Ina so a tuna da ni a kan gaskiya da son ci gaban al’umma – Dokta Balkisu Sa’idu
Tarihinta Sunana dai Balkisu Sa’idu. An haife ni a Unguwar Rijiyar dorawa da ke cikin garin Sakkwato. Ina daga cikin ’ya’ya 15 da Allah Ya albarkaci mahaifanmu da su, 12 sun rasu mu uku muka rage. Na yi karratun firamare a Unguwar Rogo, wadda ake kira Sultan Ibrahim Dasuki a yanzu. Na kare a1985 daga […]
Tarihinta
Sunana dai Balkisu Sa’idu. An haife ni a Unguwar Rijiyar dorawa da ke cikin garin Sakkwato. Ina daga cikin ’ya’ya 15 da Allah Ya albarkaci mahaifanmu da su, 12 sun rasu mu uku muka rage. Na yi karratun firamare a Unguwar Rogo, wadda ake kira Sultan Ibrahim Dasuki a yanzu. Na kare a1985 daga nan na tafi sakandaren ’yan mata ta Nana, ina cikin aji na uku ne aka yi min aure a lokacin ina da shekara 13. Bayan na samu juna biyu ne dole na bar zuwa makaranta don a lokacin ba a barin matan aure su je makaratar sakandare. Sauka ta lafiya ke da wuya na hadu da wasu matsaloli amma duk da haka sai da na koma makarantar je-ka- ka-dawo ta ’ya’yan sojoji a nan Sakkwato inda na kammala sakandaren a 1990.
Daga nan na wuce Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Jihar Sakkwato na yi karatun share fagen shiga jami’a. Da na kammala sai Allah Ya kaddari na samu gurbin karatu a Jami’ar Usman danfodiyo a Tsangayar Ilimin shari’a inda na kammala a 1998. Cikin ikon Allah a shekarar ni ce wadda ta fi samun nasara a tsangayar gaba daya. Na samu kyaututttuka da dama wadanda suka sanya kofa ta bude min.
Bayan na koma makarantar kwarewa a harkokin shari’a ta Abuja ne sai na samu aikin koyarwa a jami’ar da na kammala wato Jami’ar danfodiyo. Bisa shawarwarin da aka ba ni ne ya sanya na nemi aikin. An dauke ni ne a shekara ta 2001, amma ban fara ba sai a 2002, saboda juna biyun da nake dauke da shi. Tun daga watan biyar na shekarar da na fara aiki ina tare da jami’ar har zuwa yau.
A lokacin da nake karatu a Abuja na fara koyon aikin Lauya a Kamfanin Lauyoyi na Amana Chambers karkashin J. C. Shaka daga baya aka fadada wurin ya koma mahadar Umaru Shinkafi da sauransu, su ma har wannan lokacin ina tare da su. Samun gurbin koyarwa a jami’a ya ba ni damar karo illmi a wurare daban-daban. Misali a shekarar 2003, gwamnatin Ingila a wani tallafi da take bayarwa na karatu ta dauki nauyin karo karatun digirina na biyu a Jami’ar Dondi da ke Sukotland inda na karanci fannin dokoki da dabarun tafiyar da al’amurran man fetur.
Na kammala karatun a shekarar 2004, bayan na kammala ne suka kara daukar nauyina na karanci kwas biyu, na farko nema da sanin inda ma’adinan man fetur suke a karkashin kasa, na biyun yadda ake bayar da lasisin tonon ma’adinan albarkatun kasa kamar zinari da sauransu, kuma duk na karbi shaidar kammalawa cikin gagarumar nasara.
Dukkanmu wadanda suka samu tallafin kafin mu tafi Ingila a 2003 sai da gwamnatin ta tura mu Jihar Lagas inda aka ba mu horarwa kan sha’anin shugabanci. A shekarar 2005 gwamnatin Ingila ta sake mayar da mu makarantar koyon kasuwancin da ke Legas don kara jaddada mana kwas din shugabanci da muka yi a baya.
Kammala kwas din ke da wuya sai na koma Jami’ar danfodiyo na ci gaba da karantarwa a fanin shari’a. Cikin ikon Allah a shekarar 2007 gwamnatin Japan ta ba ni tallafin karo karatun digirina na uku a kasarsu a birnin Tokyo. Na yi karatun ne a fanin makamashi, shari’a da ka’idojinsu (Energy Law Policy).
Na kammala karatun a shekarar 2012. Girggizar kasa da ta hallaka mutane da dama da aka yi a kasar a shekarar 2011, ina can aka yi ta, Allah Ya tsare ni na kammala na dawo gida. Daga nan Jami’ar Ibadan ta nemi in rika zuwa can ina karantar da dalibansu kwas din dokokin ma’adinai, kasancewar ba su da kwararre sosai a wannan fanni.
Da amincewar Jami’ar danfodiyo, har zuwa wannan lokaci ina tare da su a kowace shekara nakan je in karatar da dalibansu in dawo a matsayin malama mai ziyara (bisiting Lecturer). Allah Ya albarkace ni da ’ya’ya biyu, Muhammad Munir da Muhammad Bello.
Ayyukanta:
Na yi ayyuka da dama. Bayan zamana malama kuma ni cikakkiyar lauya mai zuwa kotu ce. A shekara ta 2012 ni ce Edita kuma mai ba da shawara kan fanin shari’a ta wata mahada tamu.
kungiya ce da ake kira Nigerian Association for Energy Economics, watau kungiya ce ta kwararru a bangaren tafiyar da harkokin makamashi da shari’a da tattalin arziki.
Wakiliya a kungiyar lauyoyi ta kasa a Sakkwato a 2014, an zabe ni a matsayin mataimakiyar shugaba ta jiha, mukamin da nake kai har zuwa yanzu. Na yi ayyukka a kwamitoci da dama nan gida da kasa baki daya. A kwanan nan ma ina cikin kwamitin da kasa ta sanya wanda da zai tsara taron kasa na 2015.
Yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima da aka yi a 2012 ina cikin wadanda gwamnatin jiha ta gayyato don wannan aikin na tantance bayanan da jiha za ta gabatar a kasa. A 2006 kuma ina daga cikin kwamitin aikin hajji na jiha. A jami’a kuma ina cikin kungiyar malaman Jami’a watau ASUU.
Ina aiki da hukumar kasar Inggila ta dauke ni a matsayin mai koyar da dallibai kwasakwassai na fahimtar da mutum aikin da za a ba shi, tun a 2013. Kwanan nan na dawo daga Legas wajen irin wannan aikin. Wadansnan kawai nake iya tunawa a yanzu.
Nasarorinta:
Ba zan so na fadi cewa ni ce ta farko kan kaza da kaza ba, amma ina ganin al’umma su ne za su fadi wannan.
Babbar nasarar da zance na samu bai fi Allah Ya ba ni dama na samu kwakkwaran ilmin addinin Musulunci da na Boko duk da na fito daga gidan talakkawa marasa karfi. Allah Ya ba ni iko na je makarantun da kudi ma ba za su iya kaini can ba.
Kamar Jami’ar Tokyo a duk kasar ita ce ta farko ko ta biyu mafi martaba wurin ba da ingantaccen ilmi. In ka ji kudin da ake kashe wa a wurin na shekara tunaninka ma ba zai yarda za ka iya zuwa wurin don neman ilimi ba.
Da yardar Allah ne gwamnatocin da ba na kasata ba suka dauki nauyin karatuna. Allah Ya sanya wa yarana albarka kuma na yi tsawon rayuwa da mahaifiyata wadda addu’ar ta ce sirrin nasarorina. Ni ce Dakta ta farko a bangaren shari’a a wannan banggare namu.
Duk da cikas da na samu a farkon karatuna bai hana cimma burina. Ba nasarar da ta fi a duniya a ce ana yi da kai a bangaren karatunka. Kuma na samu gayyata da kyaututtuka iri-iri wanda ba kowane namiji