‘Ina so a tuna da ni a kan gaskiya da son ci gaban al’umma’
zai iya samun irin haka cikin sauki ba. Bakin gwargwado an samu nasarori masu dimbin yawa kuma muna yi wa Allah godiya. kalubalen rayuwa: kalubale na farko da na samu shi ne katsewar karatuna. Ba don cikin iyalan da na fito sun san muhimmancin ilimi ba da labarin nawa na daban ne ba wannan ba. […]
zai iya samun irin haka cikin sauki ba. Bakin gwargwado an samu nasarori masu dimbin yawa kuma muna yi wa Allah godiya.
kalubalen rayuwa:
kalubale na farko da na samu shi ne katsewar karatuna. Ba don cikin iyalan da na fito sun san muhimmancin ilimi ba da labarin nawa na daban ne ba wannan ba. Don an yi min aure ina da shekara 13 sannan na haihu a shekara 14. Hakan ya so ya takaita karatuna don ana yi wa karatun boko mummunan fahimta, amma ba haka Allah Ya tsara ba.
Rashin abin hannu ga mahaifiyata bai sa ta karaya wajen ci gaba da daukar nauyin karatuna tun ina karama ba. Tun ina karama mahaifinmu ya rasu amma bai sanya ta bari muka tsaya ba, sai da ta yi ta fadi- tashin ganin mun samu ilimi mai inganci kan haka ba mu nemi abu muka rasa a wurinta ba.
Wadda nake koyi da ita:
Tun ina karama ba wacce ke burge ni kamar mahaifiyata, kuma har yanzu haka abin yake. Allah bai kawo wata mace da ke burge ni kamar ta ba, don da muka rasa mahaifinmu ita ce ta zame mana gata, ba mu rasa komai ba har muka samu namu.
Ta ba mu tarbiyya har ta zame mana abin koyi wurin dabi’unta da hakuri. Ba wanda nake muradi da ganin kimarsa kamar mahaifiyata. A duniyar karatu kuwa ina koyi da Nana Asma’u ’yar Muhjaddadi danfodiyo yadda ta sadaukar da rayuwata kan ilimi ni ma haka nake son zama.
Burina a lokacin yarinta:
Burina na kuruciya ya cika. A lokacin da nake karama ba ni da wani buri da ya wuce na zama ‘yar jarida ko lauya. A lokacin da nake karatun digirina na farko na yi aiki da Hukumar Gidan Rediyon Jihar Sakkwato wato (Rima Rediyo) da gidan talabijin na kasa (NTA) a matsayin ma’aikaciyar kwantaragi. Bayan kammala karatuna kuma sai na zama lauya.
Kwalliyata da sha’awata:
Duk da yake sha’anin aikina bai bari na yi kwalliyya kullum ana cikin bakaken kaya amma duk lokacin da ban da zuwa kotu nakan yi sha’awar sanya Atamfa in yi kwalliya da ita. Ina da sha’awar in kasance tare da mahaifiyata muna hira. Ban da wani wuri da nake son ziyarta da ya wuce wurin mahaifiyata. A fanin wasanni kuwa ina sha’awar yin gudu ko a can Tokiyo sai da na yi gudun famfalaki (marathon) tseren kilomita 45 ne. Sannan ina sha’awar hawan duwatsu da wasan motsa jiki da kuma yoga.
kasashen da na ziyarta:
Na je Ingila da Sukotiland (Scotland) da Japan da Saudiyya da Austireliya da Masar da Dubai da Sifen da Doha a katar, a Najeriya kuwa na ziyarci mafi yawan jihohinta.
Shawarara ga mata:
Duk abin da za ki yi ki dauke shi da muhimanci. Ki kare martabar kanki. Duk macen da za ta yi hakan, ta taimaki kanta da danginta. Rashin kamun kai ne ke sanya wasu mazaje shakkun barin matansu yin ilimin boko, amma ki san darajar gidanku da kanki za a bari ki fito don ba da taki gudunmuwa da kwarewar da Allah Ya ba ki.
Mata ku tsarre gaskiya. Sirrin nasarata da na samu bai fi tsare gaskiya ba. Zan fada maka ita (gaskiyar) koda rai zai baci. Ina son bayan rayuwata a tuna da ni a kan gaskiya da taimakon al’umma.
Fitowar mata a banggaren shari’a:
Da farko dai akwai cikas don ana ganin shekarun sun yi yawa, amma yanzu an samu ci gaba don gane alfanun karatun ga ’ya mace, domin idan ta yi shi ko ba ta je kotu ba zai amfani mijinta da ’ya’yanta da danginsu da al’umma gaba daya.
In ka je Ma’aikatar Shari’a ta Sakkwato fiye da kashi daya bisa uku na ma’aikatan mata ne. Ko a ajujuwanmu da muke karantarwa a jami’a akwai inda mata suka fi yawa. Ana samun cigaba sosai kuma muna fatan hakan zai ya dore.