Ina tsammanin baƙin haure ne suka kashe sojoji a Delta — Akpabio

Mutanen Delta, mutanen kirki ne, ba na tunanin za su iya aikata irin wannan mummunan aiki.

Ina tsammanin baƙin haure ne suka kashe sojoji a Delta — Akpabio

Godswill Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce yana ganin kamar baƙi daga ƙetare ne suka hallaka sojojin Najeriya 17 a Jihar Delta.

Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne a lokacin da suke tattaunawa a zauren majalisar kan kisan kiyashin da aka yi wa zaratan dakarun a makon jiya.

Akpabio ya ce, “Mutanen Delta, mutanen kirki ne, ba na tunanin za su iya aikata irin wannan mummunan aiki.

“A ganina waɗansu ne baƙi daga ƙetare ne suka kitsa wannan abin takaicin kuma suka aiwatar, ba na so in yarda cewa jama’ar Delta ne.”

Sanata Akpabio ya buƙaci a kafa wani kwamiti mai karfin gaske da zai binciki faruwar wannan abin baƙin cikin da ya samu Najeriya.

Zaratan sojojin da wasu ɓata-gari suka hallaka dai suna bakin aiki ne a runduna ta 181 da ake kira Amphibious Batallion a Ƙaramar Hukumar Bomadi a Jihar Delta.

Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta ce ta ƙaddamar da gagarumin bincike bayan wasu ɓata-gari sun kashe sojojinta a Jihar Delta da ke Kudu maso Kudancin ƙasar.

Daga cikin wadanda ɓata-garin suka kashe, har da kwamandan da ke jagorantar sojojin da wasu masu muƙamin manjo biyu da wani mai muƙamin kyaftin ɗaya, sai kuma kananan sojoji 12 da suke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos