Ina so a tuna da ni wajen taimakawa masu rauni – Dokta Malbasatu Ibrahim

Dokta Malbasatu ita ce Amira ta Tarayyar kungiyar Mata Musulmi Ta kasa (FOMWAN) da ke Jihar Sakkwato. Mace ce hazika mai kamala da mutunci da ke son ayyukkan alheri na da’awa da fadakarwa. Tana cikin sahun gaba na matan da ke jihar Sakkwato da suka sadaukar da kansu wajen ganin mata Musulmi sun samu cigaban […]

Ina so a tuna da ni wajen taimakawa masu rauni – Dokta Malbasatu Ibrahim
Ina so a tuna da ni wajen taimakawa masu rauni – Dokta Malbasatu Ibrahim

Dokta Malbasatu ita ce Amira ta Tarayyar kungiyar Mata Musulmi Ta kasa (FOMWAN) da ke Jihar Sakkwato. Mace ce hazika mai kamala da mutunci da ke son ayyukkan alheri na da’awa da fadakarwa. Tana cikin sahun gaba na matan da ke jihar Sakkwato da suka sadaukar da kansu wajen ganin mata Musulmi sun samu cigaban rayuwa a kowane fanni. Aminiya ta zanta da ita kamar haka:

Asalinta:

An haife ni a karamar Hukumar mulkin Yabo dake Jihar Sakkwato a shekarar 1966. Na yi karatun Firamare a garin Yabo inda na fara a shekarar 1972 zuwa 1979 kammalawata ke da wuya aka kai ni makaranatar mata ta kwana dake karamar Hukumar Rabah inda na yi karamar sakandare sai aka mayar da ni makaratar mata ta kwana dake garin Sakkwato watau GGC na kare a shekarar 1984. Takarduna ba su yi kyau ba sai na tafi makaratar gwamnatin tarayya ta ilmin kimiya da fasaha na yi karatun share fage (remedial) shekara daya sai na wuce Jami’ar jihar Sakkwato na karanci ilmi da Hausa wato B.A (Ed) Hausa, na kammala a 1990. Daga nan harkokin iyali suka dauke hankalina ban sake komawa karatu ba sai a sheakrar 1997inda na yi digiri na biyu kuma na kamala a 2000. Daga nan na sake dauke kaina daga wannan fannin sai da malamina Farfesa Malami ya sake ba ni shawara sa’annan na koma na yi karatun digiri na uku a shekarar 2003. Na hadu da wasu matsalolin da ya sanya na dakatar da karatun amma na kammala a 2010. A halin yanzu ni Dokta ce a fannin Adabin Hausa.

Ayyukkanta:
Na fara karantarwa tun lokacin da na tafi bautar kasa a Jami’ar Usman Danfodiyo dake Jihar Sakkwato. Bayan nan na samu aikin koyarwa a makaratar mata ta Gwamanati GGC da ke Sakkwato, na yi shekara uku a can, na bar nan na koma Kwalejin kere-kere ta Farfaru a matsayin shugabar sashen ilmin Musulunci da Hausa na yi shekara biyu, aka mayar da ni Kwalejin tunawa da Giginya a matsayin malama har na zama mukaddashiyar shugabar makarantar na tsawon shekara biyu, daga nan na koma aiki da UNICEF kan harkokin ilmin mata na zama ko’odinatarsu ta karamar hukumar Rabah tun shekara 2005 zuwa 2008. Daga nan na koma yin aiki a SBMC a matsayin shugabar kwamitin da zai kula da makarantun da ke Shiyyoyi uku na Sakkwato watau (Sanatorial District). Bayan nan na koma malanta a makaratar fasaha da kere-kere ta Jihar Sakkwato a matsayin malama. Na yi shekara biyar tare da su yanzun kuma ina tare da kungiyar Mata Musulmi (FOMWAN) a matsayin Amira.

kungiyoyin da take ciki :
kungiyar mata musulmi ta kasa reshen Jihar Sakkwato da kungiyar ciyar da karatun mata a gaba na fasaha dake makarantar fasaha da kere-kere ta jihar Sakkwo (WITED) da kwamitin daidaita ilmin fasaha a cikin al’umma da kwamitin ilmi da shugabanci na FOMWAN, Mamba ce a kungiyar NACA da ta kula da ciwon kanjamau da sauran kungiyoyin ci gaban al’umma.

Rubuce-rubucenki:
Gudunmuwar mata a habaka rubutaccen adabin Hausa, da karuwanci a mahangar mawakan Hausa da Zuwaira Isah, kallabin da ake neman a manta da Hoton mata cikin fina-finnan Hausa da tasirin Fina-finai da rubutattun kagaggun labarai na Hausa ga matasa da mata, sai gudunmuwar matan Hausa (waka ce a harshen turanci.)

Shawararta ga mata:
Ina son na yi kira ga iyaye mata da su kyale diyansu mata su yi karatun gaba da sakandare domin su ba da gudunmuwar da ta kamata. Za mu cigaba da taimakon duk

wata yarinya dake son karatu matukar mahaifanta ba su da hali. Sa’annan su ji tsoron Allah su dage ga neman ilmin zamani da na boko, kuma a samu sana’a don zama babu sana’a matsala ne.

 

Ina so a tuna da ni wajen taimakawa masu rauni – Dokta Malbasatu

 

Abin da ya fi burgeki:
Gaskiya abin da ya fi burge ni shi ne na taimaki mai rauni, ya yi karatu kamar yadda na yi don ina bakin ciki na ga macen da ba ta da ilmin zamani da na Islama.

kasashen da ta ziyarta:
Saudi Arebiya da Kairo da Mali da Senegal Itopiya da Uganda da Dubai, amma duk a cikinsu na fi sha’awar Saudi Arabiya

 

 

Abin da take son a tuna ta da ita:
A tuna da ni a halayen kirki kamar hakuri da yafiya.

Ko akwai abin da ya faru da ke wanda ba za ki taba mantawa da shi ba?
Akwai shi, lokacin ina yarinya na taba raka mahaifina wani kauye mai suna Jabo kuma a ranar ranar Lahadi ne, watau ranar cin kasuwa, ba mu samu mota ba sai muka fara tafiya a kasa daga nan ne wadansu fatake suka hadu da mu, suka ce mu biyo su, gudun kada wani abu ya samemu haka muka yarda muka bi su. Nana muka rika takawa a kasa, tun da azahar muke bin su a kasa amma ba su isa wani gari ba sai bayan sallar Isha’i. Nan muka isa wani gari mai suna Tage da ke cikin karamar hukumar shagari wurin 11 na dare, nan muka kwana sannan suka sanya mu a cikin mota zuwa garinmu. Gaskiya mun sha wahala sosai a wannan tafiya kuma ba zan taba manta da wannan abu da ya faru da ni ba. Sannan ban mance gawar fir’auna da dutsunan da na gani a can ba a lokacin da na kai ziyara kasar Masar.