Ina samun alheri da sana’ar hayar doki – Isyaka
Haya da doki a Kurmi wani sabon abu ne ga ’ya’yan Hausawa da aka haifa a can, sannan kuma wani lamari ne na karin ilmi gare su, musamman wasu daga cikin haihuwar Kurmi. Wasu ba su taba ganin doki a zahirinsa ba sai dai ko a hoto ko kuma a fim. Da yawa ma cikin […]
Haya da doki a Kurmi wani sabon abu ne ga ’ya’yan Hausawa da aka haifa a can, sannan kuma wani lamari ne na karin ilmi gare su, musamman wasu daga cikin haihuwar Kurmi. Wasu ba su taba ganin doki a zahirinsa ba sai dai ko a hoto ko kuma a fim. Da yawa ma cikin halittun gida da suka hada da rakumi, jaki, kura da biri a halittun daji da ake shigowa gari da su ana yin wasa da su, ba kasafai suke katarin ganin su ba.
A Jihar Kurosriba, musamman garin Kalaba, Isyaka Abdullahi dan asalin Jamhuriyar Nijar mazaunin Uyo Jihar Akwa Ibom ya kawo doki Kalaba, inda ’yan Arewa suke biyan kudi kalilan suna hawan doki, suna daukar hoto; lamarin da ya zame musu tamkar wani wanda yaje wata kasa yawon bude ido haka kuma ,yan arewa da basu taba ganin doki ba a zahiri sai a hoto na tururuwa suna zuwa kallon doki suna biyan kudi ana dora su akai suna daukar hoto.
Aminiya ta tambayi Isyaka ko mai ya ja ra’ayinsa har ya kawo doki Kalaba yana haya da shi? “Abin a yaba ne kuma a yi alfahari da shi, domin ni kaina idan na shiga wani wuri mutane kan gaya min cewa su ba su taba ganin doki ba a fili sai a fim ko hoto amma yanzu ga shi sun gani suna mamaki. Dangane da dokin da na shigo da shi Kalaba, wasu har kudi suna ba ni su hau su dauki hoto. Wani lokaci suna ba ni Naira 300 zuwa 500 su hau.” Ya ci gaba da cewa, kawo doki Kurmi yana wayar da kan mazauna yankin da ba su taba ganinsa ba, musamman ’yan Arewa da aka haifa a Kurmi.
A Kudancin Najeriya, masu sana’ar wasa da kura da biri suna kara wayar da kan yara ’yan Arewa da aka haifa a can, domin wasu sai a fim ko hotuna suke ganin irin wadannan dabbobi. Isyaka ya ce a rana ta Allah matukar ba ruwan sama aka yi ba, yana samun alheri sosai. “Da sana’ar nan haka nake ci nake sha kuma nake kula da lafiyar dokin,” inji shi.
karshe ya ce abin da ya sa ’yan Kudu ba za su iya kiwon doki ba saboda wajen ciyar da su da shayarwa da kula da lafiyar dabba shi ke sanyawa su galabaita har su kai ga mutuwa. “Za ka ga an bar saniya ko akuya ta yini daure kafin a ba ta abinci ko ruwa har sai ta fita hayyacinta. Ka ga kamar doki baya son sanyi, lokacin damina a nan Kurmi sanyi yana yi wa doki illa har ya kai ga mutuwa idan ba a samu wanda zai kula da shi ba sosai.”
Wasu yara da suka hau doki, sun bayyana wa Aminiya cewa ba su taba ganin doki ba sai wannan karo, duk da cewa sun saba gani a fina-finai ko kuma a hoto.