‘Ina samun ribar Naira dubu 20 duk wata wajen sayar da ganyayyaki’

Alhaji Usman Haruna mai kimanin shekara 51 da ke sayar da ganyayyaki a Kasuwar Dare ta karamar Hukumar Gwagwalada, a Abuja. Ya tattauna da wakilanmu, inda ya bayyana yadda yake sayar da ganyayyaki, ribar da yake samu da kuma kalubalen da yake fuskanta a sana’ar. Ga yadda hirar ta kasance: Me ya sa kake sayar […]

‘Ina samun ribar Naira dubu 20 duk wata wajen sayar da ganyayyaki’
‘Ina samun ribar Naira dubu 20 duk wata wajen sayar da ganyayyaki’

Alhaji Usman Haruna mai kimanin shekara 51 da ke sayar da ganyayyaki a Kasuwar Dare ta karamar Hukumar Gwagwalada, a Abuja. Ya tattauna da wakilanmu, inda ya bayyana yadda yake sayar da ganyayyaki, ribar da yake samu da kuma kalubalen da yake fuskanta a sana’ar. Ga yadda hirar ta kasance:

Me ya sa kake sayar da ganyayyaki?
Ina sayar da ganyayyaki ne saboda in dauki nauyin iyalina. Kasuwancin ba shi da wahala. Ina saye da sayarwa duk a nan rumfata. Akan kawo mini ganyayyaki har zuwa rumfata, sannan masu saya ma sukan zo rumfata su saya. Don haka ba abu ne mai wahala ba.
Daga ina ake kawo maka ganyayyakin da kake sayarwa?
Ana kawo mini daga kauyukan Paiko da Rafin Zurfi da Yugwa dukkansu a karamar Hukumar Gwagwalada suke.
Wadanne ganyayyaki kake sayarwa?
Akwai latas da salak da kabeji da alayyahu da sauransu.
Yaya za ka kwatanta ribar da kake samu?
Akwai riba sosai, nakan samu riba fiye da ta dubu 20 a kowane wata.
Hakan na nufin sayar da ganyayyaki na dauke maka dawainiyar iyalinka?
Yau da gobe sai Allah. Ina yi abu daidai ruwa daidai tsaki, ma’ana ba na kinkimo duk wani abu da ya fi karfina. Ina da mata daya da ’ya’ya takwas, duk a cikinsu babu wanda yake aiki, sun dogara a kaina. Ni nake ciyar da su da dan abin da na samu daga wannan kasuwancin.
Su waye suke gudanar da wannan sana’ar da kake yi?
Akwai mutane da yawa, akwai maza wadanda shekaranmu suke daya da suke sayar da ganyayyaki. Su ma da wannan kasuwanci suke daukar nauyin iyalinsu.
Ko kuna da kungiya?
Eh, muna da kungiya. Mun kafa ta tun a shekarar 2011, amma ta mutu a 2013. Dalilin da kungiyarmu ta mutu kuwa shi ne, mambobinta ba sa ba da hadin kai. Ina daya daga cikin wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen kafa kungiyar. Ni ne sakatarenta, a yanzu muna bakin kokari wajen ganin mun farfado da ita.
Wadanne kalubale kake fuskanta?
Babban kalubalen da nake fuskanta shi ne, ina shan wahala kafin in samu ganyayyaki daga wurin manoma. Wani lokacin farashin da nake saya yakan karu, amma kwastomomina ba sa gane hakan. A lokacin damina manoma suna noma cikin sauki, saboda ganyayyaki suna samun isasshen ruwa. Amma a lokacin rani suna shan wahala, hakan ya sa suke kara farashin ganyayyaki.
Yaya dangantakarka da kwastomomi?
Ina da kyakkyawar dangantaka tsakanina da kwastomomina. Amma wani lokaci nakan samu wadansu da ba su da hakuri. Sannan masu neman arha sun yi yawa.
Wacce shawara za ka ba masu sana’a irin taka?
Ina ba su shawara su tsayar da gaskiya a kasuwancinsu, sannan su guji duk wani abu da zai bata musu suna.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya