Ina son auren budurwar da ta caka min wuka —Matashi
Ana sallamar shi daga asibiti ya wuce ofishin ’yan sandan da aka tsare ta yana roko su sake ta
Wani matashi da budurwarsa ta soka wa wuka ya tsaya kai da fata cewa idan ba ita ba sai rijiya.
Buduwarta ta sa wa saurayin nata, kaifi ne a lokacin da wata sa-in-sa ta suka a tsakaninsu a garin Jos na Jihar Filato, lamarin da ya sa sai da aka yi masa aiki a asibiti.
“Saboda in tabbatar mata cewa har yanzu ina kaunar ta, ana sallama ta daga asibiti, na je na duba ta a ofishin ’yan sanda domin nuna damuwata kan halin da take ciki,” inji matashin, wanda mazaunin Unguwar Rogo ne a garin Jos.
Yanzu dai budurwar, wadda ’yar Unguwar Ali Kazaure ce, na tsare a caji ofis tun bayan da ’yan sanda suka cafke ta kan aika-aikar da ta yi a ranar 2 ga watan Disamban da muke ciki.
’Yan sanda sun ce budurwar ta musanta zargin da ake mata, amma binciken da suka gudanar ya nuna ita ce ta caka wa masoyin nata wuka saboda wani sabani da suka samu.
— ‘Yadda budurwata ta soka min wuka’
Ya ce: “Ta gan mu da yarinyar ne a lokacin da ita da kawarta suke wucewa, na kuma lura cewa ta fusata, na kira amma ta ki ta amsa saboda kishi.
“Ni ban sani ba, ashe bayan gani na da ta da yi da yarinyar shiga gidan makwabta ta yi ta karbi wuka; Ba zato, ba tsammani kawai sai na ji ta soka min. Daga nan ne aka wuce da ni zuwa asibiti aka yi min aiki.
“Amma duk da abin da ya faru, har yanzu ina kaunar Fatima, ina kuma son auren ta. Abin da ya faru kuma kaddara ce, wadda za ta iya fadawa a kan kowa.
“Muna matukar kaunar juna kuma na san bacin rai ne shi ya sa ta aikata min hakan; Ta yi da-na-sanin abin da ta aikita, ta ba ni hakuri kuma na yafe mata.
“Ni dai abin da nake shi ne a taimaka min a roki iyayena su bari in aure ta, zan yi matukar farin ciki godiya game da hakan.”
— ‘Ya hakura da auren’
Da take magana da wakilinmu, mahaifiyarsa ta ce ta yi matukar mamaki jin cewa yarinyar da dan nata ke so ya aura ce ta yi masa wannan danyen aiki.
Saboda haka ta ce ba za ta bari soyayyar tasu ta ci gaba ba saboda tsoron idan suka yi aure za ta iya kashe shi.