Ina so in bar muku jihar da za ku yi alfahari da ita ce a bayana – El-Rufa’i
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya nanata niyyar gwamnatinsa wajen tafiya da kowa tare da gudanar da ayyukan raya kasa ba tare da fifita wani sashi a kan wani ba. Gwamna El-Rufa’i ya bayyana haka ne a wajen taron karrama Mataimakiyarsa Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe da mutanen Kudancin Kaduna suka shirya a garin […]
Gwamna Nasiru El-Rufai na Jihar Kaduna da Mataimakiyarsa
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya nanata niyyar gwamnatinsa wajen tafiya da kowa tare da gudanar da ayyukan raya kasa ba tare da fifita wani sashi a kan wani ba.
Gwamna El-Rufa’i ya bayyana haka ne a wajen taron karrama Mataimakiyarsa Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe da mutanen Kudancin Kaduna suka shirya a garin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jama’a.
Gwamnan wanda ya bayyana zabin Dokta Hadiza a matsayin Mataimakiyarsa a matsayin zabin Allah, ya ce cikin mutum 32 da aka kawo masa, kowanne na da wanda ya tsaya masa in ban da DOkta Hadiza, wacce ya ce sunanta ma ba ya a kusa a jerin sunayen ’yan takarar.
“Kuma ban yi amfani da addininta ko kabilarta ba, face cancantarta da kuma gogewarta. Kuma duk wata dama da za a samu a gwamnatina in dai akwai mace a ciki to akwai yiwuwar ta samu fiye da namiji matukar ta cancanci wannan aiki. Wannan shi ne aikin da muka sanya a gaba da suka hada da karfafa zaman lafiya da bunkasa noma da ilimi a fadin jihar. Burina shi ne in bar muku jihar da za ku yi alfahari da ita ko bayan ba na nan,” inji shi.
Ya ce da farko ya yi takaicin rabuwa da tsohon Mataimakinsa Bala Banted saboda nagartansa amma tunda ya matsa kan zai tafi neman Sanata don samar da kyakkyawan wakilci a majalisa sai hakan ya bayar da damar sake fitar da wata hazikar daga yankin, wacce ta tattara dukkan abubuwan da ake son shugaba da shi.
Da take jawabin, Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe ta bayyana farin cikinta da wannan girmamawa da jama’ar yankin da ta fito suka yi mata, inda ta yaba wa Gwamna El-Rufa’i kan damar da ya ba ta wajen fito da ita har jama’a suka ga ta cancanci su karrama ta.
Sannan ta yi kira ga jama’ar yankin su yi watsi da bambancin addini da siyasa da kabilanci domin mara wa gwamnatinsu baya wajen ciyar da Jihar Kaduna gaba bisa ga kyawawan kudirorin da gwamnatinsu ke dauke da su na ci gaban al’umma.
Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Jama’a da Sanga inda Mataimakiyar Gwamnan ta fito, Mista Shehu Nickolas Garba (Sarkin Noma) ya jinjina wa Gwamnan, inda ya ce hatta mutanen Kudancin jihar ba su san suna da mace mai hazaka kamar Dokta Hadiza ba sai da ya fito da ita duniya ta shaida irin zakakuran shugabannin da yankin ke da su.
Daga nan ya roki Gwamnan ya karkato da aikace-aikacen da yake yi a sauran wurare musamman na tituna zuwa yankin Kudancin Jihar “Domin yanzu lokacin shugabanci ne ba na siyasa ba,” inji shi.
A karshe Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya mika kambin girmamawa ga Gwamnan Jihar Kaduna da Mataimakiyarsa.
Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe ita kadai ce mace Mataimakiyar Gwamna a duk jihohin Arewa.