Ina sukar Tinubu ba don na tsane shi ba — Jigo a NNPP
Jigon ya ce idan Tinubu bai yi nasara a matsayin shugaba ba zai bar yankin Yarbawa abun kunya.
Jigo a Jam’iyyar NNPP, Ambasada Olufemi Ajadi, ya bayyana cewa duk wata suka da yake yi wa mulkin Shugaba Bola Tinubu, yana yin ne domin taimaka masa don yin nasara.
Ajadi, yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida, ya musanta maganganun da ke cewa ya saba sukar Gwamnatin Tarayya da jam’iyyar APC saboda ƙiyayya ga shugaban ƙasa.
- Mai kai wa ’yan ta’adda kakin sojoji ya shiga hannu a Kaduna
- Mutum 5 sun rasu sakamakon rikicin manoma da makiyaya a Neja
Ya jaddada cewa, a matsayinsa na cikakken ɗan ƙabilar Yarbawa, ba shi da wani dalili da zai yi ƙiyayya ga ɗaya daga cikin shugabanninsu.
Ya bayyana cewa “A al’adun Yarbawa haramun ne a ƙi ɗan uwa ko wani babban mutum.
“Suka ce nake yi domin taimaka wa Tinubu ya samu nasara a mulkinsa saboda shi shugaba ne.”
Ya ƙara da cewa duk abin da Tinubu ya aikata a kan mulki zai zama abin alfahari ko kuma kunya ga yankinsu a siyasa.
“Ba na nuna ƙiyayya ga shugaban ƙasarmu. A gaskiya, ina ƙaunarsa a matsayinsa na mutum kuma a matsayin shugaban ƙasarmu. Ina damuwa game da yadda zai bar wani kyakkyawan tarihi lokacin da zai bar ofis.
“Saboda zai bar ofis wata rana, kuma duk wani abin da ya cimma a ofis zai shiga cikin tarihin ƙasar nan,” in ji Ajadi.
“Ba zan iya yin ƙiyayya ga shugabana ba kasancewar ni bayarba ne. Idan aka cire siyasa da jam’iyyu, Shugaba Tinubu yana daga cikin shugabanninmu a ƙasar Yarbawa, kuma nasararsa a ofis nasararmu ce.
“Hanyar da nake bi don taimaka masa ya samu nasara a ofis, ita ce ta faɗa masa gaskiyar da ta dace ya sani don ya yi nasara. Mutane da yawa da ke kewaye da shi saboda yabo ba za su faɗa masa irin wannan gaskiyar ba.
“Hanyar rayuwarmu a ƙasar Yarbawa ita ce faɗin gaskiya, kuma wannan shi ne dalilin da ya sa yankinmu ya zama abun sha’awa wajen inganta ci gaban ƙasa tun bayan samun ’yancin kai.
“Shugaba Tinubu ya nuna wannan ɗabi’ar gaskiya ta Yarbawa ga masu mulki lokacin mulkin soji a Najeriya. Ba za mu iya cire rawar da ya taka wajen kafa wannan dimokuraɗiyyar da muke mora ta hanyar ayyukansa a NADECO ba.”