Ina  sane da matsalolinku Sarkin Gona

Mai martaba Sarkin Gona da ke Jihar Gombe, Alhaji Umar Abdulkadir Abdussalam II ya ce yana sane da matsalolin al’ummar yankin Bomala kan yadda masarautar take a halin yanzu. Sarkin Gona ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi ayarin Dagacin Bomala sa suka kai masa ziyarar gaisuwa kan nadin da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya […]

Ina  sane da matsalolinku Sarkin Gona

Sarkin Gona Alhaji Umar Abdulkadir

Mai martaba Sarkin Gona da ke Jihar Gombe, Alhaji Umar Abdulkadir Abdussalam II ya ce yana sane da matsalolin al’ummar yankin Bomala kan yadda masarautar take a halin yanzu.

Sarkin Gona ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi ayarin Dagacin Bomala sa suka kai masa ziyarar gaisuwa kan nadin da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya yi masa a matsayin sabon Sarkin Gona.

Sarkin ya ce kafin ya zama Sarkin Gona ya san duk wata matsala ta Bomala domin yana zuwa Bomala idan ya tashi daga aiki lokacin yana aikin banki.

Ya nuna farin cikinsa da wannan ziyara ta mutanen Bomala , inda ya ce rokon da suka yi na a sama musu wakilci a fadar Gona zai duba domin ya san sun cancanci haka. Daga nan sai ya nemi hadin kansu wajen ganin masu unguwanni da masu filaye suna fitar da layuka wajen sayar da filaye don a samu layuka isassu don rage cinkoso a garin.

A jawabin Dagacin Bomala Alhaji Dauda Tafida, ya ce yadda Allah Ya tabbatar masa da wannan sarauta ya sa suka jaddada biyayyarsu ga sabon Sarkin.

Sai ya tabbatar wa Sarkin cikakken hadin kai da goyon bayan mutanen Bomala ga masarautar tasa.

Da yake jawabi tun farko Magayakin Bomala Alhaji Babangida cewa ya yi sun zo ne don jaddada mubaya’arsu ga sabon Sarkin domin mutanen Bomala ’ya’ya ne ga Masarautar Gona.

Daga nan sai ya yi addu’ar Allah Ya wuce wa Sarki gaba a dukkan lamuransa da kuma ba shi ikon yin mulki bisa adalci.