Ina samun alheri da sana’ar Wanzanci – Sarkin Askar Abekuta

Alhaji Auwalu Magaji, shi ne Sarkin Askan Abekuta kuma jagoran ’yan Arewa mazauna Jihar Ogun a ƙarƙashin jam’iyar APC. A zantawarsa da Aminiya, ya shaida irin faɗi-tashin da ya yi a siyasa tare da alfanun da ya samu a sana’ar wanzanci, sana’arsa ta gado:   Yaya ka fara rayuwa a wannan yanki na Najeriya? A […]

Ina samun alheri da sana’ar Wanzanci – Sarkin Askar Abekuta

Alhaji Auwalu Magaji, shi ne Sarkin Askan Abekuta kuma jagoran ’yan Arewa mazauna Jihar Ogun a ƙarƙashin jam’iyar APC. A zantawarsa da Aminiya, ya shaida irin faɗi-tashin da ya yi a siyasa tare da alfanun da ya samu a sana’ar wanzanci, sana’arsa ta gado:

 

Yaya ka fara rayuwa a wannan yanki na Najeriya?

A nan Abeokuta aka haifi mahaifiyarmu. Wanzanci ne sana’armu ta asali, domin ita ce sana’ar gidanmu tun lokacin iyaye da kakaninmu. Mu shida mahaifinmu ya Haifa, maza 5 mace 1 duka a nan Abekuta sannan har gobe dukanmu mazan muna yin sana’ar. Abin da ake buƙata shi ne tsafta, wato abin da ya shafi ka karan kanka da kayan aikinka da yin ƙoƙarin buƙasa sana’ar ta hanyar bin dokokin kare lafiya tare da kyakkyawar mu’amala, wannan shi ne ke sanya kowace irin sana’a ci gaba da samun karɓuwa.

Ko me zaka ce game da karɓuwar sana’ar Wanzanci a yanzu, musamman ma a yankin Kudancin ƙasar nan?

AAi har gobe wannan sana’a ta Wanzanci tana ƙara samun karɓuwa ne domin hanya ce ta tsabtace jiki. Mu a yanzu ma Yarabawa sun fi bai wa aski irin namu na gargajiya muhinmmanci. Da za ka zo wannan rumfa tamu ranar Juma’a ko Asabar ko Lahadi, za ka ga waɗanda suke zuwa askin mafi yawansu Yarabawa ne, sannan wanzamai kaso biyu ne, akawi waɗanda aski kawai suke yi, akwai kuma waɗanda suke ɓangaren jan wanzanci; wato abin da ya shafi yi wa yara kaciya ciri hakin wuya, ƙaho da dai makamantan ayyukan da suka shafi na jinni. Ni duka sassan biyu na haɗa, sannan ina ba da magani irin na sanyi da makamanta haka, kuma tun da nafara sana’ar ba na yin jinga da mutum, duk abin da ya ba ni zan karɓa in ce Allah Ya sanya albarka.

A haka ne sau tari za ka ga na yi wa mutum aski ya ɗauki abin da ban zata ba ya ba ni. Ni ke yi wa Gwamnan Jihar Ogun Sanata Ibikunle aski tun kafin ya zama gwamna kuma har yanzu duk sanda yake buƙatar aski yana kirana in je in yi masa. Shi kuwa yayansa Alhaji Agba har nan yake zuwa rumfarmu in yi masa aski. Baya gare su akwai tarin manyan mutane da dama da nake wa aski sannan kuma har gobe duk wanda ya zo zan yi masa domin ba na wariya a tsakanin talaka ko mai kuɗi.

Ko ya a kayi ka sami kanka a siyaya?

Na fara siyaya tun lokacin da aka kafa jam’iyar SDP da NRC, a wannan lokacin SDP muke yi har Allah Ya kai mu lokacin da aka bai wa Cif MKO Abiyola takarar Shugaban kasa, sai faɗuwa ta zo mana daidai da zama, kasancewarsa ɗan Abekuta kuma gidansa yana nan kusa da mu a Sabo-Abekuta. Bayan da Allah Ya ƙaddara abubuwan da suka faru a wanccan lokacin, ba mu yi ƙasa a gwiwa ba, haka muka ci gaba da gwagwarmaya a siyasa. Tun daga mataki na mazaɓarmu ga shi yanzu Allah cikin ikonSa ana damawa da mu a siyasance, a mataki na jihar. Don haka shawarata ga ’yan Arewa mazauna wannan yanki namu na Kudu, su dinga shiga ana damawa da su a harkar siyasa; sannan in mutum zai yi siyasa to ya fara daga tushenta, wato mazaɓarka. Kada mutum ya ce ta sama yake so ya fara, hakan sai ka ga ya kama gaibu. Wannan ita siyasa abu ce da ke buƙatar juriya da haƙuri da kuma gaskiya da riƙon amana. Duk wanda ya riƙe wannan duk daɗewa zai sami alfanunta, domin ni yanzu alhamdu lillahi, muna ganin amfaninta, a wannan gwamnati ta Gwamna Ibikunle Amusu. Mu ‘yan Arewa mun sami alfanu da dama, duk abin da zai yi yana damawa da mu, yana martaba mu, yana ganin darajarmu da mutumcinmu. A yanzu haka ina ɗaya daga cikin manbobin kwamitin Aiki Hajji na Jihar Ogun sannan akwai da dama daga cikin ‘yan Arewa da suke aiki a matakin ƙananan hukomomi da ma jiha. Sannan muna zaune lafiya da abokan zamanmu Yarabawa da sauran ƙabilu cikin mutunci tare da martaba juna.