Ina son Trump kan fada wa ’yan Afirka gaskiya – Musebeni

Shugaba Yoweri Musebeni na Uganda ya bayyana cewa yana son Shugaban Amurka Mista Donald Trump kan yadda yake fada wa mutane Afirka gaskiya ba boye-boye. A farkon wannan wata ne, aka zargi Shugaba Trump da bayyana kasashen Afirka da ‘kazamai’ a wajen wani taro kan shigi da fici. Shugaba Trump dai ya musanta cewa ya […]

Ina son Trump kan fada wa ’yan Afirka gaskiya – Musebeni

Shugaba Yoweri Musebeni na Uganda ya bayyana cewa yana son Shugaban Amurka Mista Donald Trump kan yadda yake fada wa mutane Afirka gaskiya ba boye-boye.

A farkon wannan wata ne, aka zargi Shugaba Trump da bayyana kasashen Afirka da ‘kazamai’ a wajen wani taro kan shigi da fici.

Shugaba Trump dai ya musanta cewa ya yi wannan kalami, amma sanatocin Amurka da suka halarci taron suka nace cewa ya fadi hakan.

kungiyar Tarayyar Afirka ta bukaci Shugaba Trump ya nemi gafara kan wannan kalami nasa da ‘a zahiri nuna bambancin launin fata ne.’

Sai dai Musebeni ya ce, “Amurka ta samu daya daga cikin shugabannin da suka fi dacewa,” lamarin da ya jawo barkewar dariya daga mahalarta taron wakilan Majalisun Dokoki na kasashen Afirka ta Gabas (EALA) da aka gudanar a Kamfala babban birnin Uganda. 

“Ina son Trump saboda yadda yake fadin gaskiya ga ’yan Afirka. Akwai bukatar ’yan Afirka su warware matsalolinsu, Afirka tana da rauni,” inji shi.

Kalaman na Shugaba Musebeni ya saba da martanin da shugabanni da dama na Afirka wadanda suka la’anci sakin bakin na Shugaba Trump.