Ina samun miliyan 21 duk wata — Sanata Kawu

Ya ce bai san wasu kuɗaɗe da Obasanjo yake magana a kansu ba ya ga waɗanda ya bayyana.

Ina samun miliyan 21 duk wata — Sanata Kawu

Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila daga Kano ta Kudu, ya bayyana cewa yana samun fiye da Naira miliyan 21 a kowane wata a matsayin kuɗaɗen gudanar da harkokin ofishinsa.

A cikin wata hira da ya yi BBC Hausa, ya bayyana cewa albashin da Sanata ke karɓa bai kai Naira miliyan ɗaya, sakamakon cire-cire da ake yi wa albashin.

“Kuɗin da ake karɓa na albashi a wata bai kai naira miliyan ɗaya ba, idan an yi yanke-yanke yakan dawo kamar naira dubu ɗari shida da ɗan wani abu a matsayin albashi,” in ji shi.

Sai dai ya ce idan aka haɗe jimillar kuɗin da yake samu ya haura Naira miliyan 21.

“Saboda ƙari da aka samu, a majalisar dattawa ana ba wa kowane sanata naira miliyan ashirin da ɗaya a kowane wata a matsayin kuɗin gudanar da ofis ɗinsa.

“Ni dai ban san wani kuɗi da aka halarta ake ba ni a matsayin sanata ba,” a cewarsa.

Wannan bayanin na zuwa ne kwana guda bayan da Hukumar Kula da Albashi da Rarraba Kudi (RMAFC), ta ce kowane Sanata yana samun kimanin Naira miliyan 1.06 a kowane a matsayin albashi.

Shugaban RMAFC, Mohammed Shehu, ya yi wannan bayani a matsayin martani kan yadda ake biyan ’yan majalisar maƙudan kuɗaɗe.

Kawu ya bayyana cewa Naira miliyan 21 sun haɗa da kuɗin gudanar da ofis, kuɗin jaridu, tafiye-tafiyen cikin gida, da sauransu.

Ya nuna cewa a zahiri albashin ya kasa kai Naira miliyan ɗaya, amma idan aka yi cire-cire abin da yake ragewa bai wuce Naira 600,000 ba.

Idan ba a manta ba, tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ne, ya caccaki yawan kuɗaɗen da ’yan majalisa ke samu.

Sai dai, Sanata Kawu, ya caccaki Obasanjo, inda ya ce a zamanin mulkinsa ne aka fara ba ’yan majalisa kuɗaɗen da suke wuce hankalin mutane da nufin gyara ga kundin tsarin mulki domin sahalewa Obasanjo yin tazarce, zargin da a baya tsohon shugaban ƙasar ya musanta.