalisar Dattawa.
Aminiya ta rawaito yadda wani faifan bidiyo ya karade gari musamman a kafafen sada zumunta, inda aka nado Shettima a wajen wani taro da Sanatoci ranar Lahadi yana cewa “gwara Kiristan Kudu duk lalacewarsa da Musulmin Arewa duk nagartarsa ya Shugabanci Majalisar Dattawa.”
Kalaman nasa dai sun jawo cece-kuce matuka, musamman a shafukan sada zumunta na zamani tun daga ranar Litinin har kawo yanzu.
Shettima, a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Mataimakin Shugaban Kasa ya fitar da yammacin Litinin din, ya ce an canza masa kalaman nasa gaba daya, kuma an yi masa mummunar fahimta.
Ya ce ba a bayyana kalaman a muhallin da aka yi su ba, kuma an canza musu ma’ana don kawai su dace da manufar masu zagon kasa ga burin al’ummar Najeriya na tabbatar da hadin kan kasa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, a yayin taron da Sanatoci masu gangamin ganin Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibrin sun jagoranci Majalisar Dattawa ta goma, Kashim Shettima ya jaddada tsarin siyasar kasar, inda ya yi nuni da cewa samun Kirista daga Kudancin Najeriya da kuma wani Musulmi daga Arewaci shi ne zai tabbatar da daidaiton adalci don inganta muradin shigar da kowane bangare na addini a dama da shi a Gwamnatin Tarayya.
Sanarwar ta ambato Sanata Shettima yana nunar da cewa, bisa la’akari da cewa Shugaban Najeriya da Mataimakinsa duk Musulmai ne, to bai dace su goyi bayan Musulmi ba ya zama Shugaban Majalisar Dattawa ba, ko da kuwa Musulmin da ya fi cancanta, saboda tabbatar da daidaito a tsakanin addinai.