Ina tausaya wa ma’aikatan Najeriya- Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna rashin dadinsa bisa yadda ma’aikata a jihohi ke ci gaba kokawa a kan rashin biyansu hakkoinsu duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa jihohin. Shugaban ya nuna rashin dadin ne a lokacin da yake ganawa da wasu gwamnonin karkashin jagorancin shugaban gwamnonin Arewa, gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari […]

Ina tausaya wa ma’aikatan Najeriya- Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna rashin dadinsa bisa yadda ma’aikata a jihohi ke ci gaba kokawa a kan rashin biyansu hakkoinsu duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa jihohin.

Shugaban ya nuna rashin dadin ne a lokacin da yake ganawa da wasu gwamnonin karkashin jagorancin shugaban gwamnonin Arewa, gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari a gidan gwamnati, inda ya ce lallai ma’aikatan na ne neman tallafi domin suna matukar shan wahala.

“Ya za a yi mutum ya yi barci da kyau alhali ba a biya ma’aikatan albashinsu na watanni ba.

“Ina mamakin yadda ma’aikatan nan suke ciyar da iyalansu, su biya kudin makarantar ‘ya’yansu da kudin haya,” inji shugaban Buhari.

A nasa jawabin, Gwamna Abdul’aziz Yari ya ce duk tallafin da Gwamnatin Tarayya ta ba jihohin, sun yi amfani da su yadda ya kamata, sannan ya ce sun gaji basukan hakkoqin ma’aikatan ne daga gwamnatocin baya.

“Muma muna cikin damuwa da abubuwan da ke faruwa a jihohinmu. Kuma muna aiki tukuru wajen shawo bakin zaren,” inji shi.

Sannan kuma gwamnan ya yaba wa shugaban kasar bisa yadda ya kokarta wajen farfado da tattalin arzikin kasar.