Ina tausayin malaman da ke min kazafi – Al-Mustapha

Tsohon Babban Jami’in Tsaro na marigayi Shugaba Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya ce masu kalaman batanci game da shi kan karya kuma suke kiran kansu malamai su ji tsoron Allah domin suna fada wa mutane abin da ba shine ba: Aminiya: Manjo tunda ka fito daga inda aka tsare ka har yanzu mutane […]

Ina tausayin malaman da ke min kazafi – Al-Mustapha

Tsohon Babban Jami’in Tsaro na marigayi Shugaba Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya ce masu kalaman batanci game da shi kan karya kuma suke kiran kansu malamai su ji tsoron Allah domin suna fada wa mutane abin da ba shine ba:

Aminiya: Manjo tunda ka fito daga inda aka tsare ka har yanzu mutane ba su bar cece-kuce ba game da komawarka bakin aiki, wasu ma cewa suke yi wai an ba ka mukamin Janar shin ina aka kwana?
Al-Mustapha: Kamar yadda na yi bayani a baya a bisa tsarin aikin soja yayin da aka kai ofisan soja gaban kotu to akwai sharudda da dokokin da zai bi, wato sai an gama duk wani abu da ya shafi batun daukaka kara da mutanen Legas suka ce za su yi kana hukumar soja ta duba ita kuma ta ga me ya dace ta yi game da maganar. To shi ne na ga kafin duk a kammala wadannan abubawa da na yi ta zama haka nan sai na ce bari na ci gaba da abubuwan da nake yi na harkokin ciyar da matasa gaba domin tun kafin a tsare ni ina da harkokin matasa da nake yi.
Aminiya: Wani abu da mutane za su so su sani shi ne yau a ji ka nan, gobe a ji ka can da sunan taimaka wa matasa shin ina kake samun kudin da kake cewa kana taimaka wa matasa?
Al-Mustapha: Allah cikin ikonSa Ya hada ni da abokai da magoya baya, da taimakon Allah da kuma nasu muke wadannan abubuwa da mutanen masu son kasar nan da kishin kasa, muna da tawaga mai karfi kuma mai manufofi daban-daban masu ma’ana. Duk inda ka ji mun tafi, muna godiya ne ga iyayen kasa saboda irin addu’o’in da aka yi ta yi mana. Haka kuma shugabannin matasan mukan zauna da su domin fadakar da su tafarkin da za a bi domin a zauna lafiya, musammam a jihohin da aka samu tashe-tashen hankula.
Aminiya: Ana ta kiran ka shiga siyasa wasu ma ganin yawan tafiye-tafiyen da kake yi cewa suke yi ka shiga siyasa me za ka ce?
Al-Mustapha: Ni ba zan siyasa ba ne na fada a da, kuma ina sake fada a yanzu haka ba ni da katin kowace jam’iyya. Ni dan Najeriya ne mai son a zauna lafiya kuma a kare hakkin dan Adam, Najeriya ta samu makoma, mai kyau musamman Arewa. Kwadayinmu Arewa ta tsaya da kafafunta, duk tafiye-tafiyen da nake yi ban taba furta wani batun siyasa ba.
Aminiya: Shin kana hankaltar da matasa illar amfani da su da ’ an siyasa ke yi domin biyan bukatun kansu”
Al-Mustapha: Wannan yana cikin abubuwan da muka fi yi musamman a jihiohin Kaduna da Filato inda ake ta kashe-kashe, kuma yawanci duk da matasan ake amfani. Kwanan nan muka dawo daga Gombe da Bauchi, duk inda muka je batun guda ne babu aikin yi, don haka muke kokarin ganin sun bi hanya tagari. Wannan shi ne kwadayinmu a samu a sa su a hanya tagari, domin su ne wata rana za su mulki kasar. Akwai wani sarki da ya ce idan aka ci gaba da yadda ake tafiya yanzu, to mahaukata ne za su zo su yi mulkin Arewa. Dalilansa shi ne matasa masu shaye-shaye sun yi yawa, ya ce abin da ya ba shi tsoro shi ne yanzu ba ma sholisho suke sha ba, har da bayan gida da kwata suke shakawa don gusar musu da hankali. Babban sarki ne a Arewa ke fada mana haka lokacin da muka kai masa ziyara a yawon da muke yi don tattaunawa da matasan.
Aminiya: Fito da kai da kuma zagayawar da ka rika yi ta sa wasu na zargin cewa kana da wata boyayyiyar alaka da wannan gwamnati ina gaskiyar wannan batu?
Al-Mustapha: Ba ni da wata alaka da wannan gwamnatin illa matsayina na dan kasa. Wadanda suka kama mu suka gana mana ukuba su ne suke kirkiro irin wadannan surutai. Tun Janar Buhari na mulki a 1984 nake wadannan abubuwa ba wanda ya sani. kungiyoyin matasan nan na yi musu rajista na saka su aiki, kuma ina wannan har lokacin da aka kama ni, na kasa. Sai kuma lokacin Oputa Panel a shekarar 2001ina daure ma na kirkiro kungiyar matasa, to kuma yanzu da na fito naci gaba kafin a yanke hukuncin daukaka karar da Legas ta yi. Kamata ya yi a gode mana muna abubuwa na sadakatul jariya.
Aminiya: Kwanaki ka kalubalanci tsohon Shugaban kasa Obasanjo, shin akwai wani martani da ya yi maka?
Al-Mustapha: Kawo yanzu ba wani martani da ya mayar min, sai dai akwai wani na kusa da shi wato Fani Kayode, tsohon Ministan Zirga-Zirgan Jiragen Sama shi ne yake fada wa duniya  wai a ina  nake lokacin da Obasanjo ya rubuta wancan takarda. Ina Indiya tare da iyalina, ’yan uwa da ka gani a nan su ne suka raka ni filin jirgi akwai fasfo dina da bizar da aka yi ta zuwa Indiya, kuma ga takardun zamana a asibiti, duk inda ka shiga a duniya, ba yadda  za a yi ka buya ga kuma rubuce rubucen kasashen duniya kowa ya shiga kowace kasa za a rubuta  da lokacin shigar ka da lokacin fitarka. Abin da ya kai ni Indiya azabar da su Obasanjo suka yi min ne na je kai asibiti kuma har yanzu ban murmure ba, ina godiya da Allah Ya bar ni ina iya tafiya bisa kafufuwana. Ya rubuta wannan takarda ne don wani makirci na wadanda suka kama mu suka yi mana kage-kage da sharrance-sharrance. Shi ya sa ba na wata shakka ko haufin tunkararsu in bukatar haka ta taso.
Mu dai kishin kasar nan ya sa muke wadannan fisabilillahi, domin ba abin da ya fi zaman lafiya yau, saboda in aka dubi kasashen Masar da Sudan da Saliyo da Syria, inda na fara nawa gumurzun a Chadi ne lokacin ina da anini daya kuma muka tafi muka dawo lafiya wasu da muka tafi da su ba su dawo ba. Wanda ka ga yana neman fitina bai san fitinar ba ce, fatarmu Allah Ya sa kada kowace irin fitina ta tashi a Najeriya komai kankantarta.
Aminiya: Akwai wasu malamai da ke zarginka da wasu abubuwa ga wannan gwamnati me za ka ce kan haka?
Al-Mustapha: Na ji na wani malami a Kaduna wanda yake rantsuwa kan karya. Irin wadannan sai dai ka tausaya musu. Wallahi zai gamu da Allah har wasu mutanen da suka kulle mu suka azabtar da mu su ne suke yin wannan kazafi. Kamar wasikar tsohon Shugaban kasa ne, mun kare bincike-bincikenmu mun gano ko wane ne, alhamdu lillahi ba dai an sa kwamitin bincike ba game da wasikar insha Allahu ’yan Najeriya za su zo su ji me zai faru, sai Allah Ya fiddo su fili Ya kunyata su a idon duniya, abubuwa  za su fito a idon duniya, har da wadanda suka taya shi.
Aminiya: Ganin irin matsalar da ke addabar kasar nan musamman harkokin tsaro a Arewa an nemi shawarwarinka game da harkokin tsaro ganin kai masani ne a fanni?
Al-Mustapha: Ba wanda ya tuntube ni a kan na yi wasu abubuwa na tsaron Najeriya tunda na fito har zuwa yanzu. Abin da kake gani shi nake gani, abin da kake ji shi nake ji, amma ba a ce mu ba da wata shawara ba. Ga hukumomin da ya kamata, wannan hakki ne na kowa yanzu idan ka ga barawo zai fasa  gidan wani ka yi sauri ka fada  wannan hakki ne na dukkan ’yan Najeriya in su ga abin da zai haddasa  fitina a tashi a kare shi saboda kasar ta zauna lafiya. Amma idan abu ne na gani zai cuci kasar in rubuta wa  ’yan sanda ko SSS ko soja wanda shi na fi sani ai hakki ne na kowa idan ka rubuta ka bayar ba zai bata ba yana nan ajiye kuma wata rana zai yi amfani.
Aminiya: kaddara an jingine batun daukaka kara, za ka koma aikin soja ne ko wata sabgar za ka kama?
Al-Mustapha: Idan an kammala batun daukaka kara a yau fata in fita daga wannan aikin, dalili shi ne ina  zaman zamana ina wannan aikin na bauta fisabilillahi yau a ce misali ina wuri kaza ina da soja karkashina ana iya wayar gari a ce yau Al-Mustapha ya zama kakan Hitila, saboda haka tunda muna da masu sharri irin wadannan abin da ya fi  kyau shi ne mu bar aikin, domin abokan aikinmu da muke aji guda yau shekara biyu ya rage  mu cika shekara 35 na  barin aiki, yanzu muna da shekara 33 a  wannan aiki ka ga  ba  wani abu da ya rage.
Aminiya:Yanzu kaddara gwamnati ta kira ka domin yi mata aikin tsaro da ba  dole ne kasa  kayan sarki ba shin za ka yi?
Al-Mustapha: Ya dogara, kuma sai na yi shawara saboda akwai na gaba da mu akwai iyayenmu komai zan yi ina yin shawara.
Aminiya: Akan gan ka da mutanen da ba ’yan Arewa ba, misali kana da kyakkyawar dangantaka da Fani Amu. Su Lateef shofolahan shin mene ne dailin haka?
Al-Mustapha: A  gaskiya akwai aiki a gabanmu dole mu yi tunanin hadin kan kasar nan, saboda abu ne muhimmi. Idan aka yi zurfin tunani za a ga cewa rashin hadin kan tsakanin mutanen Kudu  da Arewa babban  hadari ne, misali in fitina ta faru a Kano, kafin ka ankara an fara kashe ’yan Arewa a Kudu, bai kamata a ce a zauna wannan abu na ci gaba ba. Haka idan dan wani abu ya faru a can sai ’yan Arewa a nan su ce za su yi ramako. Ka ga wannan bai nuna zaman kasa daya ba ke nan, fatanmu kowa a ba shi  hakkinsa a kare shi duk inda yake. Wannan ne ya sa muka je Owerri muka gana a tsakanin manyan shugabanninmu na Kudu da namu na Arewa, irin su Asari Dokubo da Dokta Fredrick Fasehun da mutanen MASSOB suka wakilci shugabannin Kudu aka yi yarjejeniya cewa hakkin kare dan Arewa a Kudu  yana hannun dan Kudu,  hakkin kare dan Kudu a Arewa yana hannun dan Arewa. Ya zamanto hakkin kare juna yana bisa kafadun juna. Ba a taba samun irin wannan ba, sarakunan Ibo cewa suka  yi  da  ana yin haka kafin a yi Yakin Basasa da ba yi  yakin ba, balle har bambance –bambancen su yi karfi.
Aminiya:  Kana ganin tafiyarku Owerri ta yi tasiri, domin cikin wadanda kuka tattauna da su an jiwo wasu suna kalamai marasa dadi ga Arewa?
Al-Mustapha: Hankalin kowa daban, muhimmin abu shi ne wannan yarjejeniyar tana nan kuma kowa ya sa hannu idan mutum ya yi wani abu da ya taka yarjejeniyar ta karya dokar kasa ba wanda ya fi karfin hukunci, inda ka ga fitina tana tashi, to doka ba ta da tasiri. Kamata ya yi a ba mu goyon baya a rika zama sosai, sarakunan Kudu na Arewa su fahimci juna, wadanda ke kan mulki na Kudu da na Arewa su fahimci juna, haka ’yan makaranta da matasa maza da mata. Idan ana haka Najeriya curewa za ta yi kuma ci gaban da kasar za ta samu cikin dan kankanen lokaci zai yi yawa.
Aminiya: Ka gamsu da taron kasa da aka shirya za a yi ke nan?
Al-Mustapha: Duk abin da za a yi idan maganar jama’a ce to akwai rahama a ciki, duk abin da mutum zai yi shi daya ba ya da kyau, maganar a hada kai ba mutum ne ya kirkiro ba addini ne.