Ina shugabannin Arewa suka dosa?
Tun daga lokacin da aka yi wa jam’iyyar APC rajista a karshen watan jiya al’amura suka fara canjawa a fagen siyasar kasar nan, kuma kafin lokacin da za a yi zaben gama-gari a watan Afrilun shekarar 2015 Allah kadai Ya san abin da zai iya faruwa. Da farko wannan rajista ta canja kidan da talakawa […]
Tun daga lokacin da aka yi wa jam’iyyar APC rajista a karshen watan jiya al’amura suka fara canjawa a fagen siyasar kasar nan, kuma kafin lokacin da za a yi zaben gama-gari a watan Afrilun shekarar 2015 Allah kadai Ya san abin da zai iya faruwa. Da farko wannan rajista ta canja kidan da talakawa ke yi wa jam’iyyun siyasa, kuma nan take jam’iyyar PDP da sauran ke kira babbar yaya ta canja rawa, ta kuma gaggauta sanya sabuwar taguwar da zamani ya dinka don kar a bar ta a baya. Haka nan ma ‘ya’yan wannan jam’iyyar sun dukufa wajen danne kirjin uwarsu, suna ba ta hakuri don kishiyar da aka yi mata, ganin yadda ta kidime, ta gigice, ta fice daga cikin kyakkyawan hayyaci.
To amma ita jam’iyyar PDP cewa take yi ba ta damu ba game da haka, domin a cewarta kunun zaki ba zai ba koko tsoro ba, kuma shugabanninta na ganin sabuwar jam’iyar karar kada miya ce kawai, domin gara da ita da a ce babu abokiyar adawa kwakkwara. A yanzu jam’iyyar PDP na cikin tunanin dabarun a za ta bi don magance tarkon da sabuwar jam’iyyar ta kafa mata, da kuma yadda za ta tsallake shingayen da ta gicciya a bisa turbarta, sai kuma ga shi nan hukumar zabe ta yi mata famin mikin da ta rigaya ta yi mata: ta sake yi wa wasu jam’iyyu biyu rajista, ciki kuwa har da ta Peoples Democratic Mobement, PDM ta wani hamshakin danta, tsohun mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Turakin Adamawa, wanda ya sha karya mata tsinke tsire a idanu a lokuta da yawa. Wannan al’amari bai yi wa jam’iyyar PDP da mutanen Arewan da suka fi yawa a cikinta dadI ba, domin kuwa an kara daukar matakin wargaza hadin kansu ne a fakaice. Yawan jam’iyyun siyasa da ‘yan
Arewa ke goyon baya ba a’ala ba ne a gare su, ganin cewa hakan zai sa su gama nika ne ‘yan kudu su kwashe garin bayan sun rarraba kuri’unsu. A takaice dai ana iya cewa fatan Turakin Adamawa da sabuwar jam’iyarsa ta PDM shi ne Allah ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba zai yi barna.
Wannan batu hakkun ne. Masu lura da al’amura na ganin cewa hakan ba karamin gurgunta hankoron haurowar mulki shiyyar Arewa zai yi ba, domin kuwa al’amari ne da zai kara farraka al’ummominta wadanda tuni ‘yan Kudu suka daidaita, bayan sun yi amfani da bambance-bambancen addini da tsagwaron kabilanci don shiga tsakaninsu, har suka haddasa bakar gaba da kiyayya wacce a halin yanzu, ke tayar da zaune a Arewar, su kuma wadanda suka haddasa hakan suna zaune lafiya, kansu a dinke. A yau manyan shugabanni da talakawan Arewa ke tsammani za su agaza musu tsira daga sharrin makiyansu na cikin gida da ketare sun shantake, domin kuwa sun rigaya sun juya masu baya, ba su tare da su, sun gwammace biye ra’ayin farraka Arewa don ganin bayanta da kuma dakile burin ‘ya’yanta da kuma dankwafar da yunkurin masu daga matsayin yankin Arewar da kyautata halayyar rayuwar al’umman cikinta.
A halin yanzu manyan Arewa sun kasa samar da kwakkwarar kungiyar guda daya tilo, da za ta yi magana da murya guda, suna ji, suna gani ana ta haihuwar kungiyoyi, yu-yu-yu, maimakon da daya kwakkwara, wadanda ke kara rarraba kawunan Arewar, sa’annan kuma fitattun kungiyoyin Arewa kamar Northern Gobernors Forum, Northern Union, Arewa Consultatibe Forum da kuma Northern Elders Forum sun kasa hada kai, su kalli alkibla guda, sun zame ‘yan kore manyan shugabannin al’ummomin kudanci, su ne ke wucewa gaba a dukkan harkokin da ake kullawa don durkusar da Arewa. Tun ba yau ne ba shugabannin Arewa ke yaudarar jama’a, suna cewa su ne suka fi kowa kishin Arewa. To amma kishin Arewar suke yi, ko kuma gyara zamansu suke yi, ko fafutikar neman abin duniya daga hannun ‘yan koren Yahudu da Nasara da ke kudancin kasar nan? Har yanzu dai talakawan Arewa ba su ga fa’idar wannan kishin da shugabanninsu ke yi ba, domin ba su tsira daga sharrin magabtansu ba.
A yanzu ma take-taken shugabannin Arewar na nuna cewa za a koma gidan jiya, babu wani abin da za su iya yi don kauce wa tsohuwar dabi’arsu ta agaza wa ‘yan siyasar kudanci a kaikaice da niyyar dakushe dukkan kokarin da ‘yan Arewa za su yi don cire wa kansu kitse a wuta a zaben 2015. Wai shin ina shugabannin Arewa ne suka dosa? A haka za a ci gaba da tafiya? Lallai da sake, domin ba za ta sabu ba, wai bindiga a ruwa