Ina so a haramta sayar da bindiga a Amurka — Biden
Ya zama dole majalisun dokokin kasar su tashi tsaye wajen dakile wannan masifa.
Shugaban Amurka Joe Biden ya sabunta kiran a tsaurara matakan mallakar bindigogi tare da haramta sayar wa fararen hula ’yan kasar makamai masu sarrafa kansu.
Sabunta kira da Shugaba Biden ya yi na zuwa ne kwana guda bayan da wani dan bindiga ya kashe mutane 8, a wani babban shagon sayar da kayayyaki da ke Jihar Texas.
- Shugabancin Majalisa: APC ta goyi bayan Akpabio da Tajuddeen
- An kama dan Najeriya yana safarar Hodar Iblis a Saudiyya
Hoton bidiyon da ya yadu, ya nuna yadda maharin ya yi amfani da bindiga mai sarrafa kanta, wajen bude wa jama’a wuta a harabar katafaren shagon sayar da kayayyakin da ke yankin Allen a jihar ta Texas.
Bayanai sun nuna yadda nan take ya kashe mutane 7, kafin daga bisani wani dan sanda ya bindige shi, yayin da mutum na takwas da ke cikin wadanda dan bindigar ya jikkata, ya ce ga garinku nan a asibiti.
’Yan sanda sun ce a halin yanzu, mutane uku ke kwance cikin halin-rai-kwakwai-mutu-kwakwai, yayin da suke ci gaba da bincike kan maharin mai shekaru 33 da suka bayyana sunansa da Mauricio Garcia.
Jami’an tsaron dai ba su tantance dalilin da ya ingiza Mauricio ya aikata ta’addancin ba, sai dai kafafen yada labaran Amurka da dama sun ruwaito cewar masu bincike sun gano wasu sakwanni da ya rika aikewa a shafukansa na sada zumunta da ke nuna dan bindigar na goyon bayan wariyar launin fata da kuma ra’ayin ’yan Nazi.
Wata kididdiga ta nuna a shekarar bana kadai, mutane 199 ‘yan bindiga dadi suka kashe a hare-haren da suka kai a sassan Amurka.
Wannan na daga cikin abin da ya sa shugaba Biden nanata gargadin cewar ya zama dole majalisun dokokin kasar su tashi tsaye wajen goyon bayan daukar matakan dakile wannan masifa, ciki kuwa har da haramta sayar da bindigogi masu sarrafa kansu.