Ina so in dora daga inda mahaifina ya tsaya – Saleem Tijjani Ibrahim
Babu shakka tarihin masana’antar fim din Hausa ba zai cika ba tare da ambaton sunan marigayi Darakta Tijjani Ibrahim ba, wanda ya rasu kusan shekara 11 da suka gabata, a yanzu dansa Saleem dan shekara 27 ya lashi takobin dorawa daga inda ya tsaya. A wannan tatatunawa da ya yi da Aminiya ya bayyana irin […]

Babu shakka tarihin masana’antar fim din Hausa ba zai cika ba tare da ambaton sunan marigayi Darakta Tijjani Ibrahim ba, wanda ya rasu kusan shekara 11 da suka gabata, a yanzu dansa Saleem dan shekara 27 ya lashi takobin dorawa daga inda ya tsaya. A wannan tatatunawa da ya yi da Aminiya ya bayyana irin burin da yake da shi a matsayinsa na matashin darakta da sauran abubuwa masu yawa.
Yau shekara kusan 11 ke nan da rasuwar mahaifinka me ya sa sai a wannan lokaci ka shiga harkar fim din Hausa?
Zan iya cewa ina cikin harkar fim tun a shekarar 1998, sai dai a wancan lokaci ina karami sosai, kuma karatu ya dauke mini hankali wanda ya sa ban saki jiki na ci gaba da harkar fim ba, duk da cewa a lokacin nakan yin wasu abubuwan. Amma na dade da burin ganin idan na girma na shiga harkar fim ko ba don komai ba, don na ci gaba da irin kyawawan abubuwan da mahaifina ya fara yi a wannan harka. Wannan ne ya sa na dauki bangaren ba da umarni.
A lokacin da ka yi tunanin shiga harkar fim a matsayin darakta ka samu wani horo ne ko kuma ka fara ne a matsayin mai koyo?
A lokacin da mahaifina yake da rai mun shaku sosai, idan da za ku tambayi mutanen da suka san shi za su gaya muku yadda yake gudanar da abubuwansa. Mahaifina irin mutanen da ke son koya wa duk wani mai sha’awa irin abin da suka sani, kasancewata dansa ya sa na koyi abubuwa da dama daga wurinsa kafin na shiga harkar fim. Haka kuma akwai mutane da ke son ganin na gaji mahaifina, mutane irin su Ali Nuhu da Mika’il Bin Hassan Gidigo, sun yi kokari ganin na dora daga inda mahaifina ya tsaya. Zan iya cewa su ne suke ba ni goyon baya a harkar aikina a matsayin darakta. Ina da difloma a harkar kwamfyuta; a yanzu haka ma ina kokarin samun wata diflomar a bangaren Kimiyyar dan Adam a Jami’ar Bayero ta Kano.
Wadannan mutane da na ambata su ne suka taimaka min da kowace irin gudunmawa ta fuskar aikina, su ne mutanen farko da suka ba ni aiki a matsayin Mataimakin Darakta. Da taimakonsu ne na samu damar yin fina-fina sama da 8 a matsayin mataimakin darakta.
Shin ka samu wani horo kan ba da umarni kafin da kuma bayan ka shiga harkar?
A gaskiya babu, sai dai kamar yadda na gaya muku tun farko na koyi abubuwa da dama daga wurin mahaifina. Haka kuma dukkan fim din da na yi aiki a kansu na yi ne a matsayin Mataimakin Darakta. Wannan shi yake ba ni damar koyon sababbin abubuwan ci gaba a harkar ba da umarni. Haka kuma zan iya bugun kirji na gaya maka cewa da kwazon darakotocin da nake aiki tare da su a yanzu ina koyon abubuwa da dama.
Yaya ka ji a lokacin da ka fara samun aiki a matsayin mataimakin darakta?
A matsayin karamin yaro na ji wani iri, lokaci zuwa lokaci kuma na rika samun ‘yar damuwa, amma kasancewar ina aiki tare da kwararu sai ya sa na ji dadin gudanar da aikin. Abin da ya sa na damu shi ne, ganin cewa an dora min kusan gaba dayan nauyin fim din sai nake ganin kamar ana ce min “Kai ka kiyaye kada ka bata abubuwa’. Sai dai da kalaman karfafa gwiwa da goyon baya na samu damar yin abin da ake bukata.
Zuwa yanzu fina-finai nawa ka ba da umarni?
A yanzu haka ina da fina-finai kusan guda takwas, misali fim din ‘Son Mai So’ da ‘Madubin Dubawa’ na taka rawar mataimakin darakta, akwai kuma ‘Rabo Ajali’ da ‘Kurman Gari’ da ‘Ra’ayin Zuci’ da sauransu su ne finafinan da na ba da umarni.
Daga cikin wadannan fina-finai da ka ambata wane ya fi ba ka wahala?
Fim din ‘Son Mai So’ ya fi ba ni wahala, dalilina na fadin haka shi ne, ina zaune bayan na karya kumallo a lokacin da Ali Nuhu ya kira ni a waya yana sanar da ni cewa akwai wani fim da zan yi aiki a kansa a safiyar wannan rana. Bayan ya ba ni labarin a rubuce sai na tambaye shi lokacin da za a yi, amsar da ya ba ni ita ce a yanzu. Ba ni da zabi a haka muka tafi wurin daukar fim din, don zan iya cewa a kan hanya na karanta abin da labarin fim din ya kunsa. Ana cikin hakan kuma sai Ali Nuhu ya tafi wani wurin, wanda kuma ragamar tafiyar da aikin ta dawo hannuna duk da cewa akwai Mansur Sadik wanda shi ma darakta ne. A gaskiya na sha wahala a wannan fim din, sai dai kuma an samu biyan bukata a cikinsa.
Yaya za ka kwatanta dangantarkar da ke tsakanin iyalinku da kuma ’yan fim?
Muna yaba musu, domin sun yi mana abubuwan alheri. Ba zan fadi sunansu ba, kasancewar duk wanda ya yi mai kyau da wanda ya yi marar kyau kowa ya san kansa. Kamar dai yadda ake fadi cewa mutum shi ne babban alkalin kansa.
A kwankin baya an shirya addu’a ta musamman ga marigayin mahaifinka, mai za ka fadi ga wadanda suka shirya wannan addu’a?
A wannan rana na zubar da hawaye a lokacin da mutane suke fadin abubuwan alheri a kan mahaifina. Ina so na yi amfani da wannan damar don na bayyana cewa wannan addu’a da aka shirya don mahaifina ita ce abin da ya taba faruwa a rayuwata wanda na fi jin dadinsa. Haka kuma ina mika sakon godiyata ga wadanda suka shirya addu’ar Allah Ya saka musu da alherinsa Amin.
Mene ne burinka a wannan sana’a?
Burina kamar yadda na bayyana a baya shi ne na ci gaba daga inda mahaifina ya tsaya. Ina so na bayar da cikakkiyar gudunmawata ga ci gaban harkar fim din Hausa. Haka kuma ina da burin na shiga sabuwar makarantar koyon harkar fim don na samu ilimi kan aikin ba da umarni. Ina kuma fatan ganin masana’antar fim din Hausa cikin kankanin lokaci ta kai matsayin jagora a duk masana’antun fina-finai na duniya.