Ina samun rufin asiri a sana’ar kayan gwari – Aminu Bakori

Aminu Safiyanu Abdullahi Bakori wani matashi ne dan shekara 25 da haihuwa, wanda ya kammala Kwalejin Nazarin Larabci Da Shari’a ta Malam Aminu Kano, inda ya samu shaidar takardar Difloma kan Shari’a. Ya rungumi sana’ar sayar da kabeji da sauran kayan rafi a Kalaba Jihar Kuros Riba. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana dalilan da […]

Ina samun rufin asiri a sana’ar kayan gwari – Aminu Bakori
Ina samun rufin asiri a sana’ar kayan gwari – Aminu Bakori

Aminu Safiyanu Abdullahi Bakori wani matashi ne dan shekara 25 da haihuwa, wanda ya kammala Kwalejin Nazarin Larabci Da Shari’a ta Malam Aminu Kano, inda ya samu shaidar takardar Difloma kan Shari’a. Ya rungumi sana’ar sayar da kabeji da sauran kayan rafi a Kalaba Jihar Kuros Riba. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana dalilan da

Aminiya: Me ya sanya ka rungumi yin sana’a maimakon tsararrakinka suna makaranta ko kai kana makarantar?
Aminu Bakori: Ni nan da ka gani na yi makaranta tun daga firamare har ta gaba da sakandare. Na yi Kwalejin Nazarin Harkokin Shari’a ta Malam Aminu Kano kuma yanzu haka ina da takardar shaidar Difloma kan shari’a da kuma dokoki.    
Aminiya: Ga wannan sana’a taka ta so ta yi kama da sana’ar sayar da kayan rafi, wadda ake ce wa kayan gwari sai dai taka tana da bambanci, me haka ke nufi?
Aminu Bakori: E, duk daya ce sai dai tawa tana da fasalinta daban, domin ni ina sayar da kabeji ne da kuma sauran kayan rafi na gwangwani, irin wadanda ake sayarwa a kasashen Turawa, ina gaurayawa da su karas da latas da koren barkono da koren wake da kokumba d albasa da kuma dankalin Turawa.
Aminiya: Ka yi bayanin kayan sayarwa, wane kalubale kake fuskanta wajen safarar kayan daga Arewa zuwa nan Kalaba?
Aminu Bakori: Babbar matsalar da muke samu idan za mu dauko kayan daga Jos zuwa Kalaba ita ce mota. Misali, yau Litinin gobe Talata za mu je kasuwanni mu sayo kaya mu zo mu tara su, a sanya cikin buhunhuna; wani lokaci sai su yi kwana biyu ma ba a samu motar da za ta kwaso su ta kawo mana su nan ba. Sannan kuma sai sun kwana kamar uku ko hudu ma kafin su iso mana nan Kalaba. Gaskiya muna samun matsala don wani lokaci kayan ma suna rubewa kafin su iso mana nan, kaya irin su kokumba da koren tattasai da wake su kaya ne da ake bukata su zo a rana daya kuma a sayar da su kan lokaci.
Wata matsalar kuma zafi na yi wa latas kabeji illa suna lalacewa, wannna ma rashin kyawun hanya na sufurin motoci ya dada taimakawa matuka gaya.
Aminiya: Don haka dai wannan babban kalubale ne ga kasuwancin ka?
Aminu Bakori : kwarai kuwa hakika.
Aminiya: Dayake mun ji akasi bari mu ji bangaren alherinta. Ana yi wa wannan sana’a kirari da ‘yau sarki gobe talaka’ me za ka ce a nan?
Aminu Bakori: To ka san sha’anin kasuwa yadda take, wani lokaci kam alhamdu lillahi, wani lokaci kuma idan ta juya baya mukan ji jiki. Idan har Allah Ya sa kana da kayan kuma ana bukatar su, ga shi ba su a kasuwa, nan da nan za ka ga ana gaggauta sayen kayan. Yanzu mutum ya sayar ya samu alheri.
Aminiya: Wadanne nasarorin ake samu a wannan sana’a?
Aminu Bakori: E, to gaskiya wannan kasuwanci alhamdu lillahi, saboda kasuwanci ne na abin da mutane suke bukata. Kaya ne na yau da kullum.
Aminiya: Daga lokacin da ka fara wannan sana’a zuwa wannan lokaci da muke wannan hira ko kwalliya ta biya kudin sabulu?
Aminu Bakori: E, alhamdu lillahi saboda a wannan sana’a na sayi abubuwa na ajiye, na samu ci gaba sosai a cikinta tun da zan ci, zan yi sutura, zan taimaka wa iyayena da ’yan uwa har ma da abokan arziki. Ga shi kuma ina zaune da jama’a lafiya, ’yan Arewa da kuma ’yan asalin wannan yanki.
Aminiya: Mene ne babban burinka a wannan sana’a?
Aminu Bakori: Ubangiji ya daukaka min wannna sana’a, ya daukake ni ni ma in samu in ga na kyautata wa rayuwa ta don ba dole ba ne in ce sai na yi aikin gwamnati duk da ina da ilmi bakin gwargwado. Amma ina son yin sana’a domin ni ma in ga wasu na ci a karkashina, suna yin aiki tare da ni don su samu abin rufin asiri su ma.
Aminiya: Dayake a Najeriya muna da mashahuran ’yan kasuwa, za ka so kai ma ka ga ka kai kamar su a kan wannan harka taka?
Aminu Bakori: Alhamdu lillahi, ina so domin in ga ni ma na bude wasu wuraren sana’a da wasu za su karu, su ci abinci karkashina, tun da kowa so yake yi ya ga ya ci gaba a kan harkokinsa .
Aminya: Kai matashi ne tun da ko shekara talatin ma ba ka kai ba, sai ga shi wasu matasan kan kyamaci yin sana’a komai kankantarta wace shawara kake dauke da ita ga irin wadannan matasa, musamman da kan bi ’yan siyasa suna maula ko aikin bangar siyasa?
Aminu Bakori: Ina ba matasa shawara su je su koyi sana’a koda ta hannu ce, idan suka yi hakuri za su cin ma nasara amma dogara da iyayenka suna da kudi ko wani dan uwa, wannan duk ba riba ba ce. A kama sana’a ya fi domin yau a duniya duk wani wanda ka ji ya shahara a kudi ko dukiya ta hanyar kasuwanci ya same ta ya kuma tara. Allah Ya taimake mu da kasarmu a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma karuwar arziki.