Ina yaba wa gwamnoni bisa amincewa da ƙudirin Dokar Haraji — Tinubu

Sai dai gwamnonin sun ƙi amincewa da buƙatar ƙara harajin cinikayya na VAT da yake ƙunshe a cikin ƙudirin.

Ina yaba wa gwamnoni bisa amincewa da ƙudirin Dokar Haraji — Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa gwamnonin Nijeriya bisa amincewar da suka yi da ƙudurin yi wa Dokar Harajin ƙasar kwaskwarima.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan yaɗa labarai da tsare tsare, Bayo Onanuga ya fitar a yammacin wannan Juma’ar.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya jinjina wa gwamnonin kan sadaukarwarsu, wadda za ta samar da haɗin kai tsakanin shugabanni a faɗin ƙasar, ba tare da la’akari da ɓangaranci ko ƙabilanci ko kuma na siyasa ba.

Tinubu ya bayyana cewa babbar manufar sabon ƙudurin dokar harajin ita ce “taimaka wa talaka, da bunƙasa gasa a fannin tattalin arziƙi, da kuma janyo hankalin masu zuba jari na cikin gida da kuma ƙetare.

A cikin sanarwar, Tinubu ya ce sabunta dokar harajin Nijeriya, wadda tuni aka daina yayin ta abu ne mai muhimmanci.

Aminiya ta ruwaito cewa a jiya Alhamis ne gwamnonin Nijeriya suka amince da ƙudurin Dokar Harajin bayan sun yi mata wasu ’yan sauye-sauye.

Daga cikin sauye-sauyen da gwamnonin suka yi kamar yadda shugaban ƙungiyarsu kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq sun ƙi amincewa da buƙatar ƙara harajin cinikayya na VAT da yake ƙunshe a cikin ƙudirin.

A cikin sabon tsarin rabon haraji a Nijeriya da gwamnonin suka fitar bayan wata ganawa da suka yi da kwamitin da aka kafa domin nazari kan ƙudurin sabuwar dokar harajin,sun ce kashi 50 cikin ɗari za a raba daidai-wa-daida tsakanin dukkanin jihohi.

Haka kuma, gwamnonin sun yi wa ƙudirin gyaran fuska da cewa kashi 30 cikin ɗari za a raba gwargwadon gudumawar da kowace jiha ta bayar wajen tattara harajin.

Sai kuma kashi 20 cikin ɗari za a raba gwargwadon yawan al’ummar kowace jiha.

Kazalika, gwamnonin sun kuma bayar da shawarar cire sashen sabon ƙudurin dokar da ya shata lokacin dakatar da ware wa Gidauniyar tallafa wa manyan makarantu da takwarorinta da sabuwar dokar ta ambato kuɗi.

“Mambobin wannan ƙungiya sun amince cewa kada a yi ƙari a harajin VAT, ko rage harajin kamfanoni na CIT a wannan lokaci, domin tabbatar da daidaiton tattalin arziƙi,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa “muna bayar da shawarar kada a sanya wani ɓangare a dokar da zai iyakance kuɗaden tafiyar da lamurra da ake ware wa TETFUND, NASENI da NITDA.”

A ƙarshe, sanarwar ta ce ƙungiyar gwamnonin tana goyon bayan cewa a yanzu Majalisar Tarayyar za ta iya ci gaba da muhawara kan dokar domin samun amincewa.