Ina ribar dimokuradiyya a Najeriya?
Gwamnatoci a Najeriya sun yi bukukuwan tunawa da ranar dimokuradiyyaduk da cewa kasar mu na fuskantar babban kalubale.Baya ga rabuwar kawunan ‘yan kasar ya rabu gida-gida, inda al’ummar kudu maso kudu ke kalamai marasa dadi iri daban –daban, musamman kalaman Cif Edwin Clark da na Asari Dokubu, wadanda suka yi batanci ga wasu dattawan Arewa […]
Gwamnatoci a Najeriya sun yi bukukuwan tunawa da ranar dimokuradiyyaduk da cewa kasar mu na fuskantar babban kalubale.Baya ga rabuwar kawunan ‘yan kasar ya rabu gida-gida, inda al’ummar kudu maso kudu ke kalamai marasa dadi iri daban –daban, musamman kalaman Cif Edwin Clark da na Asari Dokubu, wadanda suka yi batanci ga wasu dattawan Arewa masu kima ciki har da Farfesa Ango Abdullahi. Akwai kuma rikicin Boko Haram da na kungiyar Asirin ko in ce matsafan Ombatse, wadda ta yi wa ‘yan sanda da Jami’an SSS kisan kiyashi. Ga ‘yan fashi da makami da suke addabar wurare, wadanda suka hada da Birnin Gwari da Zamfara, da ‘yan fashi da alkalami da masu garkuwa da jama’a da masu ci da gumin yara da masu safarar mata da dai sauransu.
Idan muka bibiyi ire-iren wadannan manya-manyan kalubale da ke kokarin ruguza mu, za mu fahimci, bai kamata ai biki ba sam, kamata ya yi mu dukufa yin addu’a da daukar kwararan matakai da za su fidda kasarmu daga bisa wannan siradi.
Mu sani kasancewar Najeriya matsayin kasa guda, a zauna cikin zaman lafiya,lumana da mutunta juna, ya fi zama cikin yaki da rarrabuwar kawuna. A daidai wannan lokaci ya kamata daukacin ’yan Najeriya masu tausayin Talakawa su rika auna kalamansu da rubutunsu, don ka da a aikata abin ba zai taimaki kasar ba. Irin wannan salon tafiya da kasar ke tangal-tangal a kai, lallai dole ta sanya masu hankali su bijiro da tambaya, kan ina ribar dimokuradiyya ga al’ummar Najeriya?
Shi dai Talakan Najeriya bai da bisa baida tikitin Jirgi, saboda haka ko kasar ta yamutse, to da shi za ta yamutse, su kuwa azzalumai da ma kudinnsu na can kasashen waje, sai kawai su haye jirgi abinsu su yi tafiyarsu Ingila ko Amerika da sauransu, a rika hira da su a kafafen yada labarai na BBC ko CNN ko Muryar Amurka, suna fadin ga yadda za a shawo kan matsalar. Don haka Talakawa, idan Najeriya ta zauna lafiya to sai mun fi kowa cin riba, idan kuma ta ci gaba da tafiya haka, ko ta kara dagulewa, to sai mun fi kowa shan wuya.
Akwai bukatar kabilu da addinai, musamman matasa da mu guji tada rigima da sunan bambance- bambance, mu hada kanmu, ka da mu bari wasu su zuga mu don rura wutar kiyayya a tsakaninmu. Ya kamata mu tashi mu yaki miyagun dabi’u, wadanda suka ahda da cin hanci da rashawa da magudin zabe da kabilanci da tsattsauran ra’ayi. Domin idan muka yi haka, to za mu ci riba, idan kuwa muka ki, muka gwanmace mu zama ‘yan bangar siyasa, to za a yi ba damu ba. Idan Najeriya ta ruguje, to mu matasa mune za mu fi shan wahala, domin mu ne masu karancin Shekaru.
Shugabanni wadanda aka bai wa amana su rika kyautata wa talakawansu, su mayar da hankali wajen bunkasa ilimi, daukar kwararrun mallamai da gina sababbin makarantu da zuba masu kayan aiki. Sannan a farfado da noma da kiwo, a bai wa mata da matasa jari da koya masu sana’o’i, ba tare da zabi sonka ba. Allah ya taimake mu da kasarmu Najeriya.
Daga Kwamared Bishir Dauda, Sabuwar Unguwa Katsina, Muryar Talaka 08165270879.